нυĸυncιn qaѕrυ 3 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday 7 July 2017

нυĸυncιn qaѕrυ 3

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-3!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na uku****
.
Cigaba***
.
.
_Hadisi ya tabbata ruwayar bukhari da muslim daga sahab Abdullahi dan umar, yace na aboci manzon Allah (s.a.w) kuma shi yakasance baya kara sallarshi samada raka,a bibbiyu ahalin tafiya, hakama Abubakar da Umar da Usmanu, suka kasance**_
.
_Toh amma yatabbata Sayyadina Usmanu lokacinda yake khalifa yazo aikin hajji kuma seya rika cika sallah, kuma sahabbai suka bishi basu yimai inkariba, toh wannan abinda sukayi shima yana nuna cewa sallar qasru ba dole bane***_
.
_kenan Usman afarkon khalifancinsa baya cika sallah, qasru yakeyi, amma daga baya seyabar yin qasrun yakoma yana cikawa***_
.
_Toh malamai sunyi sabani gameda gwargwadon tafiyada ake iya yimata qasru shin adadin wanne irin nisane akeyin qasru***_
.
_Dawuduz Zahiri  yanada fahimtar cewa kowacce irin tafiya anayi mata qasru karamar tafiyace ko babba, koda kuwa tafiyar ta mil uku ce, yana kafa hujjah da wani hadisi ruwayar musulim daga Yahya bin yazid Alhuna'i wanda yace: na tambayi Anas dan malik gameda qasrun sallah, sai yace: Manzon Allah (s.a.w) yakasance idan yafita tafiya ta kimanin mil uku ko farsakhi uku yakanyi qasrun sallah***_
..
_wasu malamai sukace wannan hadisin baya zama hujjah dankuwa ansamu shakka acikinshi, inda yace mil uku ko farsakhi uku***_
.
_wasu kuma malamai sukace Aa idan tafiyarda zakayi doguwar tafiyace toh bazaka fara yin qasruba harse kaci mil uku kokuma farsakhi uku acikin tafiyar sannan zaka fara yin qasru***_
.
_Wasu kuma sukace dazarar kawuce gidan karshe na garinku toh shikenan sai kawai kafara yin qasru****_
.
_Wasu kuma sukace sai ka gama wuce gonakin garinku sannan zaka fara yin qasru****_
.
_wasu kuma sukace Ai ita qasru saukice Allah yayiwa matafiyi, toh dan haka duk wata tafiya metsawo toh ya halasta kayi qasru, ammasu basu iya kance nisan tafiyarba kawai sudai sunce tafiya menisa***_
.
_wasu kuma sukace Allah dai yace idan kunyi tafiya abayan qasa babu laifi kuyi qasru, sesukace kenan tsananinda ake samu ahalin tafiya shine yajawo saukinda yasa akace muyi qasru, saboda haka sukace bazaka fara qasruba harse kafara tafiya, wato raddine sukeyima wasu malamai wayanda suka fassara kalmar *DARABTUM* wanda yazo acikin ayar, sesukace ma,anarsa ai *AZAMTA* watoh dazarar kayi nufin tafiya koda kuwa bakama fara tafiyarba inhar kayi niyyar zakai tafiyar, toh kawai sukace kafara yin qasru*** toh wannan maganar itace wayancan malaman sukema raddi, shine sukuma dasuka tashi fassara waccan kalmar ta *DARABTUM* sesukace ma,anarta ai *SAFARTUM* idan kunyi tafiya, toh ai kai yanzu kana gida bakayi tafiyaba, kuma sukace tafiyarma sekayi menisa sannan zaka fara qasru amma bawai yar karamar tafiyaba, sukace wannan unguwa kaje ba tafiya kayiba***_
.
_Wasu malamai kuma sukace Qur,ani da Hadisi basuce ga tsawon tafiyarda zakayiba kafin kayi qasru kokuma kafara yin qasru, amma sesukayi tawaqqufi basuce komaiba****_
..
_Toh mu ajje wannan batun zuwa gaba kadan zan kawo muku mafi ingancin zance gameda hakan***_
.
_Toh sekuma irin tafiyarda take halasta ayi mata qasru, shin kowacce irin tafiyace akeyin qasru kokuwa an kebance wasu nau,oin tafiya wayanda ba,a yinmusu qasru??? Toh nanma malamai sunyi sabani, wato jama,a zeyi wuya a fiqhun musulinci kasamu wani abu wanda akai sabani sosai akanshi, fiyeda sallar qasru, ita kusan babu wata gaba da zaka dauka acikinta baka samu anyi sabani ba****_
.
_Imamul qurdubi ya hikaito Ijma,in malamai akan ya halasta ayi qasru a tafiyar aikin hajji da umura, da tafiya ta sada zumunci da gudun hijira, toh wayannan sune tafiye tafiyenda kan malamai yahadu akan cewa lallai anayi musu qasru, amma duk tafiyarda basuba toh anyi sabani***_
.
_Jumhurin malamai sukace ya halasta ayi qasru adukkan wata tafiya ta halas, kamar kasuwanci ko makamancin haka***_
.
_sannan jumhurin malaman suka kara cewa bai halastaba mutum yayi qasru a tafiya ta sabon Allah, kamar karuwa ko dan fashi, da sauransu, duk wayannan bai halasta garesu suyi qasruba inji jamhurin malamai***_
.
_Itama wannan maganar mu ajjeta se gaba kadan zanmuku gamsashshen bayani akanta, akan shin akwai tafiyarda ba,a yimata qasru kamar yanda wayannan tattaruwan malaman sukace???***_
.
_Sekuma adadin kwanakinda mutum zeyi yana yin qasru, shima wannan ansamu sabani akanshi, kamarfa yanda nagaya muku ita qasrun sallah kusan babu wata gaba acikinta wacce ba,ayi sabani ba***_
.
_Imamu Malik da Shafi'i, da Laisu bin sa,ad da Dabari, da wasu malamai sunada fahimtar cewa qasru ba,a wuce kwanaki uku: dazarar ka wuce kwanaki uku sukace zaka cika sallah su a fahimtarsu shine qasru kwanaki uku akeyi, wato idan kayi tafiya, dazarar ka kwana uku kana qasru agarinda kaje toh zaka cigaba da cika sallah***_
.
_Sa'idu bin Musayyib, da Abu Hanifa da Imamus Sauri sukuma sunada fahimtar cewa qasru anayin kwanaki 14 ne, idan kayi tafiya kanada damar kaita yin qasru tsawon sati biyu, amma dazarar ka haura sati biyu toh zaka cika sallah, sukuma wannan itace fahimtarsu***_
.
_Ansamu wata ruwayar kuma daga sa,idu dan musayyib wanda shine fahimtar Ahmad bin Hambal, da wayansu malamai sukuma sukace anayin qasru ne adadin salloli 21 na farilla, kawai sukace dazarar kayi tafiya toh kanada damar qasrune a salloli 21, amma dazarar kawuce haka sukace toh zaka cika sallah****_
.
_Wayansu malamai kuma sukace ai duk matafiyi yanada damar yaita yin qasru har abada, kawai indai sunanka matafiyi toh kaita yin qasru harse kadawo, koda shekaru nawa zakayi, sun kafa hujjah da hadisin Anas dan malik daya kwashe kanaki sittin agarin Naisabur kuma qasru yaitayi, akwaima asarai dayawa wayanda sahabbai sukayi tafiya kuma sukaita yin qasru har suka dawo***aduba tafsrin qurdubi mujallad na biyar shafina 259, wayannan maganaganun duk za,a gansu***_
.
_toh itama wannan matsalar mu ajjeta seku biyoni cikin bayani nagaba semuji gamsassun bayanan dakuma wayanda sukafi karfin hujjah in Allah yaso****_
.
_Yanzu dai mun kawo muku kanun bayanan malamai kenan gameda irin tafiyarda ake mata qasru, da adadin kwanaki, dakuma nisan tafiyar, sannan kuma yaushe ake fara qasrun, toh wayannan zamu gaya muku abinda yafi inganci akan kowannensu, amma se cikin bayani nagaba in Allah yaso***_
.
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support