Goron sallah 11daga (kitabu was-sunnah) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 10 July 2017

Goron sallah 11daga (kitabu was-sunnah)

*GORON SALLAH-11???!!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
:
Yau 15-10-1438, wacce tayi dai dai da 9-7-2017***
:
Taken Lekca
.
*GORON SALLAH-11*
-
Wannan shine bayani na 11
....
....
*ﺇﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ، ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻨﻪ، ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ، ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ*
.
_Bayan haka abaya idan baku mantaba munfaro bayanine gameda irin yadda aka samu wasu daga cikin magabata suka riqe ruwan zam zam yazama shine silar samun iliminsu, inda yanzu kuma akan wannan bayanin zamu dora*****_
_Imamus Sakhawy, Sweedy, Dasu Ibnu Hajar Asqalany dukkansu sunsha ruwan zam zam domin wata buqata kuma Allah ta'ala ya biya musu******_
                _Nan kusa kusama Muhammad Nasirudden Albani shima lokacinda wata cuta ta matsa mishi yayita fama da ita yanata kashe kudin magani, ahaka ahaka har Allah yasa yaci karo da wayannan hadisai wayanda suke nuna cewa Ruwan zam zam warakane, aikuwa se malam Yakoma gaba daya bayacin komai baya shan komai face ruwan zam zam shine kadai abincinshi kuma shine ruwan shansa kusan tsawon watanni biyu, harseda yawarke tangaran yadena jin alamar wannan ciwon ajikinshi sannan yadena shan ruwan zam zam****_
           _Aqasar maroko anyi wata dattijuwa itama sadda ta kamu da matsanancin rashin lafiya, ankaita asibitoci daban daban amma abun yaci tura, sekawai 'ya'yanta suka dauketa suka kaita qasar jamus, wajen manyan likitoci, amma suma da suka gama bincike akanta sesukace wannan ciwon nata yariga yagama cin qarfinta bazata warkeba mutuwa zatayi, harma suka bayarda adadin lokacinda zata mutu*****_
            _Yayinda tsohuwar taji ance bazata warkeba mutuwa zatayi, setacema 'yayan nata su dauketa su kaita madina tanaso ta mutu acan kusada Annabi muhammad (s.a.w)***_
             _Bayan sun kaita madina sun dawo gida sukayita lissafin kwanakinda yaragewa mamarsu aduniya domin suje can madina su halarci jana'izarta*****_
               _Cikin ikon Allah lokacinda sukaje madina sesuka samu mahaifiyarsu ta murmure tayi 6ul 6ul kamar ba itaba, sesuke tambayarta yaya jikin nata?? Se tace musu ai ta warke yanzu ko kadan batajin wannan ciwon a tareda ita*****_
          _Se wayannan yaran nata suka dauketa suka sake maida ita wancan asibitin na qasar jamus domin asake dubata, amma ikon Allah bayan likitoci sunyi iyakar binciken da zasuyi sun gama sesukace aikuma yanzu basuga cutarba babu ragowar wani ciwo ajikinta, sesuka tambayi yaran wanne asibitine suka kaita??? Sukace basu kaita ko inaba se garin madina acan tazauna tsawon wannan lokaci****_
           _Se aka tambayi ita dattijiwar ya akayine ta warke haka?? Setace itadai batasan komaiba amma abinda tasani shine tunda aka kaita garin madina Ruwan zam zam kawai tadinga sha,  bata cin komai bata shan komai face wannan ruwa na zam zam*****_
               _Wannan dalilin yasa wayanna likitoci suka tura aka ebo musu wannan ruwa na zam zam, sukayi bincike akanshi kuma sun tabbatarda cewa lallai akwai waraka acikinshi*****_
_Akwai mataye dayawa kuma har yanzu ana samunsu musamman lokacin aikin hajji wayanda suke zuwa saudiyya su sha ruwan zam zam da niyyar Allah yabasu haihuwa kuma dayawansu Allah ta'ala yabasu****_
             _Akwai wanda yabamu labarin haduwarshi da wata mata ita matsalarta kawai shine duk idan ta tashi haihuwa maza take haifa, bata ta6a haihuwar mace ba, kuma tanaso itadai taga ta haifi diya mace, to se akabata shawarar taje makka tasha zam zam, aikuwa tana zuwa tasha wannan ruwan shekarar bata zagayoba seda matarnan tasamu ciki kuma diya mace ta haifa wanda yake bamu wannan labarin yace ajere ajere saida wannan matar ta haifi 'ya'ya uku mata dukansu****_
:
:
Zamu dakata anan sekuma bayani nagaba Idan Allah yakaimu
=
=
_Almajirinku dan mutanen kabo_
'
_Jameel Alhassan Haruna Kabo_
_Alwahhaby-Assalafy_
.
 Nake mana fatan Alheri wassalamu alaikum
..
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support