MASU HIKIMA SUN CE
Fitowa ta 15
71. Mai neman duniya, da mai neman lahira, kamar mai sana'ar jima da mai sayar da turare ne. Mai sana'ar jima yana son mai sayar da turare ya kusance shi, don ya rika jin kamshi. Mai sayar da turare kuwa, ba ya kaunar ya zo kusa da mai sana'ar jima, don warin sana'arsa.
72. Komai yawan dukiyar wanda a ke bi shi da kwanciyar hankali.
73. Wanda bai yi sata ba ba ya fargaba in ya ga mabiyan sawu.
74. Ba kamar mutum uku a duniya: Na farko wanda ya so ka, sa'ar da kowa ya ki ka. Na biyu, wanda ya ba ka sa'ar da kowa ya hana ka. Na uku, wanda ya zo maka, sa'ar da kowa ya guje ka.
75. In za ka yi aure kada ka yi don sha'awa, sai dai ka yi don asali, ko addini, ko hali mai kyau.
Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi
Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
20/10/1438
14/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment