JAGORAN MAHAJJACI (01)
Fassarar: Dr Abubakar Sani Birnin Kudu
Ministry of Islamic affairs na Saudi Arabia suka buga
KA'ABAH ALQIBLAR MUSULMAI
Ka’abah Mai Daraja ita ce 'Dakin Allah ‘yantacce
Zukatan Musulmi duk inda suke a banngarorin duniya gareshi suke karkata.
Goshi da zukatan bayin Allah masu khushu’i da qasqantar da kai ga Allah sau biyar a yini da dare, duk wannan 'Daki suke fuskanta.
Musulmi na kwararowa tawaga-tawaga zuwa 'Daki ‘yantacce daga kowace hanya da wuri mai nisa, tun daga zamanin da Annabi Ibrahim ya ginashi,don yin aikin hajinsu, kuma domin suyi 'Dawafi a wannan 'Daki mai daraja.
Wannan don ya qara tabbatar da cewa wannan 'Daki shine:Daki na farko da aka sanyawa mutane domin su bautawa Allah a cikinsa bisa ilimi da basira, da aqida tsabtatacciya, wadda bata gurbata da miyagun aqidu da
ra’ayoyin da suka saki hanya ba.
Allah Ta’ala yana cewa:
{Kuma lallai 'Daki na farko da aka aza domin mutane, shi ne wanda ke Bakka mai albarka kuma shiriya ga talikai. A cikinsa akwai ayoyi bayyanannu (misali) matsayin Ibrahima. Kuma wanda ya shige shi ya kasance amintacce. Kuma aikin hajin 'Dakin wajibi ne domin Allah a kan mutane,
ga wanda ya samu iko zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lallai Allah Mawadaci ne daga barin talikai} Suratu aal Imran: 96-97.
Daga Ibrahim Nasidi Abu-Ilham 25/07/2017

0 comments:
Post a Comment