DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 11
51. Kada ka damu da abin da ya wuce, don ba zai dawo ba. Kada yau ta sha ma kai, domin gobe ma rana ce.
52. Yafe wanda ya cuce ka ni'ima ce. Tuna abin bakin ciki da damuwa wahala ce. Manta alheri butulci ne.
53. Babban zunubi ne ka ci naman wanda ya mutu. Ba za ka iya gaya ma sa a nan duniya ba, shi kuma ba zai yafe ma ka ba a gobe kiyama!
54. Kafin ka roki Allah abin da ba ka da shi, ka fara gode ma sa a kan abin da kake dashi, fon shi ne ya ba ka.
55. A da can mutane ba su da asibitoci amma suna da lafiya. Ba su da yawan kudi amma suna da arziki. Ba yawan makarantu amma akwai ilimi. Ba hanyoyin sufuri da na sadarwa amma akwai sada zumunci. Ba su da yawan ni'imomi, amma suna da jin dadi. Ko ka san dalili? "Albarkar abu ta fi yawansa".
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
16/10/1438
10/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment