Goron sallah 9 daga (kitabu was-sunnah) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday, 9 July 2017

Goron sallah 9 daga (kitabu was-sunnah)

*GORON SALLAH-9???!!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
:
Yau 15-10-1438, wacce tayi dai dai da 9-7-2017***
:
Taken Lekca
.
*GORON SALLAH-9*
-
Wannan shine bayani na Tara
....
....
*ﺇﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ، ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻨﻪ، ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ، ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ*
.
_Bayan haka Idan masu karatu suna biye damu abayanin baya munji Wasu hadisai wayanda suke bayyana mana falala gamida albarkan Ruwan zan zam wanda mukace zamu ambata yadda wasu daga cikin magabata da 'yan bana sukayi riqo da wannan Ruwa domin neman lafiya kuma sun samu waraka******_
            _Amma kafin mucigaba akwai wani hadisi wanda yake cikin Ibnu Majah Daga Muhammad dan Abdurrahman dan Abubakar yace: Ina zaune a wajen Abdullahi dan Abbas, sega wani mutum yazo wajenshi, seyace masa daga ina kake? Yace daga Rijiyar Zam zam, seyace kasha kuwa kamar yadda yadace? Seyace kamarya? Yace: Idan zakasha shi, ka fuskanci Alqibla, kuma ka ambaci Allah, sannan kayi numfashi guda uku kuma kasha sosai dayawa kayi tatul, idan ka gama seka godema Allah megirma da daukaka, domin Manzon Allah (s.a.w) yace: Alamarda take tsakaninmu da munafikai shine su basa kwankwadar zam zam dayawa*****_
             _Sedai wannan hadisin malamai subada maganganu akan ingancinshi***_
       _Amma ko babu komai wannan hadisin yana koyar damune wayansu daga cikin ladubba na shan ruwan zam zam, wanda nan gaba shima zamuzo da bayanin ladubban shan ruwan ajere Idan Allah yaso****_
        _Abaya can idan baku mantaba mun kawo muku hadisinda Annabi (s.a.w) yace babu wani ruwa a duniya wanda yafi na Zam zam Albarka, sannan Annabi (s.a.w) ya qara da cewa acikinshi akwai abinci ga me jin yunwa sannan kuma maganine ga mara lafiya****_
               _To Ansamu mutane dayawa wayanda suka jaraba Amfani da Ruwan zam zam gameda wata cuta wacce ta damesu wanda kamar yadda nace zam zam yana maganin dukkanin wata cuta****_
            _Amma yanada kyau muyi tambihi kafin mudora bayani, domin yanada kyau mutane sugane shifa wannan ruwa bawai kowane yakema maganiba, domin akwai wayanda sukeda shakku a zukatansu gameda hadisan Annabi muhammad (s.a.w) to shikuma wannan ruwa duk mutuminda zeshashi ba tareda yanada yaqinin hadisanba to ba lallaine ruwan yayi masa aikiba****_
               _Duk abinda zakayishi kana shakka akansa to kai zeyi wahala yayi maka amfani, amma inhar kanada yaqini a zuciyarka cewa wayannan hadisai da sukazo daga manzon Allah gaskiyane baka kokwanto akansu to inkasha ruwan zam zam zakaga tasirinshi da ikon Allah*****_
                   _Kamar yadda Ibnul Qayyum Aljauziyya yafada acikin littafinsa Zadul Mi'ad yace: Shi da idanunshi yaga mutanenda suka maida ruwan zam zam yasama abincinsu tsawon lokaci basacin komai basa shan komai inbanda wannan ruwa tsawon lokaci*****_
           _Sannan kuma shi kansa Ibnu Qayyum din yayi fama da wata laruwa wacce tadinga wahalardashi, hakan tasa lokacinda yaje rijiyar Zam zam seya dinga Karanta Iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in yana tofawa acikin ruwan zam zam ahaka har Allah ya warkar dashi****_
               _Sayyidina Umar kansa ya kasance Idan zesha Ruwan Zam zam yakance ya Allah zansha wannan ruwa da niyyar ka tsareni daga Qishin ranar Alqiyama******_
              _Wannan maganar tananan acikin Dibbun nabawi, kuma wannan take nuna mana bambancinmu da su sahabbai, lokacinda mu muketa fagamniyae neman duniya amma shi Sayyidina Umar Addu'a yakeyi Allah ya rabashi da qishin ranar Alqiyama****_
        _Muma kuma anan muna roqon Allah ta'ala ya tsaremu daga wannan qishi na ranar alqiyama****_
:
:
Zamu dakata anan sekuma bayani nagaba Idan Allah yakaimu
=
=
_Almajirinku dan mutanen kabo_
'
_Jameel Alhassan Haruna Kabo_
_Alwahhaby-Assalafy_
.
 Nake mana fatan Alheri wassalamu alaikum
..
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support