HUKUNCIN MATAR DAKE KALLON ABUBUWAN BATSA :
TAMBAYA TA 2355
********************
Assalamu alaikum Allah gafarta menene hukuncin Wanda shaawa tama yawa kuma bayason kallon batsa amma zuciyarsa ta kasa masa sai da ya kalla yake samun sukuni bayan kuma daga bays yazo yai nadama
Sannan wace adua yakama ta ya ringa karantawa
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Na farko dai wannan alama ce dake nuna Qarancin tsoron Allah azuciyar masu yin haka. Sannan kuma da alamar cewa Zuciyarta tafi Qarfinta.
Allah Madaukakin Sarki ya gaya ma Annabinsa Dawud (alaihis salam) cewq : "... KUMA KADA KABI SON ZUCIYA BALLE TA 'BATAR DAKAI DAGA KAN HANYAR ALLAH.
"HAKIKA WADANNAN DA SUKE 'BATARWA DAGA KAN HANYAR ALLAH, GARESU AKWAI AZABA MAI TSANANI SABODA ABINDA SUKA MANTA NA RANAR HISABI".
Kuma acikin suratu Yusuf (alaihis salam) Allah yace "HAKIKA ITA ZUCIYA LALLAI MAI YIN UMURNI CE GA MUMMUNAN ABU".
Allah shine ya halicci 'Dan Adam kuma ya sanya sha'awa ajikinmu domin ya jarrabemu ya bayyanar da bayinsa masu tsoronsa da kuma wadanda suka karkace daga kan hanyarsa.
Kuma ya kafa mana dokokin da zamu bi domin mu rabauta anan duniya da kuma ranar Qiyamah. Don haka Allah yace ma Annabinsa (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) :
"KA GAYA MA MUMINAI MATA SU RUNTSE DAGA IDANUWANSU KUMA AU KIYAYE FARJOJINSU ....... ".
Wannan umurni ne daga Allah (SWT) zuwa ga Matayen Muminai, bayan kuma ya gargadi Mazaje Muminai.
Kuma Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (rta) yace Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace :
"HAKIKA SHI KALLO, WANI KIBIYA NE MAI DAFI DAGA CIKIN KIBIYOYIN IBLIS. DUK WANDA YA BARI DON TSORONA, ZAN CHANZA MASA DA WANI HASKE (WATO HASKEN IMANI) WANDA ZAI JI DANDANONSA ACIKIN ZUCIYARSA".
(Mu'ujamul Kabeer na Tabaraniy juzu'i na 10 hadisi na 10,362).
Kallon batsa bai halatta ba. Kuma cewa wai sha'awa cw tayi miki yawa ba zai zama uzuri karbabbe agun Allah ba. Don haka kiji tsoron Allah ki rika tuna ranar gamuwarki dashi. Ki kiyaye dukkan gabobin jikinki daga sa'ba masa.
Allah Madaukakin Sarki yana bada labarin ranar Alkiyamah. Yace :
"AWANNAN RANAR DA ZAMU YUMQE (SANYA RUFI) BISA BAKUNANSU, KUMA HANNAYENSU NE ZASU ZANYAR DAMU, KUMA QAFAFUWANSU SUNA SHAIDARWA BISA ABINDA SUKA KASANCE SUNA TATTATAWA (NA LAIFUKA)".
Kiji tsoron ranar tonon asirai, ranar da Allah zai nunoki (kamar a vedio) gaki nan sanda kike aikata ayyukan sharrin da kika aikata..
Idan zaki tuba kiyi cikakkiyar tuba irin wacce Allah yake so. Ba wai tubar Mayaudara ba.
Addu'ar neman shiriya kuwa babu kamar fatiha. Ki rika karantawa tare da halarto girman Ubangiji. Allah mai gafara ne mai rahama. Shi keda ikon shiriya da kuma yin gafara ga bayinsa.
Allah shi gafarta mana baki daya, Aameen.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (11-10-2017 21-01-1439).

0 comments:
Post a Comment