Masu hikima sunce?? (fitowa ta 19) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday 18 July 2017

Masu hikima sunce?? (fitowa ta 19)

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 19

86. Kar ka yi sakaci da abokin gabarka, komai yardar da ya nuna maka in ya samu 'yar kafa zai zaburo maka.

87. Idan masifun zamani suka zaburo maka ka tarye su da rundunar hakuri.

88. In dai kai ba mai yarda da abin da halin zamani yazo maka da shi ba ne, sai ka dau igiya ka rataye kanka.

89. Idan al'amari ya tasar ma karewa , abin da zaka yi ta gani kullum alamomin ne na karewarsa.

90. In Allah ya sa ajalin giwa yana sama, zai ba ta fukafukan da za su kaita inda ajalinta yake.

Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

24/10/1438
18/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support