DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 19
91. Rayuwa takaitacciya ce. Kada ka cika ta damuwa. Kada dogon guri ya dauke hankalinka daga mutuwa. Aikata alheri a kowane lokaci watakila shi zai zamo mabudan aljanna a gare ka.
92. Sau da yawa mu ke kuskuren fahimtar mutane. Ma'aunin da ba ya kuskure shi ne ka ajiye kanka a matsayin wanda kake yi ma hukunci.
93. Idan ba ka son a soke ka kada ka ce komai, kada ka aikata komai. Duk wanda ya motsa dole ne sai an soke shi.
94. Mafi hankalin mutane shi ne wanda ya bar duniya kafin ta bar shi, ya gyara kabarinsa kafin ya shige shi, ya yi sallah a cikin jama'a kafin su sallace shi, sannan ya yi ma kansa hisabi kafin a gurfanar da shi a ranar hisabi.
95. Ba ka sanin dadin lafiya sai idan ciwo ya same ka. Ba za ka san dadin zaman lafiya ba sai ka gamu da tashin hankali. Ana sanin dadin haduwa ne idan rabuwa ta zo.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
24/10/1438
18/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment