Duniyarfatawa.com™: Sa'adatul Muslim

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Showing posts with label Sa'adatul Muslim. Show all posts
Showing posts with label Sa'adatul Muslim. Show all posts

Tuesday, 7 November 2017

Yaduwar bin bokaye!!?

```YADUWAR BIN BOKAYE```
~~~~~~~~~~~~~~~~


_Godiya ta tabbata ga Allah, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah da mutanen gidansa, da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa._
.
.
_Bayan haka wani abun takaici dake faruwa shine yadda zaka ga da yawa daga cikin matayen arewacin Nigeria sun jefa kansu a cikin mummunar hallaka ta sanadiyyar bakin kishi akan kishiya. Wasu mata saboda tsabar bin bokaye da 'yan duba da 'yan bori har su kansu ma sun zama matsafa qarfi da yaji, wasu kuma sun zama mazinata, suna zuwa suna zina da bokaye domin samun biyan miyagun bukatunsu._

_Akwai wasu Qawaye masu bin bokaye da faɗa ya tashi a tsakaninsu, suna yiwa juna gori sai wata tace ma ɗayar, ai yaron da kike goye dashi kema kin san ba ɗan mijinki ba ne, ɗan gidan boka wane ne. Haka dai suka rika tona ma juna asiri._

_Wasu kuma sun talauce su lalace, duk abun hannunsu ya qare saboda bin bokaye, wasu kuma addinin na su da imaninsu ma duk sun lalata, sun fi imani da maganar bokaye fiye da maganar Ubangijin su._

_Amma sai naga mafi yawan masu tofa albarkacin sunfi alaqanta abun da jahilci, ko duhun kai, alhali kuma gaskiya abun ba haka bane_

_A yanzu zaka tarar da mafiya yawan masu bin bokaye din nan, mataye ne wayayyu, 'yan boko masu aji, waɗanda ake ganin kamar kansu yaji gishiri. Kuma zaka tarar mafiya yawansu suna zuwa Islamiyyan ballantana ace basu san haramcin abun bane._

_Kuma matsalar tafi aukuwa a tsananin matayen Attajirai, 'yan siyasa da masu mulki, da sauran masu hannu da shuni. Amma yawancin matan talakawa suna fama da abin da zasu ci, koda suna son bin bokaye basu da bayarwa._

_Irin wannan harkar ta bokanci da tsafe-tsafe ta shigo har cikin kafofin sadarwa na yanar gizo wato (social media) kamar su whatsapp da Facebook. Yanzu haka akwai groups da pages da suke tallata wani abu wai shi *(Goron Tula)* wai wani abu ne wanda idan mace tayi amfani da shi, mijinta zai rikice wajen kaunarta har sai ya rabu da dukkan matansa, wai har kyautuka zai rika yi mata don dolensa!.._

_Dasu turaren jan hankali maza, da na korar kishiya da dai sauran su. Kuma matan dake wannan Sana'a r kullum sai kara yawa sukayi, kuma basu 6oye ma kowa abin da sukayi.._

_Abinda muke so mata su gane shine: bokanci ko harka da boka, ko amfani da kayan bokanci, duk haramun ne, kum hukuncin masu yinsa shine kafirci._

_Idan kikaje wajen boka kuma kika gaskatashi kin kafirce kenan, kuma ba zaki gane cewa ke kafira bace sai lokacin mutuwarki (sanda bubu lokacin tuba)_.

_Idan kika je lahira babu imani, to fa babu wata alfarmar da zaki samu a wajen Allah. Babu ceto gare ki, babu fita daga wuta, babu shiga Aljannah, babu shan ruwan Alkausara._

_kuma maganin mallakar miji ba zai mallaka miki tsarkakakkiyar soyayyarsa ba, kuma ba zai janyo miki samun soyayyar Allah ba, balle cikawa da imani._

_Duk wulakanci ko bambancin da kike gani agidan mijinki, to kiyi hakuri kiyi addu'a shine mafita, Allah ne yake juya al'amura ba boka ko malamin duba ba._

_Imaninki shine babban jarinki Aduniya da lahira, idan kika rasashi kin afka cikin talaucin da ba zaki sake yin arziki ba. Har abada. Allah ya tsare mana imaninmu._
=
=
Allah Ta'ala yasa mudace.
=
=
```DAN UWANKU HAR KULLUM ```:
IBrahim Abubakar Hamza




Share:

Thursday, 12 October 2017

HUKUNCIN MAI WASA DA SALLAH A MAHANGAR MUSULINCI

```HUKUNCIN MAI WASA DA SALLAH A MAHANGAR MUSULINCI``` ............................................... _Allah madaukakin sarki acikin Suratu Maryam aya ta 59 yana cewa "Sai waɗansu 'yan bãya sukazo a bãyansu suka tõzarta sallah kuma suka bi sha'awõwinsu. To, da sannu a hankali za'a jefasu cikin Gayyah" Allah ta'ala yace "Sai dai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai" suratu Maryam 60_ . _Babban sahabin nan Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda yace "Ba wai sun wulakanta sallah bane ta hanyar barin ta ba, aa kawai  dai sun kasance ne suna jinkirta yin ta ne akan lokacin ta"  kunga kenan da wannan fassara na Ibn Abbas zamu fahimci cewa lallai wadanda suke jinkirta sallah akan lokacin ta wato basuyin ta sai lokacin da suka ga dama to wannan ayar dasu take magana, wadanda suka kasance suna wulakanta sallah da sannu a hankali zasu afka cikin wutar gayyah bayan mutuwar su, lallai kuma zamu fahimci cewa wancan ayar fa ba wai tana magana akan kafirai bane aa tana magana ne akan wadanda suke ikirari cewa lallai fa su musulmi ne!  Dan uwa mai karatu yaya kake ganin yanda rayuwar mu ta kasance a yau?_ . _Sa'ed Ibnul Musayyib Imamt-Tabi'een Allah yayi masa rahama yana cewa dangane da wancan ayar sai yace "Sune wadanda  basuyin sallar Azahar har sai lokacin sallar la'asar, kuma basuyin sallar la'asar har sai lokacin maghriba yayi, kuma basuyin sallar maghriba har sai lokacin sallar Isha'i yayi kuma basuyin sallar Isha'i har sai lokacin sallar asuba yayi, kuma basuyin sallar Asuba har sai rana ta fito, kuma lallai ku sani duk wanda ya mutu yana acikin masu irin wannan hālin alhali bai tuba ba to alkawarin Allah a tattare dashi itace wutar gayya! Wato gayya wani kwari ne acikin wutar jahannama wanda yake da zurfi mai nīsa kuma zasu dika cin wani mummunan abinci mai wari da daci da uqūba"_ . _Allah ta'ala yana cewa  فَوَيْلٌ لِّلْمُصَلِّينَ  ma'ana "To, bone (rijiyar azaba) ta tabbata ga masallata"  amma sai ya kara da cewa الَّذِينَ هُمْ عَن صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ  ma'ana  "Waɗanda suke masu shagala daga sallar su"  wato abinda ake nufisuna shagala daga sallarsu ana nufin suna jinkirtata daga yinta akan lokaci, dan uwa kaduba fa nan maganar Allah ta'ala ne akan masu jinkirta sallah har yace  masu Rijiyar azaba ta tabbata akan su, anya kuwa muna tsoron Allah! Gamu da rayukan mu bazamu hankalta ba kuma  bazamu tunani ba tun kafin Allah yace wa mala'ikan mutuwa Emergency Operation aje a dauko masa rayukan mu, lallai'yan uwa kada mu kuskura mu dika jinkirta sallah domin  lallai ita sallah barinta yakan fitar da mutum daga musulunci_ . _Babban Sahābin Annabi  saw Sa'ad Ibn Abī-Waqqas Allah ya kara masa yarda yace: Na tambayi Annabi saw dangane da fadar Allah ta'ala wadanda suke masu shagala ne daga sallolin su, sai  Annabi saw yace "Sune wadanda suke jinkirta yinta akan lokacin ta"  wato suna jinkirta yin sallah akan lokaci saboda shagala da kuma raina ta, kuma suna kin yinta akan lokaci to  hakika alkawarin Allah a tattare dasu itace wani kwari wato wani rami ne wanda ake tsananta azaba acikin sa, wato kwari ne da Allah ta'ala ya  tanade shi acikin wutar jahannama wanda rami ne mai tsayin gaske kuma ga tsananin zafi acikin sa kuma hakika wannan kwari an tanadeshi ne ga wadanda suke jinkirta sallah basuyin ta akan lokacin ta, sai dai wadanda suka tuva zuwa ga Allah madaukakin sarki kuma sukayi nadama akan abinda suka aikata, to wadannan sune masu  rabauta in shaa Allah ta'ala_ . _"Yan uwa wallahi idan mukace zamu bayyana dukkanin abinda yazo dangane da hukuncin masu jinkirta sallah to tabbas acikin rubutun nan ko kwata bamu bayyana ba, to amma su waye masu jinkirta sallah?  Billahi suna da yawan gaske! . *

(1) MATA a gidajen su suna wasa da sallah yanda suka ga dama, kuma suna wulakanta ta matan aure da 'yan mata wallahi da ace zakaga yanda mata suke wulakan ta sallah abin sai ka zubar da hawaye kayi kuka saboda irin bala'in da suke sanya kansu aciki,* . _lallai 'yar uwa ga kisani kulawa da sallah wajibi ne a gareki ki sani Allah ta'ala yace "Mu bamu kasance muna yiwa kowwa azaba ba har sai mun aika masa da dan sako" Nahli don haka wallahi sakon Allah yazo maki ta hanyar wayar salulan ki da take a hannun ki kuma idan sakon Allah ta'ala yazo gareki wajibi ki kar6e shi koda ace kuwa yazo maki ne ta hanyar school on air, Wajibi ki umarci 'ya'yan ki da cewa suyi sallah akan lokaci haramun ne kuma babban bala'i ne jinkirta sallah idan kuwa kika juya baya nasiha bata wadatar dake ba to hakīka wutar gayyah tana nan tana jira, Allah ta'ala ya tsare mu kuma ki sani wajibi ne ki umarci mijinki crwa yayi sallah kuma aksn lokaci domin kuwa kakaf dinku ababen tambaya ne akan ahlin  ku Allah yashiryar damu_ . *

(2) DIREBAN MOTO yana wulakanta sallah yanda yaga dama sai kadan daga wadanda Allah ta'ala ya shiryar* . _Lallai dan uwa kasani kada ka yarda neman duniya yasanya ka ka kauce daga kan karaga na mun tsira kafada kangin wahala lallai wajibi ne direbobi kuji tsoron domib kada wancan ayoyin da hadisai suyi aiki akan ku, Allah ta'ala ya tsare mu_ . *

(3) SAMARI wallahi abin dai saidai muce Lā Haula Walā  Quwwata Illā Billāh wato 'yan uwa yanda samari muke yin wasa da sallah kai kace hujha ce ta lasisi da muka samu daga littafin Allah ko sunnar Annabi Muhammad data tabbatar mana da cewa lallai samari idan sunyi wasa da sallah basu da laifin komai!  Lallai wannan musība tayi mūni!* . _Wajibi samari muji tsoron Allah muyi tanadi tun kafin lokacin mu yayi wanda kuwa ya mutu baya sallah kafiri ne, baza'ayi masa sallah ba kuma baza'ayi masa wanka ba kuma baza'a bitne shi a makabartan musulmi ba arne ne!!!,  akwai dalilai masu yawa akan haka,  'yan siyasa kuji tsoron Allah ku nisanci yin wasa da sallah, kuma sarakuna kuji tsoron Allah ku nisanci yin wasa da sallah,  yāku musulmin duniya kuji tsoron Allah ku daina wasa da Allah, Allah ta'ala yana cewa, "Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada dũkiyõyinku da 'ya'yanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Kuma wanda ya yi haka, to, waɗannan sũ ne mãsu hasãra" Munafiqun,_ . _Wannan Nasīhā ce zuwa ga daukacin Al'immar musulmi daga zauren Sa'adatul-Muslim da fatan anyi shagulgulan sallah lafiya, Allah ta'ala ya kar6a mana kuma ya gafarta mana kurakuran mu anan zamu dakata Allah yasa mudace_  .

*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga* .

→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din

 https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb  . → Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp


Share:

Tuesday, 10 October 2017

Jinin haila:Abubuwanda da suka halatta ga mace a lokacin da take jinin haila!

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA
***************009*******************
ABUBUWAN DA SUKA HALATTA GA MACE A LOKACIN DA TAKE JININ HAILA!
***************************************
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu mai rahama mai jin qai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Swallallahu-Alayhi-Wasallam da ahlin gidansa yardaddun Allah da wadanda suka biyo bayan su da kyautata wa har yazuwa ranar sakamako, 'yan uwa da ikon Allah ta'ala yau ga bayanin mu da mukace zamuyi maku akan wadansu abubuwa da suka halatta ga mace mai jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) ta aikata su da kuma tabbatar da cewa acikin Littãfin Allah babu inda ya hanasu su aikata, haka kuma acikin littafan musulunci (Hadisai) babu inda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya hanasu cewa kada su aikata, kuma da yardan Allah zamu takaita rubutun bazamu tsawaita shi ba, Allah ta'ala yayi mana jagoranci,
.
1:-  YA HALATTA (Mace mai jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) ko kuma mace mai janaba ko namiji mai janaba, matar aure ko budurwa, Mai mata ko gwauro, ta hanyar Jima'ei ko kuma mafarki, kakaf dinsu ya halatta su dauki Al-Qur'ani da hannuwan su kuma su karanta Al-Qur'ani din matukar bukatar hakan ya taso, inaso kusani acikin Littãfin Allah (Al-Qur'ani) ko kuma Hadisi kakaf babu inda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ko kuma Allah ta'ala ya hana mace ko namiji don Suna acikin wannan halin cewa wai kada su dauki Al-Qur'ani, Wallahi ina yi maku rantsuwa da Allah babu wannan wajen, ya halatta kiji na sanar dake da kuma kai wanda kake da janaba ajikin ka ku karkad'e kunnuwan ku kuji ya halatta ku dauki Al-Qur'ani ku karanta matukar bukatar hakan ya taso, domin babu inda akace kada ku dauka, don haka  'yan uwa kusani wannan tilawar Al-Qur'ani din babu hani akan sa, (Asha karatu lafiya 'yan uwa na),
.
Hadisi ya tabbata acikin Sahihu Muslim Daga Ummuna Aysha Allah ya kara mata yarda tace,  "Lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana ambaton Allah a kowwane hali" ( Duba Fiqhul-Muyassir shafi na 56)          ..  Imam Muhammad Nasirud-Deen Al-Albany Rahimahullah yace  "Acikin wannan hadisin akwai halaccin karanta Al-Qur'ani ga mai Janaba, domin kuwa lallai karatun Al-Qur'ani zikiri ne (ambato) kenan zai shiga acikin maganar ta cewa (Yana ambaton Allah) (Duba Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu)      ...    Amma abinda yafi shine mutum ya  karanta Al-Qur'ani acikin tsarki, wato ya karanta shi yana tsarki domin kuwa ya tabbata acikin Hadisi na Sunan Abiy-Dawuda a lõkacin da akayi wa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi sallamah, to a lõkacin bashi da tsarki sai yayi taimama sannan ya amsa, daga nan yace  "Lallai ni an karhanta min ambaton Allah, sai dai idan ina da tsarki"   (Ku nemi wannan hadisin acikin Sahih Sunan Abiy-Dawuda mujalladi na farko shafi na 763, ko kuma a Duba Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu)
.
Sheikh Swalihul-Othaymeen Allah ta'ala yayi masa rahama yace  "Babu wani hani ga mace wacce take jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) su dauki Al-Qur'ani su karanta idan bukatar haka ya taso kamar matar ta kasance malama ce (mai koyar da karatu acikin makaranta ya halatta ta dauki Al-Qur'ani ta karantar dasu) ko kuma Daliba ce (Wacce take zuwa makaranta koyon karatu ya halatta ta dauki Al-Qur'ani taje makaranta a koyar da ita) ko kuma wadanda suke zaune acikin gida (Gashi kuma suna yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) to ya halatta su dauki Al-Qur'ani suyi tilawa idan suka bukaci hakan"   (Wannan fataawa ta Swalihul-Othaymeen Rahimahullah tana acikin littafin fatawoyin sa mai suna  *SU'ALAN-AN-AHKAAMUL-HAIDH* fatawa ta 52 shafi na 16)
.
2:-   YA HALATTA (Mace tabi duk hanyar da zatabi ta biya wa mijin ta bukata alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) amma dai banda saduwa wato banda kwanciyar aure kamar yanda bayani ya gabata acikin rubutun mu daya gabata
.
3:-    YA HALATTA (Mace alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) ko kuma mai Janaba su shiga masallaci domin jin wa'azi ko kuma daukan karatu, kada kudamu da hadisin da yazo acikin Sunan na Abiy-Dawuda hadisi na 232 wai daga Ummuna Aysha Allah ya kara mata yarda tace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace  "Lallai ni ban halatta wa mace mai jinin haila ko kuma mai Janaba shiga masallaci ba"    (Wannan hadisi karya akayi wa Annabi bai tabbata ba)   ya halatta kushiga cikin masallaci Kuyi zaman ku in shaa Allah Imam Muhammad Nasirud-Deen Al-Albany Rahimahullah yace  "Babu wani ingantaccen hadisi kai tsaye da yazo yake nuni da cewa an hana mace mai jinin haila ta shiga masallaci"   (Duba Fataawa-Muhimmah Lin-Nisaa'il-Ummah 55, ko Fiqhul-Muyassir na Sa'ad Yusuf shafi na 57)    don haka dai  'yan uwa na babu wanda ya hanaku, Allah ta'ala yasa kun fahimce ni, Allah yasa Mudace
.
Alhamdulillah anan zan dakata in shaa Allah, sai ajira mu a fai-fai na 010 kuma in shaa Allah shine zai zama rubutu na karshe akan wannan matsalar ta jinin haila, wanda kuma taken wannan rubutun shine FAA'IDOJIN MU ACIKIN WANNAN LECTURE, Allah ta'ala yayi mana jagoranci, Allah yasa Mudace, Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh
.
Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah Abu-Nabeelah Kuriga
.
                **24/Shawwal/1438**
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp


Share:

Saturday, 30 September 2017

Illolin gulma 06

```★★★ILLOLIN GULMA★★★```
~~~~~~~~~~6~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Cigaba_
.
_Akwai wani hadisi da Annabi saw yake bayar da labari akan abinda zai faru a ranar Alqiyāmah, yake cewe  "Mutum ne za'azo dashi ranar tashin Al'qiyamah gashi yayi sallah cikakka kuma yayi azumi cikakke kuma ya bayar da dukiyar sa a hanyar Allah, wata kīla ma yaje aikin hajji, gashi a filin qiyamah ayyuka na kwarai Alhamdulillah, to amma dai matsalar sa itace ya zagi wannan sai a dibi ladarsa a baiwa wanda ya zaga, haka kuma kuma yayi ma wani Qazafi shima nan sai a dībi ladarsa a baiwa wanda yayi ma Qazafin, haka kuma yaci dukiyar wani shima nan a debi ladan sa a baiwa wanda yaci dukiyar sa, haka kuma yayi gulmar wani shima anan a debi ladarsa a baiwa wanda yayi gulmar, haka kuma ya zubar da jinin wani shima nan sai a debi ladarsa a baiwa wanda ya zubar da jinin sa, haka kuma ya bugi wani shima a debi ladansa a baiwa wadanda ya zalunta, a haka malā'iku zasuyi ta dībar ladansa ana rarrabarwa amma bai isa ya hana ba, sai a samu gashi da yana da lada amma fa sun kare saboda zaluncin daya aikata yau gashi ya koma ziro, Annabi yace wannan mutumi shine fallasashshe wanda asirinsa ya gama tonuwa kai karshen Al'amari dai makomar sa itace wutar jahannama!" Allah ya tsare mu_
.
_'Yar uwa kamar yadda muka fada a baya cewa Allah ta'āla ya haramta gulma, to ga wani hadisi mai tsoratarwa wanda Abū-Hurairah ya jiyoshi daga Annabi saw, Lallai Annabi saw yace  "Lallai mutum zaiyi tayin magana da wata kalma wacce Allah ya yarda da ita, ba tare da yasani ba ko yanaga ba komai bane to kuma saboda wanban kalmar da yake furtawa sai Allah ya ta'ala ya daukaka darajarsa da ita wannan kalmar,  sannan kuma yace lallai wani bawan Allah, wato wani mutum zaiyi tayin wata magana da wata kalma wacce take acikin abinda Allah ya hana wato Allah bayason kalmar kuma shi da yake amfani da wannan kalmar a tunanin sa ba komai bane amma a haka ita wannan kalmar sai ta zama sanadin sa na shiga wutar jahannama!"  Wannan hadisi ne ingantacce yana cikin Sahīhul Bukhāri hadīsí  na 6478 sannan yana cikin Musnad da Imām Ahmad mujalladi na 2 shafi na 334,  wallahi 'yan uwa daga cikin kalmomin da Allah bayaso Gulma tana cikinsu,_
.
_Lallai dan uwa na da kuma ke 'yar uwa ta ku karkade kunnuwan ku kuji abinda zan sanar daku, wannan abin da zan fada yanzu shi yakamata mutane su dika fadawa 'yan uwansu idan sunzo masu da labari sannan zamu doshi kadan daga magabata muji abinda suka nuna mana dangane da illar harshe da kuma musībar gulma, ku kasance kuna fada ma 'yan uwanku cewa  *Dukkan mu ko ni kaina ko kai ko ke dukkan mu kakaf dinmu duk wanda yasan idan zaiyi magana acikin mu amma kuma yasan ba alkhairi bace to kawai yayi shirū mu abinda mukafi so kenan domun tanan ne zamu samu kāriya daga musība da take tattare da Gulma*     An samu inganracciyar riwaya daga Ibn Umar yana cewa  "Kashedin ku da yawan magana,"  haka kuma Imāmun-Nakha'ī yana cewa  "Mafi yawan mutane sun hallaka saboda yawan dukiya da kuma yawan magana"_
.
_Har wayau an samu asar daga Imamu Annakha'i yake cewa  "Lallai yawaita magana  a wajen da babu wata bukatar hakan, yana sanya kekashewar zuciya,"  ida kika fito gidan wance ina zaki gidan wance!  Wallahi idan ka bībiya babu abinda takeyi sai gulma, kawai ita ta zama uwar Gulma a gari bata anan bata acan ke kuwa!?    An samu wata riwaya daga salman Allah ya kara masa yarda wani mutum yace ma Salmān kayi min wasiyya yakai Salmān, a lokacin da Salmān ya tashi bashi amsa sai yace masa "Kada ka kuskura ka dika yin magana!  Sai wannan mutum yace to ni kuwa ya zanyi da jama'a dangane da bukatu na yau da kullum idan naqi nayi magana, yana fadar haka sai Salmān yace masa to kuwa kasani idan dai har zakayi magana to kayi magana da gaskiya, banda Gulma ko Annamīman ci ko karya aa kayi magana da gaskiya ko kuma kayi shiru inji Salmān Allah yayi masu rahamah_
.
 _Zamu dakata anan sai mun hadu a darasi na gaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp ‬


Share:

Illolin gulma 05

```★★★ILLOLIN GULMA★★★```
~~~~~~~~~~5~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Muna bayani akan Illolin Gulma Zamu cigaba in Allah ya yarda_
.
_Lallai dan uwa wajibi ne ka dika kiyaye harshen ka wajen fadin alkhairi Imamu Dabarānī ya ruwaito hadisi daga Aswad dan Asram Al-mahāribī yace ni kuwa sai nace ya manzon Allah kayi min wasiyyah, sai Annabi saw yace  "Shin ka kiyaye harshen ka?" Ni kuma sai na bashi amsa cewa " Ni kuwa mai zan kiyaye idan har ban kiyaye harshe na ba ya Annabin Allah? Sai Annabi yace  "Shin ka kiyaye hannuwan ka?  Ni kuwa sai na amsa da cewa "Me zan kiyaye idan ban kiyaye hannuwa na ba? Sai Annabi yace  "Kada ka kuskura kafadi wata magana da harshen ka sai dai abu mai kyau na alkhari kuma kada ka kuskura ka shimfida hannuwan ka sai dai zuwa ga aikin Alkhairi"  wannan hadisi ne Hasan Haisamī ya kawo shi acikin Maj'moo' mujalladi na 10 shafi na 303 hadisi ne ingantacce,  'yan uwa kunga wannan hadisin kai tsaye ya nuna mana haramcin gulma!_
.
_Kai wallahi ina sanar daku illar gulma,  cewa imanin dayanku baya inganta har sai mutum ya kiyaye harshen sa, 'yan uwa kada kuga kamar maganar tayi girma,  akwai hadīsī acikin Musnad na Imam Ahmad duk da wasu malaman Hadīsai sun raunata Hadīsin, hadisi ne na Anas Allah ya kara masa yarda yace Annabi Saw yace "Imanin bawa baya dai-dai tuwa har sai ya dai-daita zúciyar sa, to amma fa kusani zúciyar bawa bata dai-dai tuwa dole sai ya kiyaye harshen sa"  akwai wani hadisi wanda ya inganta  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kira magulmata da cewa  "Yaku wadanda sukayi Imani da Harshen su alhali zuciyar su batayi Imani ba? Sai Annabi yace sune wadanda suke yin Gulmar 'yan uwa, kuma suke wulakanta su_
.
_'Yar uwa kinji fa wadanda sukayi Imani da harshen su amma Zuciyoyin su basuyi imani ba sune magulmata!  To mu yanzu yaya muka dauki gulma, kamar yanda na fada maku cewa wallahi hatta wadanda suka siffantu da Ilimi acikin mālamai akan samu magulmata acikin su, 'yan uwa sai daifa mu nemi tsarin Allah, wallahi gulma tana da hatsari, kai wallahi bari kuji aljannah dakan ta ta'allaqa ne ga masu kiyaye harshe akwai Hadīsai acikin Bukhari da Muslim  Annabi saw yace  "Na lamince Aljannah ga duk wanda ya kiyaye harshen sa da kuma abinda yake a tsakanin cinyoyin sa (wato Al'aura)"   kunji kenan idan muka dauki wannan hadisin zamu fahimci cewa ashe ita kanta Aljannah mutum bazai sameta ba har sai ya kiyaye harshen sa,_
.
_' Yan uwa ga wani hadisi mai tsoratarwa da yazo acikin Sahīhul Bukhari Hadīsi na 6477 da kuma Muslim Hadīsī na 2988  hadisin Abu-Hurairah Allah ya kara masa yarda yace Manzon Allah saw yace  "Lallai mutum zaiyi tayin wata magana da wata kalma wacce baisan hatsarin dake cikin ta ba, bazai gushe ba sai wannan kalmar tayi sanadin shi na shiga wutar jahannama yana mai dawwama acikin ta wacce tsawon inda za'a saka shi yakai nīsan da yake tsakanin gabas da yamma"  wannan hadisin yana cikin littafin Jāmi'ul-Ulūm Wal-Hikam shafi na 217 karkashin sharhin hadīsī na 15,  to 'yar uwata yaya matsayin gulmar abokiyar zaman mu da muke yi bayan mun sani Allah ya haramta gulma!?_
.
_Sannan Akwai wani Hadīsi da Imam Tirmidī ya ruwaito acikin Sunan a babin Zuhdu hadisi na 2314 Annabi saw yace  "Lallai mutum zaiyi tayin magana da wata kalma shi a wajenshi wannan maganar da yake yi babu wani abu na laifi, a haka yake daukar kalmar ta sanadin wannan kalmar sai a jefashi acikin wuta wacce nīsan ta yakai tsawon shekara saba'in 70"  hadisi ne ingantacce daga Abu-Hurairah,   don haka nefa Annabi yace koda ace laifin dan uwanka ne ka ambata to kayi gulma,!_
.
 _Zamu dakata anan sai mun hadu a darasi na gaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp ‬


Share:

Illolin gulma 04

```★★★ILLOLIN GULMA★★★```
~~~~~~~~~~4~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Muna bayani akan gulma kuma mun fadi yanda Annabi saw ya fassara mana cikakkiyar kalmar gulma_
.
_Kunga kenan mu sai dai muce Allah ta'ala ya tsare mu, domin kuwa yanda muke yin mu'amala da gulma ya subhanallah,  'yar uwa ta dan uwa na Annabi ne fa ya fassara mana ma'anar kalmar gulma cewa, magana ce wacce zaka fada akan dan uwanka gashi kuma aikin sa ne fa kafada amma idan yana wajen ransa bazaiji dadi ba, to ida kuwa haka ne su waye yanzu basuyin gulma yaku ja'ama?  Mutum ne zaka sameshi gashi da siffa ta mutanen kirki amma kuma sai kasameshi da siffa ta magulmata,  kamar yanda mata suke mu'amalar 'yan uwansu a wannan bangaren har idan aka samu wata tana kokarin yi masu nasiha sai suce ai akinta ne da batayi ba da baza'a fada ba, 'yar uwa wallahi wannan Gulma ne Allah ya hana, domin kuwa Allah cewa yayi  "Kada sashin ku yayi gulmar sashi" don haka kalar wannan gulmar haramun ne inji Annabi Muhammad saw,_
.
_Lallai idan muka dauki wannan fassara ta Annabi saw akan gulma to ashe kunga kenan wajibi ne mu tsaya mu kiyaye harshen mu domin kuwa kada balā'i ya sauka akan mu, muna neman tsarin Allah_
.
_Al-Imam Al-Hasanul-Basary babban tabi'ī daga cikin tabi'ai Allah yayi masa rahama yana cewa  "Yin magana akan wannan matsal kala uku ce, wanda kuma kakaf dinsu harāmun ne abu na farko shine ita kanta Gība din wato Gulma!  Na biyu kuma Kazafi abu na uku itace Karya,"  wato labari ne yazo ya sameka cewa wanefa yana aikata kaza, kai kuma sai kadauki wannan labarin kana yadawa, to wallahi wadannan kakaf dinsu harāmun,  'yan uwa ayi hakuri zamu ambaci dalīlai kadan da suke tabbatar mana da haramcin wadannan abubuwa in shaa Allahu,_
.
 _Abu na farko da zamu fara ambata shine wani hadisi swahīhī wanda kowwannen mu yasan wannan hadisin wanda Imam Bukhari ya ruwaito hadisin mai lamba 6018 a babin Ladubba, shi kuma Imam Muslim a Babin Imāni hadisi na 47  shi kuma Imam Tirmidhī acikin Sunan Babin da yake magana akan Qiyāma hadisi na 2500 hadīsin Abdirrahman Ibn Sakhr wato Abu-Hurairah Allah ya kara masa yarda, yace lallai Annabi saw yace  "Duk wanda yayi Imāni da Allah da rana ta karshe  to ya fadi Alkhairi ko yayi shiru"   kunga kenan a karkashin wannan hadisin zamu fahimci cewa magulmata Imānin su da Allah ta'ala akwai saura ba cikakken Imani suke dashi baga Allah domin Annabi ne ya fada,  'yan uwa gulma fa tana da hadari, kawai dai mu nemi tsarin Allah Madaukaki,_
.
_Zamu dakata anan sai mun hadu a darasi na gaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp ‬

Share:

Illolin gulma 03

```★★★ILLOLIN GULMA★★★```
~~~~~~~~~~3~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Muna magana akan gulma da kuma Illolin ta wanda yanzu Zamu cigaba in Allah ya yarda_
.
_Jama'a kada mu manta fa musulmi Allah ta'ala ya daukaka darajarsa, ta 6angaren jininsa haramun ne wani musulmi ya zubar masa haka kuma dukiyar musulmi haramun ne wani dan uwa musulmi yaci, haka kuma mutuncin musulmi harāmun ne wani dan uwa ya zubar masa, kai komai ma na musulmai haramunne akan kowwane musulmi, to amma bari muji maganar Allah ta'ala akan gulma kuma muji yaya Annabi saw ya fassara mana ma'anar kalmar gulma, Allah ka tsare mu_
.
_Allah madaukakin sarki yana cewa acikin suratul Hujurāt aya ta 12,_
.
*يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِّنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ۖ وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَب بَّعْضُكُم بَعْضًا ۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَن يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَّحِيمٌ*
.
_'Yan uwa wallahi Gulma tana cikin Kabā'ir saboda Allah cewa yayi   "Yãkũ waɗanda sukayi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lallai sãshen zato laifi ne, Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yãyi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kunkĩshi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taqawa, Lallai Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jinkai"     'yan uwa kunga Allah cewa yayi  "Kada sashen ku yayi Gulmar sashe"  kenan umarni ne akeyi mana anan, to amma kada na tari numfashin ku bari muji yanda Annabi Saw ya fassara mana cikakkiyar ma'anar kalmar Gulma!_
.
_Hadisi ya tabbata acikin sahīhu Muslim hadisi na 2589 Annabi saw ya tambayi sahabban sa Allah ya kara masu yarda  cewa  "Shin ko kunsan me ake nufi da Gulma kuwa? Sahabbai suka bayar da amsa cewa Allah da Manzon sa ne kadai suka sani, sai Annabi saw yace masu  "Ka ambaci dan uwanka da abinda idan yana nan ka ambata ranshi bazaiji dadi ba, Annabi yace wannan shine abinda akece ma Gulma, wato magana ce wacce idan 'yar uwanki tana wajen sai kika fadi wannan magana akanta to ranta bazataji dadi ba,  sai wani daga cikin sahabbai yace, "To kuma idan abinda nafada akansa gaskiya ne fa?  Sai Annabi saw ya bashi amsa da cewa idan abinda ka fada akan dan uwanka gaskiya ne! To hakīka kayi gulmarsa, idan kuma abinda kafada akan sa ba haka bane to kayi masa kage inji Annabi Muhammad saw,"   dan uwa kadaiji fa Annabine ya fassara cikakkiyar ma'anar Gulma, to mu ya muke a yau?_
.
_Zamu dakata anan sai mun hadu a darasi na gaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp ‬
Share:

Illolin gulma 02

```★★★ILLOLIN GULMA★★★```
~~~~~~~~~~2~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Wannan shine bayani na biyu kuma muna magana akan Gulma_
.
_Gulma fa jama'a ina kara jaddada mana cewa wallahi gulma yanda ta yawaita acikin wannan Al'ummar babu maza ballan tana mata, kai babu manya ballan tana kanana, abin yakai ya kawo hatta acikin masallatayyar mu an mayar dasu wajaje na gulma, abin dai ya zama kamar wani Ibadah duk inda zakaji ance ga wani majalisi, to wallahi zaka samu ba majalisi bane wajen gulma ne, matsalar ba anan kadai ba hatta acikin makarantu na Islamiyya an mayar dasu sun zamo wajajen gulma, kai 'yan uwa abin fa kamar gāsa akeyi hatta a social media Facebook whats app da sauran wajajen fira akan samu zaure wanda kawai aikin su shine  gulma! mun samu wani lokaci da wuya kasamu mutum biyu zuwa uku sun zauna suna fira har su tashi basuyi gulman dan uwa musulmi ba, 'yan uwa abinfa yayi kāmāri da yawa sai dai mu nemi tsarin Allah daga wannan musifa ta Gulma_
.
_Cin naman 'yar uwarki shine ki ambaci wani al'amari nata wanda idan dai har tana nan kika ambaci wannan kalmar zataji haushi, wannan shine ma'anar gulma wato ma'nar gulma itace kaine zaka fadi wata magana akan dan uwanka idan har yana wajen kayi wannan maganar tofa zaiji haushi, wato idan kayi magana a bayan idon dan uwan ka wato bazai lamunce ba bazai yarda ba, gashi halin nata ne kika ambata amma dai idan har tana wajen ranta bazaiji dadi ba wannan fa shine ma'ana gulma,  'yan uwa saboda Illar Gulma Allah madaukaki bai barwa Annabi Saw ragamar haramta Gulma ba, shima da kansa sai da ya haramta mana yin gulma, Lā haula walā Quwwata Illā Billāh  'yan uwa mune fa muke karanta Alqur'ani mu mune Al'ummar Annabi Muhammad saw kuma ayar da Allah ya haramta gulmar 'yan uwa dani dake da ku masu karatu wallahi muna karanta wannan ayar, amma gaba daya bamuyin aiki da ita,_
.
_Gashi kuma sanin kanmu ne cewa dukkan inda muka samu umarni acikin alqur'ani to yin aiki da wannan umarnin wajibi ne, haka kuma dukkan inda muka samu wani hani acikin Alqurani tofah wannan hanin dole ne mu hanu matukar muna son mu samu rabo a ranar qiyamah, zamu dauki aya guda daya acikin Alqur'ani da Allah ya haramta gulma, daga nan sai mu dauki wasu takaitattun hadīsai da sukayi magana akan gulma,! Allah ta'ala ya shiryar damu,_
.
 _Zamu dakata anan sai mun hadu a darasi na gaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp ‬


Share:

Illolin gulma

```★★★ILLOLIN GULMA★★★```
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
*‫بسم الله الرحمن الرحيم‬ ‫الحمد الله رب العالمين و لا عدوان إلا على الظالمين و الصلاة و السلام على سيدنا محمد سيد المرسلين و إمام المتقين‬ ‫و على آله و صحبه أجمعين أما بعد يا إخوان ا Iلكرام السلام عليكم ورحمة الله وبركاته*
.
_'Yan uwa wannan wata lecture ce da zauren Sa'adatul-Muslim ta shirya maku domin tunatar da 'yan uwa maza da mata akan illoli da kuma musiibar da take tattare da gulma, wato cin naman 'yan uwa wanda muna fatan Allah ta'ala ya taimake mu, kuma ya bamu ikon fadar maku tsanysar gaskiya_
.
_'Yan uwa inaso ku sani lallai fa Gulma tana daya daga cikin manya-manyan zunubai wadanda suka zama ruwan dare game duniya,  wallahi acikin wannan Al'ummar mun dauki wadansu miyagul laifuka wadanda aikatasu musiba ne a garemu wanda har muke ganin ba komai bane a wannan zamanin namu, to lallai fa 'yan uwa kusani Gulma tana daya daga cikin laifuka wadanda muke aikatasu a yau, wadanda basuyin gulma acikin wannan Al'ummar nan 'yan kadan ne, muna neman tsarin Allah daga fadawa cikin masu irin wannan hali,_
.
_Jama'a wallahi tallahi yanda gulma ta yawaita acikin wannan Al'ummar kai yanda mutane suke mu'amala da Gulma a wannan zamanin namu wallahi kai kace hujja ce muka samu daga ayar Alqur'āni ko kuma hadisin Annabi saw, alhali kuwa Allah ta'ala ya haramta gulma acikin littafin sa,_
.
_Zamu dakata anan sai mun hadu a darasi na gaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp ‬


Share:

Thursday, 28 September 2017

Shin wajibi ne azumin Ashura!?? Saadatul muslim

```SHIN WAJIBI NE AZUMIN ĀSHURA? !```
...........................................
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Lallai azumtar ranar Ashura ba wajibi bane 'yan uwana sai dai wannan azumi ne wanda Annabi saw ya azumce shi kuma ya kwadaitar cewa a azumci wannan rana wato goma ga watan Al-muharram wanda yayi dai dai da ranar asabar mai zuwa in Shaa Allah, Annabi saw ya kwadaitar da ayi azumi a wannan rana ta Ashura wanda 'yan sha-biyu suke barnatar da jinainan su wajen saba ma Allah da kuma wahalar da kai, Imam Malik acikin Muwadda shafi na 163 karkashin Littafin Azumi hadisi na 824 yace Lallai labari yazo masa cewa lallai babban sahabin Annabi Umar dan Khaddab ya aika wajen Harith dan Hisham cewa lallai fa gobe itace ranar Ashura, don haka kayi azumi kuma ka umarci iyalanka cewa suyi azumi" 4 don haka wannan Sunnah ce amma fa mai karfi zamu ambaci hadisai guda biyu Akan haka in Allah ya yarda_
.
_Azumin a ranar Ashura Sunnah ce mai karfi Imam Bukhari ya ruwaito ingantaccen hadisi daga Ummuna Aisha Allah ya kara mata yarda tace, ranar Ashura ta kasance rana ce da Quraishawa suka kasance Suna azumtar wannan rana tun lokacin jahiliyyah, shi kuma Manzon Allah saw ya kasance yana azumtar wannan rana tun a jahiliyyah, lokacin da Annabi saw yazo garin Madinah sai yaci gaba da azumtar wannan rana kuma yayi umarni da cewa a azumce ta amma a lokacin da aka wajabta Ramadan sai ya kasance Ramadan shine Azumin da aka wajabta sai akabar azumtar Ashura ya zama Sunnah, duk wanda yaso ya azumci wannan rana ta Ashura wanda kuma yaso ya barta" (Bukhari 2002 Muslim 1125)_
.
_Hadisi ya inganta daga Abdirrahman dan Auwf Allah ya kara masa yarda yace lallai shi yaji Mu'awiyah bin Abi-sufyan a ranar Ashura a shekarar aikin hajji a lokacin shi yana Akan mimbari yana cewa "Yaku 'yan garin Madinah Ina malaman ku suke? naji Manzon Allah saw yana magana dangane da ranar Ashura cewa the" Wannan itace ranar Ashura kuma Allah bai wajabta maku Azumtar sa ba amma fa kusani ni Ina Azumi ga duk wanda yaso daga cikin ku to yayi Azumi, wanda kuma yaso daga cikin ku to yasha abin shansa, ma'ana yaci gaba da cin abincin sa" (Bukhari 2003 Muslim 1169)_
.
_Don haka dai 'yan uwa Sunnah ce kuma ku tunatar da' yan uwanku dangane da wannan Azumi na ranar goma ga watan Al-muharram domin su azumce shi kuma ayi don Allah domin neman yardan sa, Allah yasa mudace_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp


Share:

Ashura da tasu'a - Sa'adatul-muslim

```ASHURA DA TASU'A```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, ranar Ashura itace ranar 10 ga watan Al-Muharram wato watan farko na sabuwar shekarar Musulunci wanda ya inganta daga Annabi Saw cewa ya azumci wannan ranar kamar yadda bayanin ya gabata, to ita kuma Tasu'a fa?   Ranar Tasu'a itace ranar 9 ga watan Al-Muharram wacce Annabi yayi nufin azumtar wannan ranar Amma Allah madaukaki bai kai Annabi Saw wannan lokaci ba, dalili kuwa hadisin Ibn Abbas wanda yake cewa "A lokacin da Annabi Saw yayi azumin Ashura kuma yayi umarni da cewa a azumci wannan ranar, sai mukace ya Manzon Allah lallai wannan rana ce wacce yahudawa da Nasara suke girmama ta, sai Annabi Saw yace, idan har shekara ta zagayo da yardan Allah zan azumci ranar 9 ga wata, (wato 9 ga watan Al-Muharram sannan ya azumci 10 ga watan)  Ibn Abbas yace Allah madaukaki bai kaddari Annabi Saw yakai shekarar ba, sai mutuwa tazo ma Annabi Saw"  Muslim da Abu-Dawuda ne suka ruwaito wannan hadisin, duba littafin Fiqhul-Muyassir na Sa'ad Yusuf shafi na 177,_
.
_'Yan uwa kunji inda azumtar 9 ga wannan wata na Al-Muharram ya samo asali wato ka azumci 9 da 10 ga wannan watan shi akafi so, amma ga wanda bashi da karfin yin azumi guda biyu a jere shi ko ita guda daya 1 rak kawai zata iya yi to tayi kokari tayi na 10 ga watan kada tace zatayi 9 tabar na 10 aa kawai mutum matukar shi guda 1 kawai zaiyi to yayi 10 ga watan wato Ashura shi yafi, sabanin 'yan sha-biyu da suke wasa da makami suna illata jikin su wannan ba koyarwar Musulunci bane da kuma Nawasib masu yin cika-ciki shima wannan babu shi a Musulunci abinda ya inganta shine yin wannan azumi guda biyu wato 9 da 10 ga wannan watan na Al-Muharram, wanda kuma a yanzu da nake wannan rubutun da safe yau Laraba wato Wednesday 7 ga watan Al-Muharram shekara ta 1439 wanda azumin Tasu'a zai kama ranar Juma'a shi kuma Ashura ranar Asabar, Allah ya bamu ikon yin Azumin don Allah, Allah yasa mudace_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp


Share:

Tuesday, 19 September 2017

Kashe tsaka-tsaka abune mai kyau ga dalilai daga cikin hadisai.

```KASHE TSAKA ABUNE MAI KYAU```
………………………………………………
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
الحمد لله رب العالمين والصلاة السلام على رسول الله صلى الله عليه وسلم وبعد
.
_'Yan uwa addinin musulunci Addini ne mai tsafta da son zama lafiya, don haka ne ya shar'anta mana wasu ababe da suka halatta mutum ya kashe su daga ciki ma akwai wanda idan ka kashe kana samun lada, daga cikin wadannan halittu akwai tsaka! Wacce Annabi saw ya kira ta da cewa lallaifa ita tsaka algun-guma ce  wacce kuma Annabi saw ya tabbatar mana da cewa lallaifa dukkan wanda ya kashe tsaka a duka guda daya rak! To yana da lada dari (100)_
.
_Saboda illolin ta tun kafin wannan lokacin tsaka tana da illah, daga cikin illolin ta ita tsaka bakin ta kamar abin walda ne idan ta samu dan adam yana barci har ta samu dāma ta huta idanun sa a wannan sanadin yakan sanya mutum ya makance! Illolin ta yana da yawa wanda ba sai mun ambata suba anan, to amma dame ake kashe tsaka? Amsa itace ana kashe tsaka ne da dukkanin abinda ya samu na duka ba wai dole sai tsin-tsiya ba aa koda ace da takalmi ne ko wani abu na duka wanda za'ayi mata duka daya ta mutu shi akeso, idan ma kasamu dama ya halasta maka idan kaganta akan hanya kayi tsalle ka hau kanta ta mutu dukkan hakan ya halatta babu hani akai_
.
_Daga cikin laddubar kashe tsaka itace anaso a lokacin da kaga tsala sai kayi kwadayin kasheta to kayi basmala wato kace Bismillahi sai ka kai mata duka idan Allah ya kaddara ajalinta yayi shi kenan sai ka ambaci Allah ka kasheta, ko meye dalilin yin Bismillah a lokacin da mutum namiji ko mace yayi nufin kashe tsaka?  Dalili kuwa shine saboda Al'janu suna zama tsaka, kuma sukan zama kunamu (scorpions) sukan zama macizai (snake's) saboda haka ne Annabi yace mutum ya ambaci Allah a lokacin da mutum ya nufaci kashe tsaka!_
.
_Wanda wata cuta ta sameshi akan yawan kashe tsaka da yakeyi, ko yayita surutai akan ita tsakar kamar ya dika cewa tana zuwa masa idan yana barci har yakan gaza kwana a daki shin meye mafita!?  To bayanan da zamu iyayi anan shine zamuce tun farko a bangaren kashe wannan tsakar ba'abiyo ta wancan ladabin ba da muka ambata na kashe irin wadannan halittu wato yin Basmala a yayin kashe ta, kuma hakan zai iya faruwa saboda kwadayin lada da dan adam yake yi a wajen Allah sai yayi nufin kashe tsaka ashe bai sani ba aljani ne kuma sai Allah ya kubutar da Aljanin wato shi wannan mutumin baisamu damar kashe wannan tsakar ba, to shi kuma aljani da yaga ya kubuta shi kenan sai ya dika zuwa yana razana wannan bawan Allah din da daddare, ina mafita?_
.
_Mafita ga wannan matsalar itace wannan bawan Allah din ya yawaita karanta Alqur'ani mai girma da kuma yawaita addu'o'i na sunnah domin neman tsarin Allah daga wannan sharri na aljani, kamar yawaita karanta suratul-Baqarah acikin gidan da kuma kiyaye addu'o'i musamman addu'ar kwanciya barci da sauran su, kamar yin al'walah a lokacin da mutum zai kwanta barci, ta wannan hanyar in Allah ya yarda za'a samu waraka da lafiya, muna rokon Allah madaukaki mai yin hukunci da kuma buwayarsa da hikimarsa yabaiwa masara lafiya, lafiya kuma ya karemu daga sharrin shaidanu maza da mata, Allah ne mafi sani, mahaifiya ta tana fama da rashin lafiya don Allah ku sanya ta acikin addu'o'in ku Allah yasa mudace,_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp
Share:

Me ake nufi da annamimanci !!??

```ME AKE NUFI DA ANNAMĪMANCI!?```
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
الحمد لله رب العالمين والصلاة والسلام على رسول الله صلى الله عليه وسلم، وبعد السلام عليكم ورحمة الله وبركاتة،
.
_Ma'anar Annamīmanci kamar yanda Imamuz-Zahabi ya fassara mana acikin Kabā'ir shine  "Jefa magana acikin mutane (wato ka fadi magana a tsakanin mutane) wacce zata haddasa 6arna a tsakanin su, wato magana ce wacce mutum zaiyi ta a tsakanin wadansu mutane guda biyu wacce zata haddasa rikici a tsakanin su, wannan shine ma'anar Annamīmanci"_
.
_Hukuncin yin Annamīmanci kan malamai ya hadu cewa harāmun ne, wato kakaf musulman duniya sun yarda cewa Annamîmanci haramun ne, akwai dalilai masu yawa da shari'a ta kallesu ta haramta shi daga littafan musulunci Qur'āni da Hadīsi da kuma Ij'mā'ī na malamai,_
.
_Allah madaukakin sarki yace acikin suratul Qalam, cewa "Kada kabi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce"  kuma yace  "Mai zunɗe, mai yãwo da gulma"  kunga wadannan ayoyin sun tabbatar mana da cewa mai Annamīmanci da Gulma dukkan su wulakantattu ne, 'yan uwa sanya gaba tsakanin musulmi yana da had'ari ba karami ba kuma masu irin wadannan ayyuka basu shiga Al'jannah,_
.
_Hadīsi ya tabbata acikin Bukhari da Muslim cewa lallai Annabi Swalallahu Alaihi Wasallam yace "Mai Annamimanci bazai shiga Al'jannah ba"  a wani hadisin kuma Annabi Saw ya wuce ta wajen wasu kaburbura guda biyu, sak yace  "Lallai su anayi masu Azabah kuma ba wai anayi masu azaba bane saboda wasu manya-manyan zunubbai da suka aikata bane, aa kawai dai daya daga cikin su ya kasance baya tsarkaka ne daga fitsari, amma kuma dayan ya kasance yana uawo ne da Annamīmanci, sannan sai Annabi saw ya tsinki wani danyen ganye ya rabasu biyu sai ya rabasu akan wadannan kaburbura, wato ya dorasu akan wadannan kaburburan, sannan yace ina fatan a saukaka masu azaba, har zuwa lokacin da wannan ganyen zai bushe" kunga wannan cewa da Annabi saw yayi cewa ba manyan zunubai bane, to ai abinda yasa ya fadi haka shine ganin yanda mutane suka daukeshi ba komai ba, amma akwai riwayar data rabbatar da cewa yace lallai fa wannan babban zunubi ne,_
.
_An samu ruwaya daga Abī-Hurairah Allah ya kara masa yarda yace, Annabi Saw yace  "Mafi sharrin mutane zaizo da fuska biyu, wanda zaizo ga wadancan da wannan fuskar sannan kuma yaje ma wadancan da wata fuskar da kuma abinda ya kasance yana fitowa daga barshen sa (wato gulma ko Annamīmanci) acikin wannan duniyar, to kusani wallahi ranar Qiyāmah Allah zai sanya harshen sa acikin wuta!"     Abinda ake nufi da cewa mai fuska biyu shine wanda zaizo wajen wani daga cikin mutane yayi masu wata magana wacce batada alaqa da zamantakewar al'ummah sai dai magana ta Annamīmanci ko Gulma, sannan kuma sai ya koma wajen wadancan suma sai ya bayyana masu cewa gashi gashi har dai takan haka musiiba ta samu ayi fitina, wacce zata sanya hakan a samu gābā a tsakanin jama'a wannan shine Annamīmanci!_
.
_Acikin suratul Hujurāt aya ta 6 Allah yana cewa  "Yãkũ waɗanda sukayi ĩmãni! Idan fãsiqi Yãzo muku da wani babban lãbãri, to, ku nẽmi bayãni, dõmin kada ku cũci waɗansu mutãne a cikin jãhilci, sabõda haka ku wãyi gari a kan abin da kuka aikata kunã mãsu nadãma"   lallai wanda ya dauki Annamīmanci dabi'ar sa har yabar duniya a ranar Qiyamah yanaji yana gani za'a dika dībar ladansa ana baiwa wadanda yayi gulmar su da Annamîmanci, yana ji yana gani malā'iku suna dībar ladarsa kuma bai isa ya hana ba, sannan sai Allah ta'ala yayi umarni a jefashi acikin wuta, Allah ya tsare mu_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp


Share:

Wednesday, 13 September 2017

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA:HUKUNCIN WANDA YA KWANTA DA MATAR SA ALHALI TANA JININ HAILA !!

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA
***************008*******************
HUKUNCIN WANDA YA KWANTA DA MATAR SA ALHALI TANA JININ HAILA
***************************************
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, da ikon Allah wannan shine bayani na takwas kuma kamar yadda nayi maku bayani cewa in shaa Allah acikin wannan rubutun zamu yi bayani ne akan hukuncin wanda yaje ya tara da matarsa alhali lokacin tana under jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) kuma zamuyi bayani ne da hujjoji daga Littãfin Allah ta'ala da kuma Hadisan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, muna fatan Allah ta'ala ya taimake mu.
.
Duk wanda yaje ya sadu da matar Alhali tana yin jinin haila to ya sa6a ma Allah kuma ya sa6a wa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, domin kuwa sunyi hani da aikata haka kamar yadda mukayi bayani acikin rubutun mu daya gabata kuma duk munyi bayani akan itama matar Haramun ne tayi masa biyayyah a wannan lokacin dogaro da hadisi ingatacce,
.
Hadisi yazo acikin Sunan na Tirmidhiy daga Abiy-Hurairah Allah ya kara masa yarda yace, lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace    "DUK WANDA YA KWANTA DA MATAR SA ALHALI TANA JININ HAILA, KO KUMA YA KWANTA DA MATAR SA TA DUBURA KO KUMA YAJE WAJEN BOKA, TO HAKIKA YA KAFIRCE MA ABINDA AKA SAUKAR WA ANNABI MUHAMMAD S, A, W)   Duba Sunan na Tirmidhiy hadisi na 116
.
Imamun-Nawawy Rahimahullah yace "Dukkanin musulmin da ya kudurce cewa ya halatta mutum ya kwanta da Matar sa alhali tana yin jinin haila, wato ya sadu da ita ta farji to hakika wannan mutumin ya kafirta, yayi ridda ya fita musulunci, amma idan mutum ya aikata hakan ba tare da yana mai halatta wa ba:-  Idan ya kasance ya aikata hakan da mantuwa ko kuma jahili ne baisan meye haila bama shi kwata-kwata a rayuwar sa, ko kuma jahili ne baisan cewa Haramun bane saduwa da mace alhali tana yin jinin haila ko kuma yana ganin makaruhi ne, to babu komai akan sa kuma babu kaffara akan sa,   amma idan ya kwanta da ita alhali tana yin jinin haila da gan-gan kuma yasan jinin haila matar take yi kuma ya tabbatar cewa saduwa da mace alhali tana yin jinin haila Haramun ne amma yaje ya sadu da ita, to hakika ya fadawa sa6on Allah mai girma a wajen Imam Shafi'ey lallai wannan zunubi ne mai girman gaske, ya zama wajibi a gareshi daya tuba zuwa ga Allah madaukakin sarki, kuma wajibi ne sai yayi kaffara kamar yanda jamhur suka tafi akai"  (Duba Sharh Muslim na Imamun-Nawawy 3/402)
.
YANDA AKE YIN KAFFARA:-  Sheikh Abdul-Azeemu Badwiy Allah madaukakin sarki ya kiyaye shi yace   "Zance da yafi tabbatuwa shine yin kaffara ga wanda ya sadu da ita alhali tana yin jinin haila wajibi ne, saboda hadisi ya tabbata daga Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda yace, lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace dangane da hukuncin wanda yaje wa matar sa alhali tana haila sai yace   "Zaiyi dadaqah da Dinare ko Rabin Dinare"  (Duba Sunan na Ibn Maajah hadisi na 523 Abu-Dawuda hadisi na 264  Tirmidhiy hadisi na 136 Bulughul-Maram hadisi na 157) kuma wannan itace fatawar Albany acikin littafinsa Samarul-Mustadaabah, duk da wasu sunyi kokari wajen tabbatar da cewa wannan hadisin ba maganar Annabi bace maganar sahabi ce, to zance mafi Inganci shine wannan hadisi ne marfuu'ey,
.
KARIN BAYANI AKAN YANDA AKE KAFFARA:-    "Lallai Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda baiyi kasa a gwiwa ba wajen ganin yayi bayani akan wannan hadisin daya ruwaito daga Annabi, yace  " Karin bayani domin tabbatar da fahimtar wannan hadisi ya shafi farkon zuwan jini ne da kuma karshen sa, domin kuwa ya tabbata daga Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda yace (Mauquuf)  :-" Lallai ga wanda ya sadu da Matar sa alhali tana yin jinin haila farkon farawar ta wato a lokacin data fara to wannan zaiyi sadaqah da Dinare cikakke, amma wanda ya gaza hakuri jinin hailar ya dauke alhali kwanakin sun kusa cika yaje ya kwanta da Matar sa to lallai zaiyi sadaqah da Rabin Dinare"    (Duba acikin Sunan na Abiy-Dawuda hadisi na 238 ko kuma kaduba Al-wajiiz 53),
.
Don haka dai yaku  'yan uwa duk wanda ya sadu da matar sa alhali tana yin jinin haila to ya aikata babban zunubi wanda kuwa ya halatta hakan to in Allah ya yarda ya kafirta ya zama arne, ke kuma 'yar uwa ta idan mijin ki ya nemeki alhali kina jinin haila Haramun ne ki amince masa, Alhamdulillah wannan shine karshen fai-fai na 008 in shaa Allah acikin rubutun mu na gaba zamuyi bayani ne akan ABUBUWAN DA SUKA HALATTA GA MAI JININ HAILA, Allah yasa Mudace
.
Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah Abu-Nabeelah Kuriga
.
             **20/Shawwal/1438**
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp
Share:

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA:MEYE YA HARAMTA GA MAI JININ HAILA DA KUMA JININ HAIHUWA?


HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA
***************006*******************
MEYE YA HARAMTA GA MAI JININ HAILA DA KUMA JININ HAIHUWA?
***************************************
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, 'yan uwa barkan mu da wannan lokaci tare da fatan kuna cikin koshin lafiya, a yau cikin wannan rubutu da zauren SA'ADATUL-MUSLIM yake gabatar wa in shaa Allah acikin wannan fitowa ta shida din zaiyi mana bayani ne akan ababen da suka zama haramun ga mace wacce ta kasance tana yin jinin haila da kuma mace wacce ta haihu wato jinin biiqi, Allah ta'ala muke roko ya taimake mu kuma ya kar6a mana kuma ya bamu ikon rubuta dai dai kuma ya taimake mu wajen yin riko da gaskiya, Allah yasa Mudace,
.
1 SALLAH DA AZUMI:-  Bai halatta ba ga mace wacce take acikin kwanakin jinin haila (wato tana yin jinin haila) ko kuma wacce take acikin kwanakin jinin haihuwa (wato tana yin jinin biiqi) su dika yin sallah ko kuma su dika yin azumi saboda hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Abiy-Sa'eed Al-Khudriy Allah ya kara masa yarda yace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace, "Ashe baku san idan mata suna yin jinin haila basu yin sallah kuma basu yin azumi ba?"  Muslim hadisi na 79 Bulughul-Maram shafi na 71 hadisi na 158,  Fiqhul-Muyassir na Sa'ad Yusuf shafi na 55,
.
Amma idan suka samu tsarki daga jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) to bazasu rama sallah ba amma dai zasu rama azumi domin kuwa hadisi yazo acikin Bukhari da Muslim daga A'isha Allah ya kara mata yarda tace  "Lallai mu mun kasance muna yin jinin haila a zamanin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi kuma ya kasance Annabi yana yi mana umarni cewa mu rama azumi, amma kuma baya umartan mu cewa mu rama sallah" (duba Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu)
.
2 `DAWAFI A DAKIN KA'ABA:-  Baya halatta ga mai jinin haila ko jinin biiqi tayi d'awafi a dakin ka'aba saboda hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Uwar Muminai A'isha Allah ya kara mata yarda tace  "Lokacin da muka isa Sarifa sai haila ta sameni, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace  "Ki aikata dukkanin abinda mai aikin hajji yake aikatawa sai dai banda d'awafi ga dakin ka'aba har sai kinyi tsarki"  Muslim hadisi na 1211  duba Bulughul-Maram hadisi na 159 duba Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu,
.
3 SADUWA DA ITA (TA FARJI):- Haramun ne saduwa da mace alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) kuma Gaskiya dalilai akan haramcin haka suna da yawa amma dai in shaa Allah a fitowa ta 007 zamuyi bayani ne akan wannan matsalar ta 3 tare da maganganun malamai da hujjoji daga Al-Qur'ani mai girma don haka  'yan uwa a saurare mu a rubutu na gaba, Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh,
.
Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah Abu-Nabeelah Kuriga
.
                  **16/10/1438**
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp
Share:

Friday, 25 August 2017

SHIN WANKAN JUMA'A WAJIBI NE!!!?

*SHIN WANKAN JUMA'A WAJIBI NE!!!?*
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
الحمد لله رب العالمين والصلاة والسلام على رسول الله صلى الله عليه وسلم، وبعد السلام عليكم ورحمة الله
.
_'Yan uwa abokai ma'abota zauren Sa'adatul-Muslim na whatsapp jiya juma'a  mun gabatar da shirin mu karu da juna kuma muka fitar da tattaunawar tamu akan cewa shin wankan juma'a wajibi ne ko kuma ba wajibi bane, kuma alhamdulillah mun samu amspshi daban-daban daga gareku masu fa'idantar wa da kuma soyuwa, ta bangaren maza mun samu amsoshi haka kuma ta bangaren mata mun samu amsoshi muna ma Allah ta'ala godiya da ya kasance mafiya yawan ku sun amsa wannan tambayar dai dai kuma muna rokon Allah ya saka maku da alkhairi, in shaa Allahu yanzu zamu takaita amsar wannan tambaya na cewa shin wankan juma'a wajibi ne ko kuma ba wajibi bane?_
.
_Zance na gaskiya itace dan uwa ko 'yar uwa abinda yafi cancanta a gareku shine kuyi wanka ranar juma'a lallai anaso dukkanin musulmi yayi wanka kafin yatafi masallaci domin yin sallar juma'a akwai hadisai masu yawa da suke nuna falala ga wanda yayi wanka ranar juma'a, amma dai lallai fa an samu sabanin malamai dangane da cewa shin wankan juma'a wajibi ne ko kuma ba wajibi bane, amma zancen da malamai suka rinjaya akansa sosai shine wankan juma'a ba wajibi bane sai dai mustahabbi ne kayi wanka shi yafi,_
.
_Dan uwa idan kaduba littafin Fiqhus-Sunnah zakaga tattaunawar malamai akan wannan matsalar zakaga kaulin da yafi rinjaye shine wankan juma'a ba wajibi bane wannan shine kaulin Imamu Shafi'i da Qurdubiy da Hafiz Ibn Hajar,  haka idan kaduba Al-Mughniy na Ibn Qudamah 5009/704  zakaga sa6anin malamai akai amma zancen da yafi rinjaye shine wankan juma'a ba wajibi ne sai dai mustahabi ne wato idan kayi ka kyautata sosai da sosai wannan shine kaulin Imam Tirmidhiy da Auza'i da Imamu Ath'thauriy da Maalik da Shafi'i da Ibn Munzir da Ibn Abdil'barri, da wasu daga cikin magabata, wanda ya duba zaiga hujjoji masu yawa akan hakan in shaa Allah, don haka wankan juma'a ba wajibi bane amma dai dan uwa kayi wanka shu yafi domin kuwa mustahabbi ne,_
.
_'Yan uwa abokan aiki da iyayen mu da kannemu Allah ya sakanka maku da alkhairi, sai kuma wani lokacin idan muka bijiro maku da wata tattaunawar, Alhamdilillah Allah yayi mana jagoranci,_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp


KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
Share:

Tuesday, 22 August 2017

_WANENE IBN TAIMIYYAH_ (fitowa ta 6)

*_WANENE IBN TAIMIYYAH_*
➖➖➖➖6⃣➖➖➖➖
★ Ga masu bukatar page dinmu sai su shiga wannan link din suyi like  https://free.facebook.com/إبن-تيمية-رحمه-الله-136792630155923/?_rdr
.
*Rasuwarsa*
.
_Allah ya kar6i ransa a gidan maza na birnin Dimashqa yana da shekaru 67 wadanda suke cike da karantarwa da haquri da jihadi. Ya rasu kafin wayuwar garin litinin 20 ga watan Zul Qi’ida 728H, Bai yi aure ba ballantana ya bar zuri’a. Bai kuma ta6a furta kalima d'aya da take nuna rashin sha’awarsa ga auren ba. To, ko me ya hana shi cin moriyar wannan Sunnah? Sanin gaibu sai Allah,, muna rokon Allah ta'ala yayi masa rahama, kada 'yan uwa suga mun takaita tarihin sa suyi hakuri nan gaba kadan zamuzo in shaa Allahu mu baku cikakken tarihinsa filla-filla, Allah yasa mu dace_
.
*Littafan da Aka Duba Don bada Tarihin sa*
.
*1:- Al’Uqudud Durriyyati Min Manaqibi Shaikhul Islam Ibni Taimiyyati na Muhammad dan Ahmad dan Abdulhadi, tahaqiqin Muhammad Hamid Al-Faqi, bugun Darul Katib Al-Arabi.*
.
*2:- Al’A’alamul Aliyyati na Bazzar, tahaqiqin Zuhair Shawish, bugun Al-Maktabul Islami, Beirut, Lebanon.*
.
*3:- A’ayanul Asri na Ibnu Aibak As-Safadi, tahaqiqin Ali Abu Zaidah da wasu, bugun Darul Fikri, Beirut, Lebanon.*
.
*4:- Ad-Durar Al-Kaminatu Fi A’ayanil Mi’ati As-Saminti, na Hafiz Ibnu Hajar Al- Asqalani, tahaqiqin Sayyid Jad Alhaq, bugun Jami’ar Ummul Qura, makka, Saudi Arabia.*
.
*5:- Buhus An-Nadwatil Alamiyyati An Shaikhul Islam Ibni Taimiyyati, tahaqiqin Muqtada Hasan, bugun Dar As-Sami’i.*
.
*6:- Da’awatu Shaikhil Islami Ibni Taimiyyata Wa Asaruha Fil Harakatil Islamiyyatil Mu’asirati, na Salahuddin Maqbul, bugun Majma’ul Buhusil Ilmiyyati, New Delhi, India 1412H/1992M.*
.
*7:- Dhailu Dabaqatil Hanabilati, na Hafiz Ibnu Rajab Al-Hambali, tahaqiqin Muhammad Hamid Al-Faqi, bugun Darul Ma’arifati, Beirut, Lebanon.*
.
*8:- Shajaratuz- Zahab Fi Akhbari Man Zahab, na Ibnul Imadi Al-Hambali, bugun Darul Fikri, Beirut, Lebanon.*
.
*9:- Shaikhul Islami Wa Juhuduhu Fi Ilmil Hadis, na Firiwa’i, bugun Darul Asimati. Husulul Ma’amul Min Kalami Shaikhil Islami Ibni Taimiyyata Fi Ilmil Usul, na Abdurrahman xan Abdullahi Al-Amir, bugun Darul Waxan, Riyadh, Saudi Arabia, 1423H/2002M.*
.
*10:- Ibnu Taimiyyah: Hayatuhu Wa Asruhu, na Imam Muhammad Abu Zuhrata, bugun darul Fikril Arabi, Alqahira, masar. 1898H/1974M.*
.
_Alhamdulillah Allah ta'ala kashiryar damu_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp


Share:

Sunday, 20 August 2017

_WANENE IBN TAIMIYYAH_(fitowa ta 5)

*_WANENE IBN TAIMIYYAH_*
➖➖➖➖5⃣➖➖➖➖
★ Ga masu bukatar page dinmu sai su shiga wannan link din suyi like  https://free.facebook.com/إبن-تيمية-رحمه-الله-136792630155923/?_rdr
.
_A rubutun mu daya gabata mukace Ko bayan komawarsa gida Shekhul Islam yaci gaba da samun matsaloli da malamai masu qaramin sani da taurin kai. Kamar yadda suka yi cah a kansa wai don yace, in mutum yayi rantsuwar saki kaffara kawai zai yi, aurensa na nan Haka ma don cewar da yayi saki uku na komawa daya idan anyi su a zama guda. Wadannan malamai basu samu sukuni ba sai da suka sa aka hana shi fatawa a shekarar 719H._
.
_A shekara ta 720H aka sake iza qeyar babban malamin zuwa gidan kaso in da ya share wata biyar da kwana goma sha takwas. A shekara ta 726H wasu alqalai sun tsoma bakinsu a cikin rikicin Ibnu Taimiyyah da maqiyansa, inda aka wallafa wata fatawa ta qarya aka jingina ta gareshi, wai ya haramta ziyarar qabarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam dana sauran Annabawa, Alhalin shi kuwa ya rarrabe tsakanin ziyararsu ne ita kad'ai da kuma had'a ta da yin tafiyayya. Ya labarta sa6anin magabata a kanta, sannan ya nuna karkata ga hanawa idan ya kasance anyi tafiyayya saboda ita. Ya kuma bayyana hujjojinsa na ingantattun hadissai. Wannan rikicin ma dai sai da ya sake mayar da wannan bawan Allah a gidan maza, inda ya samu damar da ya yawaita wallafe- wallafe gami da bautar Allah Ta’ala A shekara ta 728H aka fitar da duk littafan da ke tare da shi da alqalumma da tawadar da aka samu a wurinsa, saboda wani malami da ake kira Ikhna’i ya kai qarar sa, don yayi masa raddi, kuma wai ya jahiltar dashi. A nan ya zama dole Ibnu Taimiyyah ya haqura ya duqufa ga zikiri da sallah da karatun Alqur’ani da yake wadannan suna a kansa tun zamanin quruciya._
.
_*RASUWAR IBN TAIMIYYAH* zamu cigaba in Allah ya yarda a darasi na gaba, ga Allah muke neman taimako_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp


KARKU MANTA GAYYATO MANA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.


Share:

Friday, 18 August 2017

Sako zuwa ga marasa lafiya

SAKO ZUWA GA MARAR LAFIYA


ابن تيمية رحمه الله;
Yana cewa;
*"Mafi yawa daga cikin marar lafiya suna samun waraka da lafiyane saboda adduarsu da rokon da suke awajan Allah ko su sami waraka ta hanyar Ruqya da ayoyin alqurani da addu'o'in da Manzon Allah ﷺ ya koyar da dogaran zuciyarsu da Allah da kyautata zatonsu zuwa ga Allah,ba dan maganin da suka sha ba"*
@الفتاوى ج ٢١ ص ٥٦٣
Sakon da yake nan shine;
"Ya kai marar da lafiya ko wanda yake jiyar marar lafiya ku kyautata zaton waraka tana wajan Allah ba shan magani ba kadai ba kwarewar lafiya ba kadai,ku yawaita yin addua idan maku da lafiya tare da neman waraka ta hanyar karatun alqurani da addu'o'in da Manzon Allah ya koya,ko sha magani a matsayin sababin samun sauki sannan ku dogara da sauki yana wajan Allah kadai".

ابن القيـّم رحمـه اللـه:
Yana cewa;
*"Ambaton Allah da karatun alqurani da addu'o'i da komawa zuwa ga Allah da dogaro ga Allah da kiyaye sallah,yana warakar da masu rashin lafiya da yawa kuma yana yaye damu ga mutane da yawa da yardar Allah"*
@مفتاح دارالسعادة ١ / ٢٥٠ 

ابن القيم رحمه الله: 
Yana cewa;
*"Babu wata chuta daga cikin chutukan zukata da chutukan jiki,face acikin alqur'ani akwai waraka ta wannan chuta ko hanyar samun warakarta"*
@زاد المعاد[٤/٣٥٢]

Wannan yana nuna mana mu yawaita karatun alqurani zamu sami raka na dukkan chutukan mu dana yan uwanmu.

محمد بن نصر المروزي:
Yana cewa;
*"Bamu san wani aikin Dha'a ba da Allah yake tunkude azaba da damuwa saboda shi kamar Sallah"*.

ابن الجَوْزِي رَحِمَهُ الله:
*"Yawan karanta alqur'ani yana aiki wajan warakar rashin lafiyar zuciya da jiki wanda zuma da sauran magani baya iya warkarwa da yardar Allah"*
@"التبصـرة" صـ (٧٩) 

ابن حجر رَحِمَهُ الله:
Yana cewa;
*"Allah ya sanyawa Masoyansa mafi ga dukkan abinda ya dora masu na jarabawa,kadai yana jinkirta samun warakarsu ne idan basu da lafiya dan ya daukaka matsayinsu da yawaita ladarsu mai yawa"*
@فتح الباري 6/483


أبو إسحاق الحربي رَحِمَهُ الله:

Yana cewa;
*"Bana kai kukana zuwa ga Mahaifiyata ko yar uwata ko matata ko wajan ya'yana ko mutum babu abinda zai kara maka sai damuwa ka kai kuka zuwa ga Allah shi kadai,a wajansa ne ake samun maganin dukkan damuwa"*

Mahaifina yayi jiya tsawon shekara goma sha biyar bai taba kai kukasa ba zuwa ga kowa ba sai Allah shi kadai.

Nima shekarana goma ina gani da ido daya dayan baya gani amma ban taba kai kukana ba zuwa ga kowa ba.
@طبقات الحنابلة (٨٧/١).


الشيخ عبد الرحمٰن السعدي رَحِمَهُ الله:
Yana cewa;
*"Addu'a takobice ta mai karfi da mai rauni,makamine na samun waraka daga dukkan bala'i,da Adduane Annabawan Allah da siddiqai suke samun cin nasara"*
@مجموع مؤلفاته(٧٣٦/٢٣)


*اللهم الشفاء والطهور والنور والرفعة لجميع مرضى المسلمين*
              *اللهم امين*



*سبحان الله وبحمده عدد خلقه ورضا نفسه وزنة عرشة ومداد كلماتة سبحان الله العظيم ..*

KARKU MANTA DA GAYYATO MANA ABOKONANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.



Share:

Kebance Ranar Jumu'a da yin azumin nafila !!!

*_KE6ANCE RANAR JUMA'A DA YIN AZUMIN NAFILA!!!_*
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
السلام عليكم ورحمة الله وبركاته وصلاة والسالم على النبي المصطفة، محمد صلى الله عليه وسلم.
.
_Dan uwa na kasani lallai Allah madaukaki yayi maka rahama, kuma kasani wajibi ne a gareka ka koyi ilimin addinin ka na musulunci domin ka bauta wa ubangijin ka'aba yanda ya shar'anta maka ta hanyar Annabinsa Muhammad saw, domin tabbatuwa akan hanyar kwarai, wannan rubutu da zauren SA'ADATUL-MUSLIM yayi maku tsarabarsa a yau to in Allah ya yarda wani hadisi ne zamu dauka mu karanta domin tunstarwa kamar yanda musulunci yayi mana tanadi ga Allah muke neman taimako kuma muna rokon sa yayi mana agaji yayi mana jagoranci,_
.
_Dan uwa na kasani Lallai ke6ance ranar juma'a da yin azumin nafila bai halatta ba ga musulmi wanda yake kokarin bin tafarkin manzon Allah saw, lallai bai halatta ba ga kowwanene ya ke6ance ranar juma'a kadai yace zai dika yin azumi na nafila  acikinta amma kuma kasani ya halatta ga wanda ya kasance yana yin azumin nafila irin na Annabi Dauda Alayhis-Salam wato yau yayi azumi gobe yasha ruwa jibi ma sai ya dauka azumi, haka dai zaiyi tayi a rayuwarsa to wannan ya halasta a gareshi yayi azumi a ranar juma'a idan ranar daukan azuminsa yayi dai dai da wannan ranar,_
.
_Sannan kuma ya halasta idan ana bin mutum azumi na ramadan ko kuma na bakance ko na rantsuwa ya halasta yayi a ranar juma'a idan ya nufaci aikata hakan, domin kadai mu abinda muke magana akai shine hani dangane da ke6ance yin azumin nafila a ranar juma'a,  hadisi ya tabbata daga Ahmad dan Mansoor Al-Maruuziy yace Salmata dan Sulaiman ya bamu labari yace Abdillahi dan Mubarak ya bamu labari yace Abdillahi dan Muhammad dan Umar dan Aliyu daga Mahaifin sa yace, lallai Kuraiba Maula Ibn Abbas ya bashi labari cewa, lallai Ibn Abbas da wasu mutane daga cikin sahabban Manzon Allah saw sun aike ni wajen Ummu-Salamah cewa intambaye ta dangane da wad'anne ranaku ne Annabi saw yake yawaita azumi acikin su? Sai tace yana yawaita azumi ranar asabar da lahadi yace sai na dawo zuwa wajensu sai na basu labari dangane da amsar data bani, lallai su sun nuna kamar suna inkarin haka, sai Ibn Abbas da sauran sahabbai suka tashi gaba dayansu sai suka tafi wajen ta sai sukace, lallai mu mun aiko dan sako zuwa gareki acikin amsar da kika bashi kin ce wai kaza da kaza (wato suka ambata mata amsar data bayar) shin da gaske amsar da kika bayar kenan (wato cewa Annabi yana yawaita yin azumi ranar asabar da lahadi)? Sai tace yayi gaskiya lallai Manzon Allah saw yana yawaita yin azumi ranar asabar da lahadi, domin kuwa lallai wad'annan ranakun sun kasance ranar Idi ne ga mushrikai (Wato ranar asabar yahudawa Ahlil Kitab suna girmama wannan rana, su kuma nasara wato Christoci suna girmama ranar lahadi,) to kuma lallai ni inaso na sa6a masu, (tunda dai su suna cin kwalliya da ado da girke-girken ababe da wake-wake da shirka da kafirci suna ciye-ciye, to lallai ni in yin azumi ne domin na sa6a masu akan abinda suke akai na 6arna), (Wannan hadisi ne ingantacce wanda Ibn Khuzaimah ya kawo shi acikin Sahihu Ibn Khuzaimah mujalladi na 3 shafi na  318,)_
.
_Don haka dan uwa na Sunnah be ka dika yin azumin nafila ranar asabar da lahadi, domin yin koyi da manzon Allah, kuma kasani haka dabi'ar Manzon Allah saw yake dukkanin abinda ya kasance yahudawa sunayi acikin wannan duniyar to Annabi duk yanda zaiyi ya sa6a masu sai yayi domin kada yayi kamacece niya da baahude ko bana sare, shin kai haka kake!? Allah shi gafarta mana, lallai zaman lafiya ga dan Adam shin koyi da Annabi saw Allah yasa mudace,_
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb 
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp



KARKU MANTA DA GAYYATO MANA DA ABOKANANKU ZUWA WANNAN SHAFIN MUN GODE.
Share:

Archive

Unordered List

Support