Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 18) dr.mansur ibrahim sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday 17 July 2017

Masu hikima sunce ?? (fitowa ta 18) dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 18

81. Itaciyar da ba ta da 'ya'yan da zaka iya amfani da ita su, ko inuwar da za ka ji dadinta, ko bawon da za ka yi igiyoyi da shi, yi maza ka maishe ta makamashin wuta

82. Mutumin da ya so ya taimake ka, lalle in ya so cutar ka zai cuce ka.

83. Duk al'amarin da ka tasar ma, amma ba ka zo masa ta kofarsa ba, ka tabbata ka kuskure shi.

84. Ya kamata kowa yayi kokarin a cikin neman abincinsa, amma fa kar ya manta da Allah.

85. Kowane mai rai ransa aro ne. Komai dadewar abin aro kuwa, mai shi zai karba.

Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

23/10/1438
17/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support