DAGA ZAUREN FIQHU :
LABARIN ANNABI ISA (AS) DA WANI MUTUM MAI KWADAYIN DUNIYA.
Watarana Annabi Eisa (as) yayi niyyar tafiya wani gari Mai nisa domin yin Wa'azi sai wani mutum daga cikin mutanensa yace zai bi shi.
Annabi Eisa (as) ya taho musu da guzurin wata Gurasa kwaya biyar. Sai ya mika ma wannan mutumin domin ya ajiye musu.
Suna cikin tafiya sai suka tsaya suka ci guda daya-daya. (saura uku kenan suka rage) Don haka sai wannan Mutumin yaci gaba da ajiyewa.
Da suka Qara yin gaba sai Annabi Eisa (as) yace masa "Fito mana da Gurasar nan guda uku muci".
Sai yace "A'a Ya Ruhallahi, guda biyu dai ko?".
Wato ashe ya boye ya cinye guda daya aciki. shi yasa yace sauran kwaya 2.
Kun san dabi'ar Dan Adam, kullum yafi so ya samu abu fiye da sauran mutane.
Da Annabi Eisa (as) ya tambayeshi to ka swn dai guda uku ne suka rage. Shin ina sauran gudar? Sai yace A'a shi fa SAM!! guda biyu aka bashi ajiya!!!.
Shi kenan suka ci gaba da tafiya har suka je tsakiyar wani Daji. anan suka ga wata barewa tare da 'Ya'yanta guda biyu.
Sai Annabi Eisa (as) ya kira daya daga cikin 'ya'yan barewar nan. Yazo suka kwantar dashi suka yanka, suka fede, suka gasa suka ci.
Bayan sunci sai Annabi Eisa (as) ya ta'ba jikin barewar, yace mata "TASHI DA IZININ ALLAH".
Nan take sai ta mike taci gaba da rayuwarta.
Sai Annabi Eisa (as) ya dubi abokin tafiyar tasa yace masa "INA ROKONKA DON GIRMAN UBANGIJIN DA YA NUNA MAKA WANNAN AYAR (YA RAYA WANNAN BAREWAR BAYAN MUTUWARTA) INA SO KA GAYA MIN GASKIYA.
SHIN WAYE YA CINYE GURASAR NAN GUDA 'DAYA?"
Sai yace "A'a ni bani bane. Kuma ban san wanda yaci ba".
Shikenan sai suka ci gaba da tafiya har suka je bakin wani Qaton kogi. Da suka zo sai Annabi Eisa (as) yayi addu'a nan take suka har kan ruwan kogin suna tafiya da izinin Allah ba tare da sun nutse ba.
Bayan sun tsallake, sai Annabi Eisa (as) yace ma abokin tafiyar tasa :
"KA DUBI GIRMAN UBANGIJIN NAN WANDA YA NUNA MAKA WANNAN AYAR (DA IKONSA NE MUKAYI TAFIYA AKAN RUWA BA TARE DA MUN HAU KOMAI BA, KUMA BAMU NITSE BA) KA GAYA MUN GASKIYA. SHIN WANENE YA CINYE GURASAR NAN GUDA DAYA? "
Sai mutumin nan ya sake rantsewa cewa Shi fa WALLAHI ba shine yaci ba, kuma bai san ko waye yaci ba.
Sai Annabi Eisa (as) yayi shuru ya kyaleshi suka ci gaba da tafiya. Sunzo cikin tsakiyar daji sai suka zo wani waje. Sai Annabi Eisa (as) ya debi Qasa ya tara, sannan yace "KI ZAMA ZINARE (GOLD) DA IZININ ALLAH". Nan take sai wannan Qasar ta zama wani Qaton dunkulen Zinare.
Sai Annabi Eisa (as) ya raba Zinaren kashi uku. Sannan yace ma Mutumin: "Kashi 'daya nawa, kashi daya naka, kashi 'daya kuma na Mutumin da ya cinye gurasar nan! "Sai mutumin nan ya kada baki yace "YA ANNABIN ALLAH, AI NINE DAMA NA CINYE GURASAR NAN".
Kunji fa Mutumin duniya. An nuna masa Mu'ujizozi har guda biyu, kuma na rokeshi don girman UBANGIJIN da ya nuna masa wadannan Mu'ujizozin, amma duk da haka yaqi ya fadi gaskiya. Sai yanzu da yaga abin duniya.
To shikenan sai Annabi Eisa (as) yace masa "To na bar maka duk Zinaren nan ka rike ya zama naka".
Shikenan wannan mutum yana zaune tare da zinarensa yana tunanin yadda zai yi dashi sai ga wasu Mutane su biyu sunzo wucewa. Da suka hangeshi tare da wannan dukiya mai yawa, sai sukayi niyyar su kasheshi su kwashe dukiyar. Don haka sai yace musu "A'a kar ku kasheni. Gara mu raba dukiyar nan gida uku. Kowannenmu ya dauki kaso guda.
Sun yarda sun amince, sun zauna suna hira tare dashi sai suka ji yunwa ta sawo su gaba..
Don haka suka yanke shawarar cewa zasu aika 'dayan cikinsu yaje cikin gari ya sayo musu abinci suci.
Bayan ya tafi cikin gari, ya sayi abinci yaci ya koshi sannan sai Shaitan ya riya masa azuciyarsa "Don me zan raba dukiyar nan tare da Mutanen nan, Mai zai hana in zuba musu Guba (Sammu) acikin abincin nan, idan sunci sun mutu sai in rike dukiyar nan gaba dayanta!! "
Su kuma bayan ya tafi sai sukayi shawarar mai zai hana idan ya dawo su afka masa da su bubbugeshi, su kasheshi su rike dukiyar atsakaninsu!!" Don haka yana dawowa sai suka hau Jibgarsa, basu dena ba har sai da suka ga ya dena numfashi..
Bayan ya mutu sai suka ce bari suci abincin nan su koshi.. Domin suji dadin raba dukiyar nan.
Bayan suci sun koshi, nan take sai suka kama shure shure. Nan suka suka mutu agefen wannan tarin Zinaren.
Rannan Annabi Eisa (as) ya dawo zai wuce ta kusa da wajen sai ya iske Gawarwakinsu ayashe agefen dukiyar.
Sai yace ma almajiransa (wadanda suka dawo tare dashi) :
"KUNGA FA, WANNAN ITA CE DUNIYA!! KUYI KAFFA-KAFFA DA ITA!!".
Aduba cikin KITABUZ ZUHDI na Imam Ibnu Abid-Dunya, shafi na 175 za'a ga wannan labarin.
Duniya kenan budurwar wawa, Kin gama da Uban mutum kinga bayan kakansa da kakan-kakansa ma balle shi.
Lallai muji Tsoron Allah, mu kiyayi handama da babakere..
Mu tsaya akan halal dinmu..
Kuma mu rika fadin gaskiya komai rintsi!!
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990
0 comments:
Post a Comment