KUNDIN MASU TUBA (013)
LABARIN ZUL KALA'I
**********************
Ibnu Duraidin ya karbo daga Rayyashiy shi kuma daga Asmu'iy (babban Malamin Lugah din nan) yace :
"Manzon Allah (saww) ya kasance ya aika wasika zuwa ga Zul Kala'i (daya daga sarakunan Qabilun Larabawa) yana kiransa zuwa ga Musulunci. Kuma ya aika Wasikar ne ta hannun Jareer bn Abdillahil Bajaliy (Radhiyallahu Anhu).
Zul Kala'i lamarinsa ya Qasaita atsakanin Mutanensa har ya fara da'awar Rububiyyah (Wato yana ce musu wai shima abin bauta ne). Kuma Mutanensa sun bishi akan haka (Wato suna bauta masa) har zuwa lokacin da Annabi (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya bar duniya tun kafin Jareer din ya dawo.
Zul Kala'i yaci gaba da yin abinda yakeyi (Shirka da kuma Qaryar Allantaka) har zuwa zamanin Khalifancin Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (rta) sannan yaji kwadayin shiga Musulunci.
Ya taho zuwa garin Madeenah tare dashi akwai Bayinsa gida dubu takwas (8,000). Ya Musulunta ahannun Sayyiduna Umar, kuma ya 'yantar da bayi guda dubu hudu (4,000).
Sai Sayyiduna Umar (rta) yace masa "Ya Kai Zul Kala'i ina so ka sayar min sauran bayin naka. Zan baka kashi biyu cikin uku na kudin anan Madeena. Sauran kashi dayan kuma a garin Sham.
Zul Kala'i yace masa "Ka jinkirta mun zuwa gobe zanyi tunani game da abinda ka fa'da".
Sai ya koma gida ya 'yantar dasu baki daya.
Yayin da gari ya waye Sayyiduna Umar (rta) ya tambayeshi "Menene ra'ayinka game da abinda na fa'da akan sha'anin bayinka?".
Sai Zul Kala'i yace "Ai Allah ya za'ba mana abinda yafi alkhairi garemu ni dasu, fiye da abinda ka fa'da".
Yace "Me kenan?".
Yace "Gaba dayansu sun zama 'Yantattu domin Allah Madaukakin Sarki".
Sai Sayyiduna Umar yace "Lallai ka dace Ya Kai Zul Kala'i ".
Sai yace "Ya Kai Sarkin Muminai! Hakika ni ina da wani Zunubi wanda bana Tsammanin Allah zai gafarta min shi".
Sayyiduna Umar yace "Wanne irin laifi ne haka?".
Zul Kala'i yace "Watarana na boye ma Mutanen dake yin bauta gareni, sannan na bayyana garesu bisa wani waje mai tsawo.
"Nan take sai da Mutane dubu dari da wani abu suka fa'di sukayi Sujadah gareni".
Sai Sayyiduna Umar (rta) yace masa "Hakika ita tuba tare da ikhlasi da kuma mayat da zuciya zuwa ga Allah, da kuma dena aikata zunubi, ana fatan samun gafara tare da rangwame na Allah".
"Allah Madaukakin Sarki yace "KADA KU FIDDA TSAMMANI DAGA RAHAMAR ALLAH".
Ulwan bn Dawud ya karbo daga wani mutum acikin mutanensa yana cewa :
"Azamanin Jahiliyyah Mutanen gidanmu sun aikeni da Kyautuka zuwa ga Zul Kala'i. Sai da na zauna tsawon shekara guda akofar gidansa ban samu damar shiga wajensa ba.
Sannan watarana da ya leko daga saman benensa, duk mutanen dake kewaye da benen nasa babu wani wanda bai zube Qas yayi Sujjadah gareshi ba. Sannan yayi umurni aka karbi kyautukan kowa.
Bayan shigarsa Musulunci kuwa ya rungumi rayuwa irin ta talauci kuma ya zauna cikin ibadah da tsoron Allah har karshen rayuwarsa.
Alhamdulillah Ya Allah ka Qarfafi imaninmu ka kiyayemu daga sa'ba maka, ka kyautata karshenmu kasa mu cika dal imani. Ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU (29/09/2017 )

0 comments:
Post a Comment