MASU HIKIMA SUN CE
Fitowa ta 22
3. WASIYYAR DAN HUSAINI
Ga wasiyar Dahiru dan Husain da ya yi wa dansa Abdullahi lokacin da Sarkin Musulmi Ma'mun ya nada shi Gwamnan Rakka da Masar. Ya ce,
"Ya kai dana! Ka zama mai hakuri, domin Allah yana tare da masu hakuri, kuma Allah yana tare da masu tsoronsa, da masu aikata aikin kirki. Bayan wannan ka riki ayyukan mutanen kirki da suka wuce. In kuma ka tasar ma wani al'amari, ka nemi taimakon Ubangijinka a kan sa. Ka dubi al'amurran da ya yi umrni da a aikata su, sai ka aikata su. Ka kuma dubi al'amurran da ya yi umarni a bar su, sai ka bar su. Ka dage bisa ga kwaikwayon Annabinmu Sallallalahu Alaihi wa Sallam, a cikin duk al'amurransa game da al'umma. Kada ka yi adalci ga wanda ka ke so, ka hana wanda kake ki. Ko ga makusancinka ka hana manisanci. Ka fifita ilimi da masanansa, da addini da masu aiki da shi. Kada so da ka yi ma'aikatanka ya hana ka ka kaifafa ido da binciken al'amurranka da ke hannunsu. Ka bincika su da kanka don ka gan su da idonka. Ba adalci ba ne ka sanya wani ya binciko muhimman al'amurra. Duk wanda ka sanya ba zai gano maka su yadda zaka gano ba. Idan kuma ya gano maka su da idonsa, to, harshensa ba zai fada maka su daidai yadda su ke ba. Kada ka manta da cewar Allah a cikin Alkur'ani, "Ka gaggauta aiwatar da haddodin Ubangiji ga masu laifi, bisa gwargwadon yadda kowa ya cancanta. Kada kayi sakaci ko sasauci a cikin yin haka. Domin sakacinka ko sassaucinka a cikinsa zai bata al'amarinka. Ka yawaita shawartar maluma da masana. Ka rinka karbar shawarar wadanda suka jarraba al'amura, da masu hankali, da masu hikima. Kada ka sa jahili tibis cikin mashawartanka, ko wanda ya jahici al'amurra da su ke bijiro maka. Kada ka karbi shawarar da suka yi maka, domin cutarsu ta fi amfaninsu yawa. Idan ka himmatu ga zartar da wani al'amari ka yi tunani kan yadda zai je ya dawo. Idan ka hangi salama, da sawaba a cikinsa, yi maza ka gaggauta shi. Im ba haka ba, to, ka saurara, kada ka aikata shi har sai ka nemi shawarar masanansa.
Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi
Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
27/10/1438
21/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment