Masu hikima sunce ?? ( fitowa ta 35) dr.mansur ibrahim sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday 5 August 2017

Masu hikima sunce ?? ( fitowa ta 35) dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 35

156. Laifin da tufar arziki ta boye, idan iskar tsiya ta zo sai ta bayyana shi.

157. Idan kai maciyin tuwo ne, kada ka zagi Sarkin noma.

158. Idan ka raina tuwonka ba zai kosar da kai ba.

159. Ka nemi girman duniya da aikinka, kada ka nemo shi da asalin babanka.

160. Sakarcin duniya bai wuce mutane uku ba: Na farko: Wanda yayi wa kurma waka. Na biyu, wanda yayi rawa domin makaho. Na uku, wanda ya caba ado cikin duhun dare ya yi ta yawo.

Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

10/11/1438
3/8/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support