DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 22
106. Ba kowane lokaci ne mutane za su fahimce ka ba. Karamar kwakwalwa ba ta gane manyan kalamai. Babban kifi sai babbar gora.
107. Ana sanin darajar mutum ne ta hanyar halinsa ba ta hanyar matsayin gidansu ba. Gina kanka da kanka. Ka daina gadara da matsayin gidanku.
108. Da yawa wadanda ke ce ma 'ya'yansu: "Ina son ka zama Likita" ".. Ka zama Injiniya" ".. Ka zama Malami". Mutum nawa ne su ke ce ma dansu: " Ina son ka zama mai albarka, mai taimakon jama'a"?
109. Kada ka damu da cewa karya ta mike kafa. Tabbas karya za ta gushe. Kada ka damu da tambayar yaushe ne gaskiya za ta bayyana? Lalle za ta bayyana komai dadewa. Abin da ya kamata ya dame ka shi ne, mine ne matsayinka; a kan gaskiya ka ke ko a'a?
110. Rayuwa a kullum cikin canji take. Yaro zai girma, babba ya tsufa, mai lafiya ya yi ciwo, wani mai ciwo ya warke, rayayye kuma ya mutu. Lokacin da ka samu sannan wani zaai rasa. Idan ka fadi wani ne zai tashi. Rungumi hukuncin Allah a cikin amincewa da yarda.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
27/10/1438
21/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment