MASU HIKIMA SUN CE
Fitowa ta 14
66. Lalle da jaki na magana, da ba ya rasa abin da zai fadi game da Ubangijinsa.
67. Ana ba ka don abu uku: Na daya, ana ba ka don ana jin tsoron ka. Na biyu, ana ba ka, don ana kwadayin a wurinka. Na uku, ana baka, don ana jin tausayin ka. Wanda ya fi dadi duk a cikin su, a ba ka don kwadayin a wurinka. Wanda ya fi muni kuwa shi ne a ba ka don ana jin tsoron ka.
68. Duk yadda ka yi gudu ba ka cim inuwarka.
69. Da za wuni, ka kwana kana tambayar agogo lokaci, ya dai iya nuna maka a fili, amma ba shi da bakin da zai fada ma ka..
70. Gaskiyar da ba a da iko a zartar da ita, gwamma kada a fade ta.
Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi
Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
19/10/1438
13/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment