Goron sallah 4 daga (kitabu was-sunnah) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 8 July 2017

Goron sallah 4 daga (kitabu was-sunnah)

*GORON SALLAH4???!!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
:
Yau 14-10-1438, wacce tayi dai dai da 8-7-2017***
:
Taken Lekca
.
*GORON SALLAH-4*
-
Wannan shine bayani na Hudu
....
....
*ﺇﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ، ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻨﻪ، ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ، ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ*
.
_Bayan haka Abaya munji irin yadda Annabi Ibrahim yayi addu'a bayan ya ajjiye matarsa awannan kwari to yabar mata qunshi na dabino da salka ta ruwa sannan yatafi yabarsu, wanda hakan kuma yana daga cikin manya jarabawa wayanda Allah ta'ala yayiwa Annabi Ibrahim dan kuwa ya kwashe shekaru masu yawa yanason yasamu da, seyanzune Allah yabashi amma kuma se akace yatafi da dan nashi da matar yakaisu wannan kwari ya ajjesu kuma yatafi yabarsu****_
               _Bayan Annabi Ibrahim yatafi se ita Hajara ta wanzu tana cin wannan dabinon da yabarmata tana kuma shan ruwa shikuma danta yana samun Ruwan nono daga jikinta yanasha******_
              _Ahaka ahaka har yau da gobe wannan dabinon yaqare ruwan shima ya qare, sekawai tazauna tana zaman jiran tsammani, to kuma tausayi irinna Uwa setaga yaronta yanzu baya samun abinci gashima har yana neman yashiga wani hali itakuma bazata iya zaunawa tazura ido tana kallonshi har ya mutu ba****_
           _Ananne seta tashi tabazama, to dama akwai dutsen Safa ana wajan sekawai taje tahau wannan dutsen aguje taname tsammanin zatasamu ta hango wayansu jama'a su tallafa mata kokuma tasamu ruwa amma ina bata samuba kuma bataga kowaba sekawai tasauko aguje tadawo wannan kwarin inda tabar yaronta seta kama habar zaninta ta lullu6e fuskarta saboda bataso taga yadda wannan yaron nata ze mutu****_
_Sekuma tasake fita aguje takoma tahau daya dutsen na Marwa wanda shima yake anan wajajen kusa da ita, haka tadingayi tafita aguje tahau dutsen safa tasauko tazo kwarinnan da yaron yake seta saka ha6ar zani ta lullu6e fuskarta, tasake bazama aguje tanufi dutsen marwa canma dai taga babu mafita seta sake yankowa aguje tasauko qasa inda yaron yake tasake rufe fuska seda tayi haka sau bakwai wanda shine asalin inda akasamo sa'ayi wanda akeyinsa a lokacin aikin hajji*****_
                   _Idan Allah yasa kasamu zuwa saudiyya ayanzu zakaga wani waje wanda aka sanya wayansu korayen futullu a inda ake sa'ayi ayanzu, alamar wajenda ake farawa da inda ake gamawa inda ake dan gudu gudu, to wannan wajen shinefa inda muke maganar wajenda Ita Hajara ta ajje wannan yaro nata Annabi Isma'il (AS)****_
          _Amma yanzu idan kaje wajen kana iya rudewa kasantuwar yadda aka qawatashi da tayal da saurab kayan alatu na zamani, to kuma wannan yasan aikin hajji akeyin sassarfa anan wajan saboda itama Hajara haka tadungayi, wanda ita ta riqa yin hakane saboda tanaso tawuce danta dasauri karma taga yadda zemutu*****_
       _Kuma wannan yasa sunnah ne idan akazo wajen ariqa yin sassarfa kamar yadda ita saratun tadinga yi****_
           _To tayi hakanne bayan tagama zagaye na bakwai ta juyo har zata wuce kawai saitaji wani sauti wanda yabata mamaki har taji kanta yana dan sarawa setaji sautinfa da gaskene yaqi tsayawa, shine setace shin ko kanada wani taimakone wanda zaka iya yimin???_
             _Abinda bata saniba shine ashe mala'ika jibrilu ne Allah ya aikoshi wajenta, shine yasaka fiffikensa ya daki qasa, kawai nan take sega Ruwan Zam zam yafara 6u66ugowa inda itakuma Hajara ganin wannan ruwan awannan lokacin seta saka hannayenta tariqa tarbe wannan ruwa tana tattareshi tanaso ta hadashi waje guda*****_
       _Shine Annabi (s.a.w) yake cewa Allah yajiqan Mahaifiyar Annabi Isma'il inda ace taqyale ruwan Zam Zam bata tareshiba, toda yanzu yazama idan ruwane wanda yake kwarara iya Inda Allah yanufa ako ina se ayita samun Ruwan Zam zam_
 _Amma tunda ta tareshi shine yacigaba da wanzuwa awannan wajen kuma har yanzu yananan beta6a qarewaba kuma kullun shansa akeyi ba,a ta6a samun wani lokaci wanda za,ace babu ruwan zam zam ba***_
          _To wannan qoqarinda da ita hajara tayiy na tare wannan ruwa shinefa abinda yaragema ruwan qarfi, amma ibda ace bata surka da qoqarintaba tabar abinda Allah yayi to da mu'ujiza da albarkar Wannan ruwa tawuce yadda ake gani yanzu kamar yadda zamuzo muji irin albarkokinda suke cikin wannan ruwa nan gaba kadan****_
:
:
Zamu dakata anan sekuma bayani nagaba Idan Allah yakaimu
=
=
_Almajirinku dan mutanen kabo_
'
_Jameel Alhassan HarunaY Kabo_
_Alwahhaby-Assalafy_
.
 Nake mana fatan Alheri wassalamu alaikum
..
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support