Goron sallah 12 daga (kitabu was-sunnah) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 10 July 2017

Goron sallah 12 daga (kitabu was-sunnah)

*GORON SALLAH-12???!!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
:
Yau 15-10-1438, wacce tayi dai dai da 9-7-2017***
:
Taken Lekca
.
*GORON SALLAH-12*
-
Wannan shine bayani na 12
....
....
*ﺇﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ، ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻨﻪ، ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ، ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ*
.
_Bayan haka Wannan shine bayaninda mukesa rai zezama na qarshe idan Allah yaso wato shine zezama nannadar tabarmar wannan goron namu na sallah*****_
             _Akwai wayansu ladubba guda bakwai wayanda malamai suke cewa yanada kyau mutum ya lura dasu a sadda zesha ruwan zam zam****_
_Ladabi nafarko shine anaso kafara ambaton Allah kafin kafarashan ruwa wato mutum yayi bismillah kenan a karon farko kafin yafarasha****_
           _Nabiyu kuma shine anaso kasha dayawa saboda wancan hadisin damukaji manzon Allah (s.a.w) yace munafikai sune basa shan ruwan zam zam da yawa****_
           _Ladabi na uku shine anaso mutum ya fuskanci Alqibla a sadda zesha ruwan zam zam***_
          _Na hudu shine anaso kayi numfashi uku, wato idan kakafa kanka kasha sosai seka cire kashaqi iska kafitar, sannan kasake kafa kai kaqara kwankwada sosai sannan kasake cirewa kayi numfashi anaso kayi haka sau uku****_
            _Nabiyar shine akayi sa6ani akanshi wato shan ruwan Zam Zam a tsaye, wasu malamai suna qidayashi daga cikin ladubban shan ruwan zam zam a tsaye saboda hadisanda akasamo Daga Abdullahi Dan Abbas wayanda Imamu Ahmad yakawosu ciki Musnad:_
*«ﺃَﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﺷَﺮِﺏَ ﻣِﻦْ ﺯَﻣْﺰَﻡَ ﻭَﻫُﻮَ ﻗَﺎﺋِﻢٌ»*
*MANZON ALLAH (S.A.W) YASHA RUWAN ZAM ZAM ALHALIN YANA TSAYE****
*ﻋَﻦِ ﺍﺑْﻦِ ﻋَﺒَّﺎﺱٍ، ‏«ﺃَﻥَّ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲَّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﺷَﺮِﺏَ ﻣِﻦْ ﺩَﻟْﻮٍ ﻣِﻦْ ﺯَﻣْﺰَﻡَ ﻗَﺎﺋِﻤًﺎ»*
*DAGA IBNU ABBAS (RA) LALLAI ANNABI (S.A.W) YASHA RUWAN ZAM ZAM ACIKIN GUGA A TSAYE*
       _Da wayannan hadisan yasa wayansu malamai suke ganin yana daga cikin ladubban shan ruwan shine ashashi a tsaye, amma wasu malamai suna ambata wayansu dalilai wayanda sukace suneG sukasha Annabin yasha ruwan a tsaye dan haka sukace sha atsaye baya daga cikin ladubban shan ruwan****_
          _Ladabi na shida anaso kariqe mazubin ruwan da hannun dama**_
         _Sannan kuma wayannan ladubbanfa base kaje can makka dinba, adu inda kake in aka kawo maka ruwan to anaso kacika wayannan ladubban amma dai ba dole bane****_
            _Na bakwai shine kayiwa Allah godiya bayan kagama shan ruwan sekace Alhamdulillahi sannan kuma sekayi addu'oinda zakayi na neman biyan buqatarka****_
_Amma yana daga cikin kusakuranda mukeyi ayau shine yadda ake surka ruwan zam zam da  wani ruwa wanda bashiba dan wai munaso ya qara yawa, se mutum yasamu jarka guda na ruwa seya diga zam zam kadan aciki seya dinga rabawa mutane wannan kuskurene sannan kuma yana ragema shi zam zam din qarfi****_
         _Aa shi ruwan zam zam din abarshi shi kadai kar ahadashi da komai koda kuwa zezama kadan kadan za,a samu asha yafi alheri akan ahadashi da wani ruwanda bashiba*****_
              _Sannan marasa lafiya yanada kyau duk wata larurarda take damunka ka rungumi ruwan zam zam kamar yadda kukaji wayansu sun samu biyan buqata abaya****_
             _Wato naso ace ni dinnan inada kusanci ko wata hanyarda zata sadani da shugaban najeriya Muhammadu Buhari da se ince wannan jinyarda yakeyi yanzu haka a qasar burtaniya inama ace Qasar Saudiyya suka kaishi yakwashe watan ramadan baki dayanshi acan yana shan ruwan zam zam, kuma musamman ace yana karanta Suratul fatiha aciki sannan ya sha dayawa, yazamana bayacin komai beshan komai face Ruwan zam zam har watan ramadan yaqare, albarkatu guda hudu kenan, nafarko ga Albarkan Qasa me tsarki nabiyu ga Albarkan Shi Zam zam din sannan na uku kuma ga Albarkan watan Ramadan sannan kuma ga Albarkan suratul fatiha, kunga ni naso ace shugaban qasarmu ya hada wayannan hudun a wannan lokacin insha Allahu da tuni yadawo mana tangaran sedai ace jikin tsufa amma dai batun wani zazzabi ko wani guntun rashin lafiya dagudu wannan zerabu dashi insha Allahu****_
            _Amma kuma har yanzu Lokaci be qure manaba inama ace wani daga kusan makusantan shugaban qasar zasuga wannan Goron sallah namu Shugaba Buhari yarabu da qasar Burtaniya yakoma qasar Saudiyya yaduqufa shan ruwan zam zam da Ikon Allah duk wata cutarda take cikin jikinshi seta fita ta rabu dashi****_
         _Ayi haquri abaya nace da wannan zamu nade tabarman goron namu to amma akwai wasu bayanai dadama wayanda suka cancanta ace mun shigar dasu kuma gashi basu samu shigaba dan haka se asake biyomu dai kada agaji****_
:
:
Zamu dakata anan sekuma bayani nagaba Idan Allah yakaimu
=
=
_Almajirinku dan mutanen kabo_
'
_Jameel Alhassan Haruna Kabo_
_Alwahhaby-Assalafy_
.
 Nake mana fatan Alheri wassalamu alaikum
..
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪu ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support