DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 13
61. Idan ka ga mutum yan tsarguwa da shiga cikin jama'a, shi maha'inci ne. Idan ka ga mutum yna fushi a wurin jayayya to, maras hujja ne. Idan ka ga mutum yana fada, ba shi da abin fadi. Mai gaskiya ba ya tsoron jama'a. Mai hujja ba ya fushi. Mai abin fada ba ya fada!
62. Fulawa tana koya mana fara'a da murmushi. Tururuwa tana koya mana aiki. Zuma tana koya mana tsari. Zakara yana koya mana sammako. Kowace halitta da tata gwaninta.
63. Wanda ya fi kowa jin dadi a cikin mutane shi ne wanda bai damu da sha'anin mutane ba.
64. Ba duka wanda ka ke so ne yake amfanin ka ba. Ba kuma duka wanda ka ke ki ne yake cutar ka ba. Wuka ko tana da laushi yanka ta ke yi, magani kuma tare da dacinsa ana samun waraka a cikin sa.
65. Da zarar ka ji karar wayarka ka san wani yana son magana da kai ne. Kamar haka ne da ka ji kiran sallah ka san ubangijinka na neman ka. Kada ka sanya karba kiran mutane ya fi ma kka muhimmanci a kan kiran Allah.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
18/10/1438
12/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment