Goron sallah 13 daga (kitabu was-sunnah) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 10 July 2017

Goron sallah 13 daga (kitabu was-sunnah)

*GORON SALLAH-13???!!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
:
Yau 15-10-1438, wacce tayi dai dai da 9-7-2017***
:
Taken Lekca
.
*GORON SALLAH-13*
-
Wannan shine bayani na 13
....
....
*ﺇﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ، ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻨﻪ، ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ، ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ*
.
_Bayan haka har yanzu dai muna bayanine gameda waraka wanda zam zam yake zama ga al'umma, sedai mafi yawan mutane basu gane hakanba****_
               _Sau da yawa akan samu yawaitar mutuwar aure saboda mijin yasamu matsala baya iya gamsarda ita matar, to insha Allahu idan kana daga cikin mazajenda suke fama da wannan matsalar to idan kanada hali kayi maza kanemo ruwan zam zam kadingasha idan so samune ma kadinga karanta suratul fatiha aciki kadingasha kuma  kadinga shanshi dayawa kuma kasha shi kana me yaqinin cewa zaka samu waraka sannan kuma kayi addu'a bayan ka gamasha karoqi Allah ya yaye maka wannan matsala, kadauki kamar watanni biyu kanayin hakan*****_
             _Sannan kuma itama macenda bata jin dadi alokacinda suke tarayya da mijinta ita batajin komai, to kema idan kinada irin wannan matsalar sekiyi mar maza ki rungumi zam zam in Allah yaso zakiji chanji bada jimawaba****_
        _Wanda yakeda matsala ta yoyon futsari kaima ka gaggauta rungumar wannan ruwa na zam zam da ikon Allah zaka samu waraka****_
            _Dayawa 'yan mata suna kawo mana qorafin cewa sunaso suyi aure amma babu wanda yake zuwa wajensu dan neman aurensu, to kema idan kina cikin wayanda suke fama da irin wannan matsalar yi marmaza ki riqe wannan ruwa na zam zam kamar yadda mukayi bayaninshi asama insha Allahu zakisha mamaki*****_
          _Wani kuma seyace shi yawan mantuwace matsalarsa duk abinda ya karanta babu wuya zeji kawai ya manta, kaima nemi zam zam kadinga tofa suratul fatiha aciki kanasha da Ikon Allah zakasha mamaki*****_
             _Sau dayawa larura takan samu mutum kuma aje asibiti likitoci su aunashi suce su basuga ciwoba bayan kuma shi yasan irin radadinda yakeji acikin jikinshi, to kaima in kanada irin wannan matsalar yi maza kanemi ruwan zam zam kadinga karanta fatiha acikinsa kanasha da ikon Allah tangaran garau zaka koma duk wannan radadin seka dena jinshi***_
             _Wani kuma zakaji yace baya iya yin azumi saboda olsa, to kaima marmaza nemi Zam zam tun yanzu kadinga tofa fatiha aciki kanasha da ikon Allah ramadan mezuwa dakai zamu azumceshi ko daya bazakasha ba sedai wani dalili daban yasaka kasha azumin amma dai ba olsa ba insha Allahu****_
_Wanda yake fama da cutar kansa shima yasamu zam zam ya dinga yayyafawa awajen yanasha, yanasha yana wanke ciwon dashi, da ikon Allah shima zega abin mamaki****_
             _Mace me ciki ko wacce tafara naquda asamu ruwan zam zam tadingasha da ikon Allah zata haihu lami lafiya***_
         _Amma dai malamai sunce makaruhine adinga tsarki da ruwan zam zam, shinema yasa aqasar saudiyya zakuga sunjawo ruwa daga teku wanda dashine ake tsarki kuma zakuga sun rubuta cewa kada asha wannan ruwan***_
        _Amma kuma babu laifi ayi wanka dashi ko a wanke gawa dashi, kamar yadda Abdullahi bin Zubair ya wanke Asma'u dashi saboda neman dacewa da albarkarda take cikinshi***_
_Wanda yakeda matsala irinta Duddimi kaoma kasamu zam zam ka dinga wanke fuskarka dashi kuma kadinga sha, da ikon Allah zaka warke tangaran****_
      _Duk wata cutarda take damunka koda Qanjamau ne ko Ebola da ikon Allah idan ka lizimci shan ruwan zam zam zaka warke tangarau****_
           _Mata wayanda suketa faman wahalarda kansu suna neman magunguna na bature duk dan su samu kar6uwa a wajen mazajensu to kuma kudena zuwa kuna 6ata kudadenku kuna siyan abinda yake cutarda rayuwarku, kawai kukama zam zam da ikon Allah buqatarku zata biya bama kan ba, har qafa da duga digan mijin zaki samu matuqar kinyi imani da Allah kuma kina kyautata mu'amala sannan kina yawaita shan ruwan zam zam din kina roqon Allah biyan buqatunki*****_
           _Sannan kuma ga wanda Allah yasa yasamu zuwa aikin hajji shima anaso kafin yakaiga yin dawafi na bankwana ya dage ya cika cikinshi dam da ruwan zam zam***_
           _Mata dasuke fama da matsalar  Impection kuma kuriqe wannan ruwan dakyau kamar yadda mukayi bayani asama da ikon Allah zakuji dadinshi***_
         _Abincine ga me jin yunwa, sannan kuma maganine ga mara lafiya inji rasulullahi (s.a.w) duk wata cutarda tadameka ko wacce irice ruwan zam zam yana maganinta da ikon Allah*****_
 =
_Alhamdulillahi anan mukazo qarshen wannan lekcar, amdadin daukacin wayanda suka tallafamin har wayannan bayanai sukazo gareku****_
::
==
_Almajirinku dan mutanen kabo_
'
_Jameel Alhassan Haruna Kabo_
_Alwahhaby-Assalafy_
.
 Nake mana fatan Alheri wassalamu alaikum
..
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support