Goron sallah 10 daga (kitabu was-sunnah) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 10 July 2017

Goron sallah 10 daga (kitabu was-sunnah)

*GORON SALLAH-10???!!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
:
Yau 15-10-1438, wacce tayi dai dai da 9-7-2017***
:
Taken Lekca
.
*GORON SALLAH-10*
-
Wannan shine bayani na Goma
....
....
*ﺇﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ، ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻨﻪ، ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ، ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ*
.
_Bayan haka abaya idan baku mantaba nace muke sefa me Imani shine yake iya riqon ruwan zam zam amatsayin abinci kuma ruwan ya riqeshi, domin kada kace bari kaje ka gwada kagani ko gaskene, ma'ana kana shakka kenan, to wannan zam zam ba lallaine yayi maka amfaniba****_
           _Abdulallahi Dan Abbas yakasance duk sanda zesha Ruwan Zam zam shikuma yakansce *ALLAHUMMA INNI AS'ALUKA ILMAN NAFI'IN, WA RIZQAN WASI'AN, WA SHIFA'AN MIN KULLI DÃ'IN***
       _Ya Allah ina roqonka kabani ilimi me Amfani, da arziki me yalwa, dakuma waraka daga dukkan cuta***_
            _Kunji wannan babban sahabi dai 'yan uwa  wanda kuma ku kunsani idan Allah yabiya buqatarsa ko be biyaba, wannan basenace wani abu ba tunda ku kunsane wanene Ibnu Abbas a duniyar musulinci******_
                   _Imamu Abu Hanifa shikuwa duk sadda zesha ruwan zam zam roqon Allah yakeyi akan yabashi ilimi, wanda ku kanku ayanzu kunsani idan yasamu iimin ko be samuba tunda kunsan wanene Abu Hanifa a duniyar musulinci wanda har mazhaba guda gareshi, to kuna iya cewa Zam Zam shine sirrin iliminshi****_
        _Imamuna Ash-Shafi'i shikuwa idan zesha ruwan Zam zam yakan roqi Allah yabashi iya harbi da kibiya, malaman tarihi sukace kuma Allah yabashi wannan abinda ya nema domin kuwa sukace idan ya harba kibiya sau goma, to tara suna samun wannan abinda yaharba, dayace kawai take gocewa****_
              _Sannan kuma yakan qara da roqon Allah yabashi ilimi da Aljanna, wanda shi kansa yana cewa Allah ya amsamin guda biyu, domin idan zansha ruwan zam zam ina roqon Allah yabani iya harbi, kuma gashi yabani, sannan ina roqonshi yabani ilimi shima gashi yabani, to ina fatar Allah yabani na ukun****_
           _Muma anan muna tayashi Addu'a Allah yabashi aljannar tare damu baki daya****_
            _Imamuna Abu Isah Attirmizy babban malamin hadisi ne yake cewa watarana ina cikin dakin ka'aba gashi ancika anyi cinkoso anata dawafi, nikuma se fitsari yakamani ya matseni, na rasa yadda zanyi natakura sosai, kuma idan nace zanfita ahaka to zanyita taka mutane, yace inacikin wannan hali na matsuwa sekawai na tuna da Hadisin Annabi (s.a.w) wanda yace Ruwan zam zam yana matsayin abinda kasha dominsa, kawai sena tafi bakin rijiyar zam zam na kafa kaina nasha sosai nacika cikina, Tirmizy yace tunda yagama shan zam zam awannan lokacin besake jin qishiba har asubahi haka yakutsa cikin mutane yacigaba dayin dawafi******_
              _Kunji masu tsabar imani 'yan uwa, futsari fa yakeji amma hakanan yasake bankama cikinshi ruwa amma kuma saboda imaninda yayi da hadisan Manzon Allah segashi yasamu biyan buqatarshi****_
      _Shugaban masu tauhidi na Duniya, Ibnu Khuzaima, wanda ake cemasa Imamu Ahlut tauhid, duk daluban Hadisi sunsan wanene Ibnu Khuzaimah, to shima sanda aka tambayeshi menene sirrin samun iliminshi?? Seyace:  zam zam shine sirrin samun ilimina idan nakafa kaina inasha sai inyita roqon Allah yabani ilimi, to wannan shine sirrin samun ilimina****_
                _Ibnul Arabi Almaliky yake gayama dalubansa cewa sadda naje saudiyya na kafa kaina a ruwan zam zam sekawai naciga da roqon Allah yafahimtar dani Alqur'ani, Yace musu wannan roqon nawa idan Allah yakar6a ku kun sani, inma be kar6aba kun sani, yace amma sedai abinda namanta ban roqaba shine Allah yabani ikon aiki da Alqur'anin idan ya horemin iliminsa***_
         _Ko yanzu duk daluban ilimi sunsan wanene Ibnul Araby a fagen Qur'ani, shine yakeda Littafin tafsiri Ahkamul qur'an, kuma jigone babba a mazhabar malikiyya to shima sirrin samun iliminshi kace zam zam ne****_
:
:
Zamu dakata anan sekuma bayani nagaba Idan Allah yakaimu
=
=
_Almajirinku dan mutanen kabo_
'
_Jameel Alhassan Haruna Kabo_
_Alwahhaby-Assalafy_
.
 Nake mana fatan Alheri wassalamu alaikum
..
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support