Masu hikima sunce (fitowa ta 12) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday 11 July 2017

Masu hikima sunce (fitowa ta 12)

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 12

56. Mai karimci yana boye maka rashinsa, har ka gan shi kamar mawadaci ne.

57. Shugaban jama'a shi ya fi su shan wuya.

58. Abi da ba ka same shi da ladabi da rarrashi ba, ba za ka same shi da kaushin hali da wauta ba.

59. Mai samu shi aka fi kauna. Amna mai hikima da mai ilimi su suka fi amfani.

60. Farkon fushi hauka ne. Karshensa kuwa nadama ce.

Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

17/10/1438
11/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support