Falala da hukuncin kwanciya da tsarki (alwala) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 8 November 2016

Falala da hukuncin kwanciya da tsarki (alwala)

*FALALA DA HUKUNCIN KWANCIYA DA TSARKI (ALWALA).*

A- *FALALAR KWANCIYA DA TSARKI*

@-Wanda ya kwana cikin tsarki,yana kwanane tare da Mala'ika a shinfidarsa, kuma mala'ika yana yimasa addua.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
"Ku tsarkake wannan jiki, sai Allah ya tsarkakeku, domin babu wani bawa da zai kwana cikin tsarki (alwala) face ya kwana tare da Mala'ika acikin mayafinsa,babu wani motsi da bawan zaiyi acikin wani lokaci na dare face yace:
Allah ka gafartawa wannan bawan naka,domin ya kwana cikin tsarki".
#Alban yace Hadisine mai kyau: Saheehut Targheeb

@-Allah yana amsa adduar wanda ya kwanta da tsarki (alwala).
Annabi s.a.w yana cewa:
"Babu wani musulmi da zai kwanta cikin tsarki(alwala) sannan ya tashi cikin dare ya roki Allah alkhairin duniya da na Lahira  cikin dare,face sai Allah ya biya masa buqatarsa".
#Abu Dauda, kuma albany ya ingantasa.
#Ahmad.

@Wanda ya kwanta da tsarki(alwala) kamar mai azumine mai tsayuwar dare.
Amru BN As R.A yana cewa
"Wanda ya kwanta yana mai tsarki kamar mai azumine kuma mai raya dare da ibada".
#Tirmizy da Hakim

B- *HUKUNCIN KWANCIYA DA TSARKI(alwala).*

Malamai suna cewa kwanciya da tsarki ba wajibi bane, Sunnace ta Annabi s.a.w mai hukuncin mustahabbi.
Annabi s.a.w ya kasance idan zai kwanta barci yana yin alwala sannan ya umarci wani daga cikin sahabbansa akan haka.
#Bukhari.

Abinda ake nufin tsarki lokacin kwanciya barci shine alwala saukakkiya wato wadda ba'a wanki uku ba,kuma alwala ba karyewa saboda wani hadasi kamar fitar da iska ko wasa da iyali,saboda alwalace ta barci bata sallaba.
#Duba Umdatul qary.

NB:
Kuma mutum zai yi wannan alwala ko yana da janaba.
Domin an tambayi nana Aisha R.A ya Annabi s.a.w kwanci idan yana da janaba sai tace yakanyi dayan abubuwa ukku:
-ko yayi wankan janaba sai yakwanta ko
-Yayi alwala ko kuma
-yayi Taimama.
#Saheehul Jami'I.

Allah ne mafi sani.

Allah ka bamu ikon kiyaye, amin

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support