Labarin wani dattijo mai hikima ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday, 7 July 2017

Labarin wani dattijo mai hikima

LABARIN WANI DATTIJO MAI HIKIMA
***************************************
Wani Dattijo mai hikima yana zaune agefen kogi yana hutawa, Yana kallon ruwa. Chan sai yaga wata Qatuwar kunama (Scorpion) ruwa ya daukota. Amma bata mutu ba, tana kokarin tseratar da kanta amma ta kasa.
Nan take sai Dattijon nan ya fara neman wani sanda wanda zai tsamo kunamar nan da ita, amma bai samu ba. Don haka sai ya mika hannunsa domin ya daukota. Ita kuwa kunamar ta harbeshi har sai da ya Qwala Eehu!
Da ya gama Eehunsa sai ya sake mika hannunsa domin ya dauko kunamar nan, Ita kuwa ta Qara harbinsa har ma yafi na farko.
Ya sake mika hannunsa kenan a karo na uku, ashe akwai wani saurayi agefensa yana kallon duk abinda ke faruwa. Sai yace: "Haba dattijo!! Mai yasa zaka rika mika hannunka kunar nan tana cizonka. Ina ruwanka da ita! Ka kyaleta mana'.
Shi kuwa Dattijon nan bai kulashi ba, Har sai da ya samu nasarar tsamowa Kunamar nan daga hallaka. Sai ya juya wajen saurayin yace masa :
"Ya kai Saurayi! Ka sani ita kunama babbar dabi'arta shine HARBI DA CIZO DA MUGUNTA. Ni kuwa Musulmi Mumini, Manyan dabi'o'in da Ubangijina ya horeni akansu sune TAUSAYI, HAKURI, JURIYA, TAIMAKON GAJIYAYYU, AFUWA, DA KUMA YAFEWA.
Shin kafi son in bar Dabi'ar kunamar nan ta rinjayi dabi'una, Ko kuwa inyi amfani da tawa dabi'ar don in samu rabo awajen Ubangijin da ya halicci Kunamar nan!!!".
***********
ZAUREN FIQHU :
Hakika da yawa acikin mutane ana samun masu dabi'a irin ta kunamar nan. Ko acikin 'Yan uwanka ko abokanka, Ko iyalanka zaka iya samun masu irin wannan dabi'ar. Kana iyakar kokarinka wajen taimakonsu amma su bassu gani. Kullum sai Mugunta da butulci da Qeta suke shirya maka.
Kayi kokari kayi koyi da dattijon nan mai hikima. Ka tuna da girman Ubangijinka wanda kake yin komai dominsa. Don neman yardarsa. Kar ka bar dabi'ar mugaye ko Mahassada ta rinjayi dabi'arka.
Kyalesu da halinsu kaci gaba da kyautata musu. Ta wannan hanyar Allah zai yi maka maganinsu.. Amma idan ka dauki irin tasu dabi'ar, dakai dasu duk ba zakuyi daraja awajen Allah ba.
Wannan nasihar tazo muku ne daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3)
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support