Dr Jalo Jalingo
'YAN BIDI'AH NE KE CEWA MU'AZU BIN JABAL BA YI DA
FIKHU:
Babu masu cewa Sahabin Annabi Mu'azu Bin Jabal ba
yi da fiqhu sai 'yan bidi'ar da ke raina shaidar Annabi
mai tsira da amincin Allah, suke kuma raina shaidar
sahabbansa, suke kuma raina shaidar Salafus Salih.
Dalilin wannan magana tawa kuwa shi ne:-
1. Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 3790, da Ibnu Majah
Hadithi na 154, da Ibnu Hibban Hadithi na 12,927, da
Bazzar Hadithi na 6,786 da isnadi sahihi daga Anas Dan
Malik ya ce:-
(( ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﺍﺭﺣﻢ ﺍﻣﺘﻲ ﺑﺄﻣﺘﻲ ﺍﺑﻮ
ﺑﻜﺮ، ﻭﺃﺷﺪﻫﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻤﺮ، ﻭﺃﺻﺪﻗﻬﻢ ﺣﻴﺎﺀ ﻋﺜﻤﺎﻥ، ﻭﺃﻗﺮﻭﻫﻢ
ﻟﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺑﻲ ﺑﻦ ﻛﻌﺐ، ﻭﺍﻓﺮﺿﻬﻢ ﺯﻳﺪ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ، ﻭﺃﻋﻠﻤﻬﻢ
ﺑﺎﻟﺤﻼﻝ ﻭﺍﻟﺤﺮﺍﻡ ﻣﻌﺎﺫ ﺑﻦ ﺟﺒﻞ )).
Ma'ana: Manzon Allah mai tsira da mincin Allha ya ce:
"A cikin al'ummata wanda ya fi kowa tausayin al'ummar
shi ne Abubakar, wanda ya fi tsanani wajen kariyar
hakkin Allah shi ne Umar, wanda ya fi kunya da gaske
shi ne Usman, wanda ya fi su kwarewa a karatun
Alkur'ani shi ne Ubayyu Bin Ka'ab, wanda ya fi su iya
rabon gado shi ne Zaid bn Thabit, wanda ya fi su sanin
Halal da Haram shi ne Mu'azu bn Jabal)).
2. Hakim ya ruwaito Hadithi na 5,187, da Sa'id Bin
Mansur Hadithi na 2,319, da Ibnu Abi Shaibah Hadithi
na 33,567, da Baihaqiy cikin Sunan Hadithi na 12,551 da
isnadi sahihi daga Aliyyu Bin Rabaah cewa:-
(( ﺍﻥ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﺧﻄﺐ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﺎﻟﺠﺎﺑﻴﺔ
ﻓﻘﺎﻝ : ﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺍﻥ ﻳﺴﺎﻝ ﻋﻦ ﺍﻟﻘﺮﺀﺍﻥ ﻓﻠﻴﺎﺕ ﺍﺑﻲ ﺑﻦ ﻛﻌﺐ،
ﻭﻣﻦ ﺃﺭﺍﺩ ﺍﻥ ﻳﺴﺎﻝ ﻋﻦ ﺍﻟﻔﺮﺍﺋﺾ ﻓﻠﻴﺎﺕ ﺯﻳﺪ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ، ﻭﻣﻦ
ﺃﺭﺍﺩ ﺍﻥ ﻳﺴﺎﻝ ﻋﻦ ﺍﻟﻔﻘﻪ ﻓﻠﻴﺎﺕ ﻣﻌﺎﺫ ﺑﻦ ﺟﺒﻞ )).
Ma'ana: ((Umar Dan Khattab Allah Ya Kara masa yarda
ya yi wa mutane huduba a Jaabiyah sai ya ce: Wanda
ke son ya yi tambaya game da Alkur'ani sai ya je gurin
Ubayyu Bin Ka'ab, Wanda kuma ke son ya yi tambaya
game da ilmin gado sai ya je gurin Zaid Bin Thaabit,
Wanda kuma ke son ya yi tambaya game da ilmin Fikhu
sai ya je gurin Mu'azu Bin Jabal)).
3. Ibnu Sa'ad ya ruwaito cikin Tabaqaat athari na 2,575
daga Sahal Bin Abi Hathmah ya ce:-
(( ﻛﺎﻥ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻔﺘﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﺛﻼﺛﺔ ﻧَﻔَﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻬﺎﺟﺮﻳﻦ ﺅﺛﻼﺛﺔ ﻣﻦ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭ : ﻋﻤﺮ، ﻭﻋﺜﻤﺎﻥ،
ﻭﻋﻠﻲ، ﻭﺍﺑﻲ ﺑﻦ ﻛﻌﺐ، ﻭﻣﻌﺎﺫ ﺑﻦ ﺟﺒﻞ، ﻭﺯﻳﺪ ﺑﻦ ﺛﺎﺑﺖ )).
Ma'ana: ((Wadanda suka kasance suna ba da fatawa a
zamanin manzon Allah mai tsira da amincin Allah
mutum uku ne daga cikin Muhajirai, da kuma mutum
uku daga cikin Ansarawa: Umar da Uthman da Aliyyu,
da Ubayyu Bin Ka'ab da Mu'azu Bin Jabal da Zaid Bin
Thaabit)).
Allah Ka tsare mu da musibar bidi'ah da kuma togewa a
kan kariya. Ameen.

0 comments:
Post a Comment