Taqaitaccen fashin baqi akan hirar da ta gudana, Ta tambaya da amsa, Tsakanin mal nura mujahid da Dr. ahmed gumi ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday 11 July 2017

Taqaitaccen fashin baqi akan hirar da ta gudana, Ta tambaya da amsa, Tsakanin mal nura mujahid da Dr. ahmed gumi

TAQAITACCEN FASHIN BAQI AKAN HIRAR DA TA GUDANA
TA TAMBAYA DA AMSA , TSAKANIN MALAM NURA
MUJAHID DA DR. AHMAD GUMI .





Babu shakka dukkan wanda ya saurari wannan hirar da ta
gabata , zaiga babu wani abu da DR. Gumi ya gyara na
miyagun aqidunsa , kuma babu wata kwaskwarima da yayi
akan wata aqida ta mavarnata da ake jifan shi da ita , babu
abunda DR. Gumi yayi acikin hirar sai qara fito da miyagun
aqidun Sa na riqaqqun YAN BIDI'A.
Zamuyi taqaitaccen tsokaci akan miyagun aqidun da ya
tabbatar dasu acikin hirar:



1. DR. GUMI YAYI INKARIN HUJJA DA HADISI AHAD A
BABIN AQIDA DA BABIN FIQHU .



NI KUMA NACE :



Wannan aqida ta DR.Gumi aqidace tsohuwa ta maqiya saqon
manzanni , Asalin wadanda suka fara gudana akan wannan
aqidar wurin soke saqon manzanni sune mushrikai ; su suna
ganin bazasu karvi SAQON Allah ba sai idan yazo ta hanyar
tawaturi , Allah ya tabbatar da hakan daga garesu inda suke
cewa :



" ﺃﺑﺸﺮﺍ ﻣﻨﺎ ﻭﺍﺣﺪﺍ ﻧﺘﺒﻌﻪ ﺇﻧﺎ ﺇﺫﻥ ﻟﻔﻲ ﺿﻼﻝ ﻭﺳﻌﺮ "


ﻭﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ :
" ﻓﻠﻮﻻ ﺃﻟﻘﻲ ﻋﻠﻴﻪ ﺃﺳﻮﺭﺓ ﻣﻦ ﺫﻫﺐ ﺃﻭ ﺟﺎﺀ ﻣﻌﻪ ﺍﻟﻤﻼﺀﻛﺔ ﻣﻘﺘﺮﻧﻴﻦ "



Daga baya qungiyar bidi'a ta mu'tazila sai suka dauko
wannan qa'idar daga mushrikai , suka fara aiki da ita domin
su rushe hadisan Manzan Allah !!
Sai mu'tazila sukace a mas'ala ta aqida dolene hadisi yazama
mutawaturi kuma ya dace da hankalinsu kafin su karve shi !!!


Al'imam Assam'any yana cewa gameda su :


: ﻭﺇﻧﻤﺎ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺬﻛﺮ ﺃﻥ ﺧﺒﺮ ﺍﻟﻮﺍﺣﺪ ﻻ ﻳﻔﻴﺪ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺑﺤﺎﻝ ، ﻭﻻ
ﺑﺪ ﻣﻦ ﻧﻘﻠﻪ ﺑﻄﺮﻳﻖ ﺍﻟﺘﻮﺍﺗﺮ ﻟﻮﻗﻮﻉ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺑﻪ ، ﺷﻲﺀ ﺍﺧﺘﺮﻋﻪ ﺍﻟﻘﺪﺭﻳﺔ
ﻭﺍﻟﻤﻌﺘﺰﻟﺔ ، ﻭﻛﺎﻥ ﻗﺼﺪﻫﻢ ﺑﺬﻟﻚ ﺭﺩ ﺍﻷﺧﺒﺎﺭ "
‏( ﺍﻟﺤﺠﺔ ﻓﻲ ﺑﻴﺎﻥ ﺍﻟﻤﺤﺠﺔ ، ٢١٤ /٢ )


Magabatan Musulmi sunyi ijma'i akan aiki da hàdisi ÃHÃD da
karvansa bisa yaqini , da karvan Sa acikin dukkan babuka na
addini , babu wadanda suka savawa haka sai YAN BIDI'A !!


ﻗﺎﻝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ :
" ﺑﻞ ﻛﺎﻧﻮﺍ ‏( ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ‏) ﻻ ﻳﺸﻜﻮﻥ ﻓﻲ ﺧﺒﺮ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﻣﻊ ﺗﻔﺮﺩﻩ ﺑﻜﺜﻴﺮ
ﻣﻦ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ، ﻭﻟﻢ ﻳﻘﻞ ﺃﺣﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﻳﻮﻣﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﺪﻫﺮ : ﺧﺒﺮﻙ ﺧﺒﺮ ﻭﺍﺣﺪ ﻻ
ﻳﻔﻴﺪ ﺍﻟﻌﻠﻢ ، ﻭﻛﺎﻥ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﺟﻞ ﻓﻲ ﺻﺪﻭﺭﻫﻢ ﻣﻦ ﺃﻥ ﻳﻘﺎﺑﻞ
ﺑﺬﻟﻚ ....
ﻓﻬﺬﺍ ﺍﻟﺬﻱ ﺍﻋﺘﻤﺪﻩ ﻧﻔﺎﺓ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻋﻦ ﺃﺧﺒﺎﺭ ﺭﺳﻮﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ
ﺧﺮﻗﻮﺍ ﺑﻪ ﭐﺟﻤﺎﻉ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺍﻟﻤﻌﻠﻮﻡ ﺑﺎ ﻟﻀﺮﻭﺭﺓ ﻭﺇﺟﻤﺎﻉ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻴﻦ ،
ﻭﺇﺟﻤﺎﻉ ﺃﺀﻣﺔ ﺍﻹﺳﻼﻡ ، ﻭﻭﺍﻓﻘﻮﺍ ﺍﻟﻤﻌﺘﺰﻟﺔ ﻭﺍﻟﺠﻬﻤﻴﺔ ﻭﺍﻟﺮﺍﻓﻀﺔ
ﻭﺍﻟﺨﻮﺍﺭﺝ "
‏( ﺍﻟﺼﻮﺍﻋﻖ ﺍﻟﻤﺤﺮﻗﺔ ، ٨٦١ )


WATO ASALI SU MU'TAZILA BASA KARVAN HADISI ÃHÃD NE
A BABIN AQIDA KAWAI , SAI KUMA AKA SAMU WASU YAN
BIDIAN SU KUMA SUKA WARE BABIN FIQHU , SUKACE
BAZASU KARVI HADISI AHAD BA ACIKIN SA , IBN
TAIMIYYAH YANA MARTANI AKAN WADANNAN YAN BID’AR
SAI YAKE CEWA :


" ﻭﻛﺬﻟﻚ ﺃﺻﻮﻝ ﺳﺎﺀﺭ ﺍﻷﺀﻣﺔ ﻭﺟﻤﻴﻊ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﺍﻷﺧﺒﺎﺭ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ
ﻣﻘﺒﻮﻟﺔ ﻓﻲ ﺟﻤﻴﻊ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻟﺨﺒﺮﻳﺔ ﻭﺍﻟﻌﻤﻠﻴﺔ ،ﺍﻷﺻﻮﻝ ﻭﺍﻟﻔﺮﻭﻉ ،
ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻭﻻ ﻓﻲ ﺍﻷﺀﻣﺔ ﻣﻦ ﻳﺮ ﺍﻟﺨﺒﺮ ﻓﻲ ﺑﺎﺏ ﻣﻦ ﺃﺑﻮﺍﺏ
ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺑﺄﻧﻪ ﺧﺒﺮ ﻭﺍﺣﺪ ، ﻭﻟﻢ ﻳﻨﺸﺄ ﺫﻟﻚ ﺇﻻ ﻣﻦ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﺪﻉ "
‏( ﺍﻻﻋﺘﺮﺍﺿﺎﺕ ﺍﻟﻤﺼﺮﻳﺔ ، ٨٥ ‏)


ﻭﻗﺎﻝ ﺃﻳﻀﺎ :


" ﻭﻫﺬﺍ ﻣﻤﺎ ﺍﺗﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ ﺳﻠﻒ ﺍﻷﻣﺔ ﻭ ﺃﺀﻣﺔ ﺍﻹﺳﻼﻡ : ﺃﻥ ﺍﻟﺨﺒﺮ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ
ﻣﻘﺒﻮﻝ ﻣﺼﺪﻕ ﺑﻪ ﻓﻲ ﺟﻤﻴﻊ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﻌﻠﻢ ، ﻻ ﻳﻔﺮﻕ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻤﺴﺎﺀﻝ
ﺍﻟﻌﻤﻠﻴﺔ ﻭﺍﻟﺨﺒﺮﻳﺔ ، ﻭﻻ ﻳﺮﺩ ﺍﻟﺨﺒﺮ ﻓﻲ ﺑﺎﺏ ﻣﻦ ﺍﻷﺑﻮﺍﺏ ، ﺳﻮﺍﺀ ﻛﺎﻧﺖ
ﺃﺻﻮﻻ ﺃﻭ ﻓﺮﻭﻋﺎ ، ﺑﻜﻮﻧﻪ ﺧﺒﺮ ﻭﺍﺣﺪ ، ﻓﺈﻥ ﻫﺬﺍ ﻣﻦ ﻣﺤﺪﺛﺎﺕ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﺪﻉ
ﺍﻟﻤﺨﺎﻟﻔﺔ ﻟﻠﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ "
‏( ﺍﻻﻋﺘﺮﺍﺿﺎﺕ ﺍﻟﻤﺼﺮﻳﺔ ، ٥٠ )


SANNAN KUMA ANSAMU QUNGIYAR SHI'A RAFIDHA DA
QUNGIYAR JAHMIYYAH SAI SUKUMA SUKAYI WATSI DA
HADISI ÃHÃD GABA DAYA ; YAZAMA BASA KARVAN SA
ACIKIN DUKKAN BABUKAN ADDININ .
WADANNAN SUNE SUKA DACE DA MUSHRIKAI CIF_CIF
AKAN AQIDAR SU TA INKARIN SAQO NA 'DAI'DAIKUN
MUTANE .


AL'IMAMUSH SHADIBY YANA CEWA GAMEDA SU :


" ﻭ ﺫﻫﺒﺖ ﻃﺎﺀﻓﺔ ﺇﻟﻰ ﻧﻔﻲ ﺍﻷﺧﺒﺎﺭ ﺍﻵﺣﺎﺩ ﺟﻤﻠﺔ ، ﻭﺍﻻﻗﺘﺼﺎﺭ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ
ﺍﺳﺘﺤﺴﻨﺘﻪ ﻋﻘﻮﻟﻬﻢ ﻓﻲ ﻓﻬﻢ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ...
ﻓﻔﻲ ﻫﺎﺅﻻﺀ ﻭﺃﻣﺜﺎﻟﻬﻢ ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ : ﻻ ﺃﻟﻔﻴﻦ
ﺃﺣﺪﻛﻢ ﻣﺘﻚﺀﺍ ﻋﻠﻰ ﺃﺭﻳﻜﺘﻪ ، ﻳﺄﺗﻴﻪ ﺍﻷﻣﺮ ﻣﻦ ﺃﻣﺮﻱ ، ﻣﻤﺎ ﺃﻣﺮﺕ ﺑﻪ ﺃﻭ
ﻧﻬﻴﺖ ﻋﻨﻪ ، ﻓﻴﻘﻮﻝ : ﻻ ﺃﺩﺭﻱ ، ﻣﺎ ﻭﺟﺪﻧﺎ ﻓﻲ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺗﺒﻌﻨﺎﻩ "
ﻭﻫﺬﺍ ﻭﻋﻴﺪ ﺷﺪﻳﺪ ﺗﻀﻤﻨﻪ ﺍﻟﻨﻬﻲ ، ﻻﺣﻖ ﺑﻤﻦ ﺍﺭﺗﻜﺐ ﺭﺩ ﺍﻟﺴﻨﺔ "
‏( ﺍﻻﻋﺘﺼﺎﻡ ، ١٦٥ ‏)


ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺴﺮﺧﺴﻲ ﺍﻟﺤﻨﻔﻲ :


" ﻭﻗﺎﻝ ﺑﻌﺾ ﻣﻦ ﻻ ﻳﻌﺖ ﺑﻘﻮﻟﻪ : ﺧﺒﺮ ﺍﻵﺣﺎﺩ ﻻ ﻳﻜﻮﻥ ﺣﺠﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ
ﺃﺻﻼ "
‏( ﺃﺻﻮﻝ ﺍﻟﺴﺮﺧﺴﻲ ، ٣٢١ ‏)


ﻭﻗﺎﻝ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺎﺟﺐ ﺍﻟﻤﺎﻟﻜﻲ :


" ﻳﺠﺐ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺑﺨﺒﺮ ﺍﻟﻮﺍﺣﺪ ﺍﻟﻌﺪﻝ ، ﺧﻼﻓﺎ ﻟﻠﻘﺎﺳﺎﻧﻲ ﻭﺍﺑﻦ ﺩﺍﻭﺩ
ﻭﺍﻟﺮﻭﺍﻓﺾ "
‏( ﺷﺮﺡ ﺍﻟﻌﻀﺪ ، ١٣٩ )



SABODA HAKA AQIDAR DR. GUMI TA INKARIN HADISI ÃHAD
A JUMLACE , AQIDA CE TA QUNGIYAR SHI'A DA JAHMIYYAH
, WACCE TA SAMO ASALI DAGA MUSHRIKAI .



2. DR. GUMI YA RUSHE INGANTATTUN HADISAN ANNABI
GABA DAYAN SU DAGA SU ZAMA HUJJA ACIKIN ADDINI
,BISA HUJJAR CEWA KODA SUN INGANTA TO HADISAN
SUNANAN A MATSAYIN ZATO ; BABU TABBAS A KAN SU !!!


NI KUMA NACE :



WANNAN AQIDA TA DR. GUMI , MA'ANAR TA SHINE :


INKARIN MANZANTAKAN MANZAN ALLAH SALLALLAHU
ALAIHI WA SALLAM .


3. DR. GUMI YA TABBATAR DA MANHAJIN SA MAI CEWA :


" Ba'a kirdadon fahimtar magabata ga nassi acikin mas'ala ta
aqida "


NI KUMA NACE :


WANNAN MANHAJI NÀ DR. GUMI SHINE ASALIN MANHAJIN
DUKKAN QUNGIYOYIN BIDI'A , GUDANA AKAN SA SHI YA
MAIDA SU YAN BID'IA , KUMA HAKAN SHNE TAKEN DUK
WATA QUNGIYAR BIDI'A ,IBN TAIMIYYAH YANA CEWA:


" ﻓﻌﻠﻢ ﺃﻥ ﺷﻌﺎﺭ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﺪﻉ : ﺗﺮﻙ ﺍﻧﺘﺤﺎﻝ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻠﻒ "


‏( ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻱ ، ١٥٥ /٤ )

MANHAJIN AHLUSSUNNAH YA GUDANA NE AKAN
KIRDADON FAHIMTAR MAGABATA GA NASSOSHIN SHARI'A
ACIKIN DUKKAN BABUKAN ADDINI , BASA RARRABEWA
TSAKANIN WANNAN BABIN DA WANCAN ; SUCE BABIN
FIQHU ZA'ABI SALAF , AMMA BABIN AQIDA ZA'AYIWA
SALAF TAWAYE , WANNAN SHINE HAQIQANIN TAFARKI NA
ZINDIQAI DA MULHIDAI !! KUMA BABU WANDA ZAI KAMA
WANNAN TAFARKI FACE YA HALAKA YA FANDAREWA
SHARI'A .


ﻗﺎﻝ ﺷﻴﺦ ﺍﻹﺳﻼﻡ :


” ﻭﻟﻬﺬﺍ ﻣﺎ ﺯﺍﻝ ﻛﻞ ﺫﻱ ﻋﻘﻞ ﻭ ﺩﻳﻦ ﻳﺮﺩﻭﻥ ﻋﻠﻢ ﻣﻌﺎﻧﻲ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ
ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﻭ ﺍﻟﻔﻘﻬﺎﺀ ﻓﻴﻪ ، ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺗﻠﻘﻮﻩ ﻃﺒﻘﺔ ﺑﻌﺪ ﻃﺒﻘﺔ ، ﻣﻴﺮﺍﺛﺎ
ﻣﺤﻔﻮﻇﺎ "

‏( ﺍﻻﻋﺘﺮﺍﺿﺎﺕ ، ٣٠ ‏)

ﻭﻗﺎﻝ ﺃﻳﻀﺎ :


"ﺃﻥ ﻣﻦ ﻋﺪﻝ ﻋﻦ ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ، ﻭﻣﺎ ﺭﻭﻭﻩ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ _ ﭐﻣﺎ ﺳﺎﻟﻜﺎ ﻃﺮﻳﻘﺎ ﺃﺧﺮﻯ ﺇﻟﻰ ﻓﻬﻢ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ، ﺇﻭ
ﻣﻌﺮﺿﺎ ﻋﻦ ﺍﻟﺠﻤﻴﻊ _ﻓﻼ ﺑﺪ ﻟﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺠﻬﻞ ﻭﺍﻟﻀﻼﻝ ﻭﺍﻹﻓﻚ ﻭﺍﻟﻤﺤﺎﻝ ،
ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﺷﻔﺎ ﺟﺮﻑ ﻫﺎﺭ ﻳﺆﺩﻳﻪ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻜﻔﺮ ﻭﺍﻟﻨﻔﺎﻕ "
‏( ﺍﻻﻋﺘﺮﺍﺿﺎﺕ ، ٣٠ )


AL'IMAMUSH SHADIBY YANA BAYANIN MANHAJIN YAN
BIDI'A NA GANGANTA SAVAWA SALAF WURIN FAHIMTAR
NASSI SAI YAKE CEWA :


" ﻭﻛﺜﻴﺮﺍ ﻣﺎ ﺗﺠﺪ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻭﺍﻟﻀﻼﻟﺔ ﻳﺴﺘﺪﻟﻮﻥ ﺑﺎ ﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ،
ﻳﺤﻤﻠﻮﻧﻬﺎ ﻣﺬﺍﻫﺒﻬﻢ ، ﻭﻳﻐﺒﺮﻭﻥ ﺑﻤﺘﺸﺒﻬﺎﺗﻬﻤﺎ ﻓﻲ ﻭﺟﻮﻩ ﺍﻟﻌﺎﻣﺔ ،
ﻭﻳﻈﻨﻮﻥ ﺃﻧﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﺷﻲﺀ ...
ﻭﻛﺜﻴﺮ ﻣﻦ ﻣﻦ ﻓﺮﻕ ﺍﻻﻋﺘﻘﺎﺩﺍﺕ ﺗﻌﻠﻖ ﺑﻈﻮﺍﻫﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﻲ
ﺗﺼﺤﻴﺢ ﻣﺎ ﺫﻫﺒﻮﺍ ﺇﻟﻴﻪ ، ﻣﻤﺎ ﻟﻢ ﻳﺠﺮ ﻟﻪ ﺫﻛﺮ ﻭﻻ ﻭﻗﻊ ﺑﺒﺎﺗﻞ ﺃﺣﺪ ﻣﻦ
ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻷﻭﻟﻴﻦ "


‏( ﺍﻟﻤﻮﺍﻓﻘﺎﺕ ﻓﻲ ﺃﺻﻮﻝ ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ، ٥٢/٣ )


SABODA HAKA WANNAN MANHAJI NA DR. GUMI , MANHAJI
WANDA DUKKAN YAN BIDI'A SUNYI ITTIFAQI AKAN GUDANA
AKAN SÀ ; GUDANA AKAN SA MA SHINE TAKEN SU .
SAURAN ABUBUWAN DA DR. GUMI YA TABBATAR A
WANNAN HIRAR WANDA KUMA MUNSHA YIN RUBUTU AKAN
SU , SUNE KAMAR HAKA :


4. AQIDAR CIN KARO TSAKANIN ALQUR'ANI DA HADISI :

# wannan Aqidar qungiyar Khawarij ne .

5. AQIDAR GABATAR DA RA'AYI AKAN NASSI INGANTACCE .


#wannan aqidar dukkan YAN BIDI'AR ILMUL KALAM ne
,asalin ta kuma aqidar IBLIS NE .

6. AQIDAR CEWA DUK HADISIN DA BAYA CIKIN BUKHARI
BOLA NE .

#wannan yana daga cikin jinsin aqidar wasu YAN BIDI'A da
suka bayyan a qarni hudu ; ganin :duka _duka hadisan da
suka inghanta basukai dubu goma ba.


Alhakim Annaisabury yana cewa gameda da su :


ﻭﻗﺪ ﻧﺒﻎ ﻓﻲ ﻋﺼﺮﻧﺎ ﻫﺬﺍ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺒﺘﺪﻋﺔ ﻳﺸﻤﺘﻮﻥ ﺑﺮﻭﺍﺓ ﺍﻵﺛﺎﺭ ،
ﺑﺄﻥ ﺟﻤﻴﻊ ﻣﺎ ﻳﺼﺢ ﻋﻨﺪﻛﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻻ ﻳﺒﻠﻎ ﻋﺸﺮﺓ ﺁﻻﻑ ﺣﺪﻳﺚ "
‏( ﺍﻟﻤﺴﺘﺪﺭﻙ ، ٤٢ /١ )


AMMA SU WADANNAN SUN BAN_BAN TA DA DR. GUMI TA
HANYOYI KAMAR HAKA :

* SU SU AWURIN SU INGANTATTU SUN WUCE DUBU UKU ,
SHI KUMA DR. GUMI YANA GANIN DUBU UKU NE KAWAI BA
BOLA BA , AMMA SAURAN DUKA BOLA NE .

* SU SUNA DAN MUTUNTA MANZAN ALLAH ; BASUYI
TSAURIN IDON CEWA HADISAN SA BOLA BA , AMMA DR.
GUMI BAYA MUTUNTA MANZAN ALLAH , SHIYYASA YAYI
TSAURIN IDON KIRAN HADISAN SA DA BOLA .


* SU AWURIN SU TAYIWU SUYI AIKI DA WADANDA SUKA
WARE SUKACE SU KADAI NE INGANTATTU ,A MATSAYIN
DALILAI NA SHARI'A MASU ZAMAN KAN SU .

ÀMMA SHI DR. GUMI BAYA AIKI DA HADISAN BUKHARIN A
MATSAYIN DALILAI NA SHARI'A MASU ZAMAN KANSU , A'A
YANA KARVBAN SU NE KAWAI A MATSAYIN ABUN
QARFAFA RA'AYI ; MANZAN ALLAH BAIDA MATSAYI A
WURIN SA DA ZAI KARVI SAQONSA KAI TSAYE A MATSAYIN
DALILI NA SHARI'A . ZAI KARVI HADISAN NE KAWAI A
MATSAYIN DALILI DA RAKIYA !!!

SABODA SHI AWURIN SA KODA HADISAN SUN INGHANTA
TO KUMA BAZA'AI AIKI DA SUBA BISA CIN GASHIN KANSU ,
SABODA AWURIN SA HADISAN ZATO NE BASU DA
TABBAS !!!



7 . INKARIN TASIRIN SIHIRI .

*wannan aqida ce ta falasifa da jahmiyyah da mu'tazila .


8. INKARIN SAUKOWAN ANNABI ISA .

#wannan aqida ce ta Jahmiyyah da mu'tazila .


9. INKARIN SHAFAN ALJANU .
#wannan aqida ce ta falasifà da jahmiyyah da mu'tazila .


A TAQAICE WANNAN SHINE TSOKACI AKAN VARNAR DA
DR.AHMED GUMI YA TABBATAR A HIRAR DA YAYI NA TAMBAYA DA
AMSA TARE DA MALAM NURA MUJAHID
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support