```Assalamu alaikum
Malam Dan Allah ga tambayata. Menene sihiri kuma ya kasu gida nawa kuma ya rabe-rabensa suke???```
_*AMSA:*_
*******
وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،
Sihiri kalma ce da ake jinginawa wani abu boyayye.
Sihiri gaskiya ne, kuma akwai sihiri daban-daban da yake kama mutane a bayyane ko a boye ya sanya musu hauka ko ya kashe su, ko kuma ya raba tsakanin mata da miji. Sihiri yana tasiri ne da izinin Allah. Aiki ne na shaidanun aljannu wanda mafi yawa ana cin nasararsa ne ta hayar yin shirka da Allah. A kuma kusanci shaidanun aljannu ta hanyar ababen da suke so, wadanda sun ginasu ne ta hanyar sanyawa Allah kishiya *(Shirka kenan).*
*Al-qurafi* yace: sihiri gaskiya ne, kuma mutumin da aka yiwa sihiri zai iya mutuwa ko kuma halittarsa da halayensa zasu iya canzawa.
Allah yace:
ﻭﺍﺗﺒﻌﻮﺍ ﻣﺎ ﺗﺘﻠﻮ ﺍﻟﺸﻴﺎﻃﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﻣﻠﻚ ﺳﻠﻴﻤﺎﻥ ﻭﻣﺎ ﻛﻔﺮ ﺳﻠﻴﻤﺎﻥ ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻟﺸﻴﺎﻃﻴﻦ ﻛﻔﺮﻭﺍ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻟﺴﺤﺮ وما ﺃﻧﺰﻝ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻠﻜﻴﻦ ﺑﺒﺎﺑﻞ ﻫﺎﺭﻭﺕ ﻭﻣﺎﺭﻭﺕ ﻭﻣﺎ ﻳﻌﻠﻤﺎﻥ ﻣﻦ ﺃﺣﺪ ﺣﺘﻰ ﻳﻘﻮﻻ ﺇﻧﻤﺎ ﻧﺤﻦ ﻓﺘﻨﺔ ﻓﻼ ﺗﻜﻔﺮ ﻓﻴﺘﻌﻞﻣﻮﻥ ﻣﻨﻬﻤﺎ ﻣﺎ ﻳﻔﺮﻗﻮﻥ ﺑﻪ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻤﺮﺀ ﻭﺯﻭﺟﻪ ﻭﻣﺎ ﻫﻢ ﺑﻀﺎﺭﻳﻦ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺃﺣﺪ ﺇﻻ ﺑﺈﺫﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻳﺘﻌﻠﻤﻮﻥﻣﺎ ﻳﻀﺮهم ﻭﻻ ﻳﻨﻔﻌﻬﻢ ﻭﻟﻘﺪ ﻋﻠﻤﻮﺍ ﻟﻤﻦ ﺍﺷﺘﺮﺍﻩ ﻣﺎ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﻣﻦ ﺧﻼﻕ ﻭﻟﺒﺌﺲ ﻣﺎ ﺷﺮﻭﺍ ﺑﻪ ﺃﻧﻔﺴﻬﻢ ﻟﻮ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ.
_Kuma suka bi abinda shaidanu ke karantawa akan mulkin Sulaiman, kuma Sulaiman baiyi kafirci ba, kuma shaidanu sune sukayi kafirci, suna karantar da mutane sihiri da abinda aka saukar dashi akan mala'iku biyu a Babila, Haruta da Maruta. Kuma basu sanar da kowa ba face sunce: "Mu fitina ne kawai, saboda haka karka kafirta. Suna neman ilimin abinda suke rarrabewa tsakanin mutum da matarsa dashi daga garesu. Kuma su (Masu yin sihirin) basu zama masu cutar da kowa dashi ba, saida izinin Allah. Kuma suna neman ilimin abinda yake cutar dasu kuma baya amfaninsu. Kuma lallai ne haqiqa sun sani, tabbas, Wanda ya saye shi bayada wani rabo a lahira. Kuma tir da abinda suka sayar da rayukan su dashi, da sun kasance sun sani._
Wannan ayar ta nuna cewa sihiri gaskiya ne, kuma mai sihiri yana cutar da mutane ko ya raba mata da miji, amma duk saida izinin Allah.
Allah yace:
ومن شر النفاثات فى العقد
_Da sharrin mata masu tofi a kulle-kulle. (Mata Mayu Kenan)._
Wannan ya nuna cewa sihiri gaskiya ne, shiyasa Allah ya umarcemu da mu nemi tsari daga sharrin masu sihiri.
Dalili mai kara tabbatar da cewa sihiri gaskiya ne shine:
Hadisi yazo a *Bukhari da Muslim* cewa:
Wani bayahude *Labeed ibn Al-a'asam* yayi wa *Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)* sihiri.
Malamai sun bayyana rabe-raben sihiri da dama. Amma zamu kawo 10 daga cikinsu inshaa Allah.
Rabe-raben sihiri guda goma (10).
1. Sihirul Infisaam
2. Sihirul mahabbah/At-tiwalah
3. Sihrul Takhyil
4. Sihrul Junuun
5. Sihrul Khumul
6. Sihirul Hawatif
7. Sihrul Maraad
8. Sihir An-nazif
9. Sihrul Washiikun Nikah
10. Sihirul Jinsiiy
1. سحر الإنفصام
*Sihirul Infisaam*
Wannan yana daga cikin bakin tsafi Wanda ke raba ma'aurata ko a jefa kiyayya tsakanin abokanai biyu ko kuma yan uwa.
*Alamominsa:*
#. Canzawar halayya na gaggawa daga soyayya zuwa kiyayya.
#. Yawan neman fitina da abokin zama.
#. Canzawar fuskar mata ko miji (idan miji ya kalli matarsa zaiga fuskarta ta zama mummuna, Haka matar idan ta kalli mijin)
#. Wanda aka yiwa sihirin yana qin duk wani abu da dayan yayi dan faranta masa.
#. Wanda aka yiwa sihirin zai tsani wurin da dayan yake. (Misali miji ya tsani dakin matarsa).
2. سحر المحبة او التولة
*Sihrul Mahabba/At-tiwalah*
At-tiwala wani nau'i ne na sihiri wanda yake sa namiji yaso matarsa a makance.
*Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)* yace:
_Attiwalah shirka ne._
Yace shirka ne saboda yanasa Wanda yayi sihirin tinanin ce wa sihirin yana aiwatar da abinda Allah baiyi ba.
_*(Al-Nihaya 1/200).*_
3. سحر التخيل
*Sihrul Attakhyil*
Wannan sihiri ne mai kamar rufa ido. Wannan shine nau'in sihirin da mutanen fir'auna sukayi a jayayyar fir'auna da Annabi Musa. Sun jefa igiya ta zama maciya.
4. سحر الجنون
*Sihrul Junuun*
Wannan shine sihiri wanda ake aika shaidanin Aljani ya haukata mutum.
*Alamominsa:*
#. Yawan mantuwa da dimaucewa.
#. Furta rikitattun kalamai.
#. Ido kan fito gulu-gulu su kakkafe a kasa.
#. Yawan tsumaniya (rashin zama wuri daya).
5. سحر الخمول
*Sihrul khumuul*
Anan boka yakan tura aljani ya shiga kwakwalwar mutum ya zauna yana canza masa tinani ya kadaitar dashi daga mutane. Shine sihirin da samari suke yiwa budurwa don ta so su. Ko budurwa tayiwa saurayi dan ya aureta.
*Alamominsa:*
#. Rikitaccen so
#. Cikakkiyar yarda da ra'ayin wanda akayi asirin dominsa.
#. Rashin magana (yin shiru-shiru).
#. Rashin damuwa da kowa.
#. Yawan ciwon kai.
#. Juyewar kwakwalwa.
6. سحر الهواتف
*Sihrul Hawatif*
Wannan sihiri yanada alaqa da aljana mace. takan sa mutum ya rika yin mafarki maras kyau da kuma jin kiran sunansa idan yana a farke, amma bai san daga inda kiran yake fitowa ba.
*Alamominsa:*
#. Rike ma mutum numfashi a lokacin barci.
#. Yin mafarkin wani na kiranka.
#. Jin murya ana kiran sunanka amma baka san inda kiran yake fitowa ba.
#. Yawan yin wasiwasi.
#. Yawan zargin abokai ko kawaye da yan uwa.
#. Yin mafarkin fadowa daga wani tsauni mai tsawo ko bene mai tsawo.
#. Yin mafarkin wani dabba ya biyoka (kamar zaki, damisa, maciji etc.)
7. سحر المرض
*Sihrul marad*
Ana yin wannan sihiri ne domin a sanya wa mutum rashin lafiya.
*Alamominsa:*
#. Tabbataccen/dauwamammen ciwo na wani sashen jiki.
#. Firgita.
#. Mutuwar sashen jiki.
#. Mutuwar jiki baki dayansa.
#. Rashin aiki na dayan wadannan (harshe, anta, fata, kunne, ido ko kwakwalwa).
8. سحر النزف
*Sihrun Nazif (Zubar jini bayan haila)*
Wannan sihiri yana shafar yan uwa mata ne kawai. Mai sihirin (boka) yakan aika aljani zuwa ga matar da zai yiwa sihirin, ya umarci aljanin da ya sanya mata zubar jini. Aljanin zai shiga jikin matar ya shiga jijiyoyinta da magudanar jini yana zagayawa acikin jikinta.
*Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)* yace: _shaidan yana yawo cikin jikin Dan Adam kamar jini._
_*(Bukhari, Fathul Bari 4/282).*_
Idan aljanin ya kai ga jijiyoyin mahaifarta sai ya zabura da karfi a ciki sai yasa jini ya fara zuba a gabanta.
*Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)* ya tabbatar da hakan lokacin da *HAMNA bint JAHSHI* ta tambayi *Manzon Allah* ra'ayinsa akan jinin dake zuba kuma ba lokacin al'ada ba.
Sai yace:
_Wannan zubar jinin daga zaburar shaidanin aljani ne (a jijiyar mahaifa)._
Malaman fiqhu suna kiran *An-nazifa* da *Istihaadha.*
*Ibn Al-athir* yace istihaadha na nufin zubar jini bayan na al'ada. Wannan jini yana iya daukar watanni yana zuwa. Zai iya zuwa dan kadan ko mai yawa.
9. سحر وشيك النكاح
*Sihru washiikun nikah*
Wannan sihiri ne na hana mace aure.
Anan aljani yanada zabi guda biyu:
#1. Idan zai iya shiga jikin yarinyar, to zai sanyata taji ta tsani duk wani wanda yake sonta da aure, a haka zata ki aminceamincewa da kowa.
#2. Idan bazai iya shiga yarinyar ba, to zaiyi amfani da سحر التصور sihirin surar jiki da waje. Anan duk mai son yarinyar da aure idan ya kalleta Zai ganta a mafi munin fuska da kirar surah.
Haka itama idan ta kalli duk mai sonta da aure zata gansa a mummunar fuska da sura, komai tsananin kyansu zasu canza a ganin masoyansu. Ta hanyar aikin da shaidanin aljanin yayi.
Duk wanda yace yana sonta zakaga ya janye a yan kwanaki kadan, ba tareda wani ingantaccen dalili ba.
Idan sihirin mai karfi ne sosai, to idan mai neman aurenta yazo shiga gidansu zaiji damuwa ta rufe shi, kuma yaga bakin duhu a gabansa kamar yana a dakin gidan yari. Saboda haka bazai kara dawowa a gidan ba.
A lokacin wannan sihirin aljanin zai rika sanya ma yarinyar ciwon kai lokaci zuwa lokaci.
*Almominsa:*
#. Yawan ciwon kai wanda baya jin magani.
#. Matsanancin ciwon kirji (musamman tsakanin la'asar zuwa tsakiyar dare).
#. Wanda aka yiwa sihirin zaiga masoyinsa a mummunar sifa..
#. Bakin ciki a cikin barci.
#. Yawan ciwon ciki.
#. Ciwon baya (lower part of the back).
10. سحر الجنسي
*Sihrul Jinsii.*
Wannan sihiri ne da ya shafi saduwa tsakanin mata da miji.
Ya kasu kashi 3.
*1. Ar-rabat al-ajzal jinsi*
*2. Addhu'uf aljinsi*
*3. Ar-rabat an-nisaa'u*
*1. Ar-rabt al-ajzal jinsi (karfin sha'awar namiji)*
A wannan sihirin, namijin da aka yiwa sihirin zaiji karfi da sha'awa a gabanin saduwa da matarsa, har yakai ga azzakarinsa ya tashi tin yana nesa da matarsa, amma da zarar ya kusanto ta sai zakarin ya kwanta yayi laushi kamar habar gyale. A dalilin haka saduwa bazata yiwu ba. A haka rayuwar zata cigaba har matar ta gaji ta nemi a raba auren.
*2. Addhu'uful jinsi (raunin sha'awa)*
Wannan sihirin yana dauke sha'awar namiji na tsawon lokaci, miji zai sadu da matarsa bayan lokaci mai tsawo (kamar sau 2 a shekara). Kuma idan anzo saduwar baya daukar lokaci zai tsaya (kamar 2mins kawai), sai zakarinsa ya rasa karfinsa.
*3. Ar-rabatun nisaa'i*
Akwai nau'o'in rabatun nisaa'i har 3.
*#1. Rabt alman*
Wannan sihirin yana sanya mace ta hana mijinta saduwa da ita ta hanyar hade kafafunta biyu GAM, kuma duk karfin mijin bazai iya raba kafafun ba, saboda ba karfin matar bane karfin shaidanin aljani ne. Ita kanta bazata iya raba kafafun ba. Koda ace tayi yunkurin hakan.
Wani bawan Allah ya fuskanci wannan matsalar daga matarsa, sai yake ganin laifinta, sai tace abin yafi karfinta ba laifinta bane. Wata rana ta gayamai cewa yasa mata mari na karfe (iron shackles) ya raba kafafunta sannan ya sadu da ita. Yayi hakan amma baici nasara ba.
Sannan tace yayi mata allurar barci sannan ya sadu da ita. Yayi hakan yayi nasara, amma ita kuma matar bazata taba amfanar wannan zaman ba. Saidai shi mijin ne kawai yake amfanuwa.
*#2. Rabt at-taballud (rashin jin sha'awa)*
A wannan sihirin, aljanin da aka aiko zai shiga a sashen kwakwalwa inda tinanin sha'awar mace ke fitowa. Ya kawar mata da jin sha'awa a lokacin da mijinta yake saduwa da ita. A dalilin haka zata rasa jindadin jima'i, sai ta fara kin mijinta ta daina amince masa a majirkicinsu.
Jikinta zaiyi rauni sosai a lokacin saduwa kuma batajin komai na sha'awa koda mijinta yayi mata duk abinda yakeso bazata ji komai ba. Aljanin zai dauke tinaninta na sha'awa ta yadda tantanin ta bazai iya fitar da ruwan da zai jiqa farjinta ba, a dalilin haka farjinta zai bushe qaf. Saboda haka saduwa bazata yiwu ba.
*#3. Rabat an-nazif (fitar jini lokacin saduwa)*
Wannan ya banbanta da sihir an-nazif. Saboda wannan jinin yana zuwa ne a lokacin da akayi nufin saduwa ko kuma ana cikin saduwar. Jini mai yawa yakan zuba a lokacin saduwa, wannan zai hana mijinta saduwa da ita.
Akwai wani Soja ya bada labari yace idan ya dawo hutu matarsa tana zubar jini, a ranar da ya koma aiki jinin zai dauke. Kuma idan yazo Hutu yakan yi kwanaki biyar.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_

0 comments:
Post a Comment