DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 21
101. Wani aboki yana bin ka don ya koyi alherinka. Wani kuma yana bin sawunka don ya kama laifinka. Rinka hattara da abokai.
102. Wani mutum idan ka yi ma sa alheri zai saka maka ne da sharri. Idan ka amfane shi zai cuce ka. Idan ka sa shi inuwa zai jefa ka a rana. Kada ka damu. Ka ci gaba da yin alheri, kowa halinsa ya ke yi.
103. Da yawa mutanen da muka san su, muka yi, hulda da su a yau sun riga mu gidan gaskiya. Idan yau mu ne, wata rana ba mu ne ba.
104. Idan ka ga mutane suna tururuwa zuwa gidanka abin bukatarsu ne Allah ya ajiye a wajenka. Idan ka rasa shi kowa zai kama gabansa. Kada ka nemi hutu daga taimakon jama'a. Daukakarka ita ce bukatuwar su zuwa gare ka.
105. A wuri uku ake samun halin mutum: Idan aka ba shi aure, ko aka yi ciniki da shi, ko aka yi tafiya mai nisa a tare da shi.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
26/10/1438
20/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment