Taskar falaq da nas ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 10 July 2017

Taskar falaq da nas

TASKAR FALAQI DA NASI.

Daga taskar Dan uwa mal Mustapha Musa Abu Aisha.

Yahudawa sunyiwa Manzon Allah ﷺ ta hanyar Labidi bnul A'asam,kuma Sihirin yayi tasiri akan Manzon Allah ﷺ da yardar Allah,dan Allah ya tabbatar da abu guda biyu;-
-Tabbatar da cewa Manzon Allah ﷺ mutum ne kuma bawan Allah,kuma Allah yana iya jarabtarsa kuma baya baimallaki komai ba acikin Rububiyyar Allah.
-Tabbatar da cewa sihiri yana tasirine akan kowa da Izin Allah akan kowa.

-Sannan dan akarantar da Al'ummar Annabi Muhammad ﷺ hanyar warware Sihiri ta hanya ingantacciya,da kuma hanyar samun kariya daga kamuwa daga Sihiri.

Sunyi Sihirin ne da Comb na Manzon Allah ﷺ da yake gyara gashi da shi,tare da sauran gashinsa da yake jikin comb din,suka sanya a cikin wata rijiya a garin Madina da ake kiranta *Bi'iru Garwan*

*Waraka daga sihiri yana cikin Falaqi da Nasi*

Sai wannan Sihiri yayi ta cutar da Manzon Allah ﷺ,sai Manzon Allah yayi ta addu'a yana ta rokon Allah,sai Allah ya nuna masa warakarsa daga wannan sihiri ta abu guda biyu;-
*Dauko wannan sirin da wararesa tare da karanta Falaqi da Nasi lokacin warware wannan sihiri*

Manzon Allah ﷺ ya aiki sabbai suka shiga wannan Rijiya suka dauko wannan sihiri.

*Wararare Sihiri da Falaqi da Nasi*

Bayan an fiddo wannan sihiri sai Allah ya saukowa da Manzon Allah ﷺ Surorin Falaqi da nasi.

Sihirin da sukayiwa Manzon Allah ﷺ yana da kulle guda 11,suma surorin Falaqi da Nasi suna da ayoyi guda 11,sai Manzon Allah ﷺ  duk lokacin da ya karanta aya daya sai ya warware kulli guda daya,yana gama karanta surorin ya gama kunce kullukan gaba daya,sai ya sami lafiya kamar bai taba ciwo ba.

*Falaqi da Nasi sunfi komai amfani ga rayuwar dan Adam*

Ibn Qaiyim Allah yayi masa Rahama yana cewa:
"Buqatar da mutum yake da ita game da falaqi da Nasi yafi buqatar da ransa take da ita akan ruwa da abinci da Iska,da tufafi da Muhalli,domin idan babu Falaqi da Nasi babu yanda za'ayi mutum ya sami nutsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarsa"

*Maganin Falaqi da Nasi*

Falaqi da nasi suna maganin dukkan wani sharri da cutar mutum da aljani da yardar Allah,shi yasa mafi tsadar Ruqyar Manzon Allah ﷺ idan baya da lafiya ko zai yiwa waninsa shine ya karanta falaqi da Nasi da Qulhuwa,hatta a lokacin rashin lafiyar na ajali nana A'isha R.A ta kasance tana karanta masa Falaqi da Nasi da Qulhuw alokacin da baya iya karantawa saboda rashin lafiya.

Rashin karanta falaqi da nasi da rashin yawan anfani da su shine babban dalilin yaduwar dukkan wani sharri abaya kasa,da zamu dawo mu rungume su da Minsami waraka daga dukkan wani sharri baki daya.

Allah ne mafi sani

Mu hadu a darasi na gaba Insha Allah.

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support