DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 20
96. Idan kwalba ta fashe za a ji kukan fashewarta ne sau daya amma za a taka ta sau goma. Haka mummunar magana ta ke idan aka fade ta, za a ji ta sau daya, amma za ta dade tana zungurar zukata.
97. Aboki guda daya ne zai taya ka kwanciyar kabari. Shi ne aikinka. Aikata alheri don ka samu aboki na kwarai a wannan kogo da ba shi da makawa.
98. Abu uku su na bata lokaci ne: Da-na-sanin abin da ya wuce kuma ba zai dawo ba, da neman yardar mutane gaba daya kuma ba za ta samu ba, da hada kanka da wanda ya fi ka kuma ba za ka cim ma sa ba.
99. Wanda ya fi kowa wadata ba lalle ne ya fi ka arziki ba. Wadatacce shi ne wanda yake samun biyan bukatunsa.
100. Idan ka ga mutum yana sukar dan uwansa bai lura da nasa laifin ba. Ku sukar dan uwanka da ka ke yi shi ma aibi ne.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
25/10/1438
19/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment