LABARI MAI GIRGIZA ZUCIYA
*******************************
Abdullahi bn Almubarak (rah) yana daga cikin magabata na kwarai, kuma mutum ne Salihi.
*******************************
Abdullahi bn Almubarak (rah) yana daga cikin magabata na kwarai, kuma mutum ne Salihi.
Wata shekara bayan yayi niyyar tafiya aikin Hajji, sai ya fita domin yin ban-kwana da abokansa (Almajiransa) kafin tafiyarsa. Amma akan hanyar ne yaga wani abu wanda ya tada masa hankali ya firgitashi.
Ya hangi wata baiwar Allah tana tone juji (bola) tana tonowa wani MUSHEN KAZA wacce aka jefar. Ta daukota ta sanya a Qasan hammatarta, ta juya ta tafi aboye acikin duhu.
Sai yayi kiranta yace "Mai kikieyi ya ke baiwar Allah?!". Sai tace "Ya kai bawan Allah, kyale halittu da mahaliccinsu. Domin Allah yana da sha'ani acikin lamarin halittunsa".
Sai Ibnul Mubarak yace mata "Ina yi miki magiya don girman Allah ki gaya min labarinki".
Sai matar tace masa "Amma wallahi ba don ka riga kayi mun magiya ba, da ban gaya maka halin da nake ciki ba".
Kafin ta fara gaya masa har hawaye ya fara zuba daga idanunta. Sai tace "Hakika mu Allah ya halatta mana cin mushe. Domin ni Bazawara ce Matalauciya. Kuma (ni) mahaifiyar 'ya'ya mata ne guda hudu".
"Mutuwa ta dauke Mahaifinsu mai kula dasu, Yanayi ya tsananta garemu, kuma dukiya ta Qare daga gareni. Kuma na kwankwasa kofofin mutane (wato na bibbi gidajen jama'a) amma ban samu wata zuciya mai tausayi daga wajensu ba".
"Sai na fita domin nemowa abinci ga 'Ya'yana wadanda wutar yunwa ta riga ta Qone musu hanta. Sai Allah ya azurtani da samun wannan mushen kazar da kake gani. Shin zakayi jayayya dani ne akanta?".
Daga jin wannan labari nan take sai Idanuwan Ibnul Mubarak suka rika zubda hawaye. Sai yace mata "Karbi wannan amanar".
Sai ya damka mata dukkan dunkiyar da yayi niyyar tafiya aikin hajjin nan da ita.
Sai Uwar marayun nan ta karba ta juya wajen 'ya'yanta tana godiya. Shi kuwa Ibnul Mubarak ya juya zuwa gidansa. Alhazai na garinsu kuma suka tafi suka sauke faralinsu sannan suka dawo.
Amma abin mamakin duk da cewar shi bai je aikin Hajji ba, amma duk Alhazan sun dawo suna yin godiya gareshi bisa hidimar da yayi musu awajen aikin Hajji.
Suan cewa "Allah yaji Qanka Ya Kai Ibnul Mubarak! Babu wani wajen zama da muka zauna fache sai ka bamu wani abu daga ilimin da Allah ya sanar dakai. Kuma bamu ga wanda ya fika wajen bautarka ga Allah Ubangijinka ba, awajen aikin Hajjin nan na wannan shekarar".
Sai Ibnul Mubarak yayi mamaki kuma hankalinsa ya tashi game da al'amarinsa, da kuma al'amarinsu. Shi dai bai bar garinsa ba (ballantana ace har an ganshi awajen aikin Hajji). Kuma shi ba yaso ya bayyanar musu da sirrinsa. (wato ba yaso ya gaya musu cewar yayi sadaqah ne da kudinsa).
To da ya kwanta barci sai yaga wani kyakkyawan mutum wanda haske ke fita daga fuskarsa. Yana ce masa "AMINCIN ALLAH YA TABBATA AGAREKA YA KAI ABDULLAHI. SHIN BAKA SAN KO NI WANENE BA? AI NINE MASOYIN NAN NAKA MUHAMMADUR RASULULLAHI (SAWW) NINE MASOYINKA ADUNIYA DA LAHIRA, KUMA NINE MAI CETONKA ARANAR LAHIRA. ALLAH YA SAKA MAKA DA ALKHAIRI BISA ABINDA KAYI MA AL'UMMATA".
"YA KAI ABDULLAHI 'DAN MUBARAK! HAKIKA ALLAH YA GIRMAMAKA (YAYI MAKA KARAMCI) KAMAR YADDA KA GIRMAMA MAHAIFIYAR MARAYUN NAN. KUMA ALLAH YA RUFA MAKA ASIRI KAMAR YADDA KA RUFA ASIRIN MARAYUN NAN".
"HAKIKA ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA HALICCI WANI MALA'IKA NE DA SIFFARKA. YA KASANCE YANA TAFIYA TARE DA ALHAZAN GARINKU AWAJEN GUDANAR DA AYYUKAN HAJJI".
"KUMA HAKIKA ALLAH YA BAMA KOWANNE ALHAJI LADAN AIKIN HAJJI GUDA 'DAYA NE. AMMA KAI KUMA ALLAH YA RUBUTA MAKA LADAN AIKIN HAJJI GUDA SABA'IN!!".
Allahu Akbar!! Ya jama'a kunji fa!!!. Ya ku masu alfahari da yawan aikin Hajji!! (Nayi arfa sau kaza! Naje Umrah sau kaza!! Nayi dawafi sau kaza!!).
In dai yardar Allah kuke nema, ku zagaya gidajen Marayu da Miskinai da Fakirai mana! Zaku samu yardar Allah anan!!
Ka kwashi Matanka da Qananan 'ya'yanka ka tafi dasu Umrah alhali Makwabcinka ko limamin masallacin Unguwarku, ko 'yan uwanka suna kwana da yunwa.. (Wallahi ba lallai ne Allah ya karbi Umrar taku ba).
Wallahi ladan ciyar da Mayunwata guda goma yafi ladan zuwa Umrarka. Wasu daga cikin magabata suna cewa :
"Loma guda daya wacce aka sanya acikin cikin Mayunwaci, tafi alkhairi fiye da gina masallatan juma'a guda dubu".
Ka bar Makobcinka ko 'dan uwanka acikin yunwa da talauci, amma kaje kana LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIKA". (Kai kanka kasan Allah ba zai amshi gaisuwarka ba).
Wannan Qissar tana nan acikin Sifatus Safwah na Ibnul Jawzee.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (10-01-2017).
In sha Allahu daga nan kafin kamawar watan Ramadhan Zauren Fiqhu zai kafa wani bangare mai suna GIDAUNIYAR MARAYU wacce in sha Allahu zamu tara wani abu atsakaninmu domin ciyar da marayu da Miskinai alokacin Azumi. Sannan da kulawa da majinyata marassa galiho. In sha Allahu.
Allah shi taimakemu ameeen.
0 comments:
Post a Comment