Mahaifinsu yana karkashin tasirin sihiri ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday 8 July 2017

Mahaifinsu yana karkashin tasirin sihiri

MAHAIFINSU YANA KARKASHIN TASIRIN SIHIRI :
TAMBAYA TA 2241
********************
Salam alaikum.
Da fatan anyi sallah lafiya. Allah ya karawa Mal Imani da taqawa.
Malam mahaifinmu ne tunda ya Kara aure yau shekara hudu zuwa biyar da suka wuce ba ya kula mu yayanshi samsam ko waya in munyi masa sai yaga dama yake dauka, kannanmu da yake da hakkin cinsu baya basu balle sha.
Malam har ta kai ta kawo sai yayi watanni bai ko leko gidan da muke ba, wataran har sai yayi tafiya wata kasar ya dawo sai dai mu sami labari a gari. Kwanakin baya har cewa yayi shi babu ruwanshi da mu. Mu je muyi duk abun da muka ga dama a duniya kuma muje zamu gani.
Gashi ina son Zan yi aure manema suna so su turo Amma yaqi saurarona yace babu ruwanshi. Malam tambaya ta a nan mene hukunci wannan furuci?.
2. Mene halin aurensu shi da mahaifiyarmu tunda babu wani mu'ala ta aure a duk shekarun nan.
3. Malam Zan iya yin aure ba tare da izininshi ba?
4. Ina so a taimaka mana da addu'a dan irin abubuwan da yake fada mana na maganganun batanci kamar da sihiri ko shaidanu. Allah ya saka da alkhairi.
Mal nagode Dan Allah a boye sunana.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya wajabta ma 'Ya'ya yin biyayya ga Mahaifansu, to su ma Mahaifan akwai hakkokin da Allah ya shar'anta ma 'Ya'yansu akansu.
Misali akwai ciyarwa da shawarwa da Ilmantarwa har zuwa lokacin da yaro zai isa balagarsa.
Akwai kuma tarbiyyantarwa bisa tsari irin na Islama. Akwai kuma kyautata alaqah da kuma yin adalci atsakanin iyalai.
To amma bisa yadda bayananki suka nuna, shi Mahaifinku duk yayi watsi da wadannan Hakkokin naku dake kansa, yana bin son ransa.
Shawarar farko wacce zan baki ita ce Ku rungumi hakuri dake da mahaifiyarki da sauran Qannenki. Kada ku watsar da nasa hakkin dake kanku. Ku rika sanyashi cikin addu'o'inku ako yaushe.
2. Bisa dukkan alamun abubuwan da yakeyi kamar akwai tasirin Sihiri ko Sammu atare dashi. Domin babu mutum mai cikakken hankali da zai Kyale iyalansa har tsawon wadannan shekarun ba ya kula dasu, alhali yana da hali, kuma gashi ana zaune gari daya.
3. Har yanzu Aurensu yana nan da Mahaifiyarki tunda bai ce ya saketa ba. Sai dai ku Qara hakuri kuma kuci gaba da yi masa addu'a har Allah ya yaye masa matsalar da yake ciki.
Idan kuma tana tsoron cutuwa ta dalilin rashin samun kulawa ko wata Mu'amala daga Mijinta, zata iya samun waliyyanta ta sanar dasu. Su zasu tuntubi nasa waliyyan su zauna atsakaninsu domin samun mafita acikin lamarin.
4. Miyagun Kalamai ko tsinuwa ko barrantar da kansa da yakeyi daga gareku, wannan ba zai shafeku ba. Mutukar dai baku aikata wani abu na rashin ladabi agareshi ba. Koda ya tsine muku babu abinda zai sameku. Allah ba zai yi fushi daku ba.
5. Addinin Musulunci yana umurni da Aurar da 'Ya Mace da zarar ta samu Manemi ba tare da wani Jinkiri ba. Don haka idan Mahaifinki Ya Qi ya sanya hannunsa cikin maganar aurenki, Ba zuciya zakiyi ba.
Kije ki kwantar da kanki ki tausasa lafazi gareshi ki nemi yafewarsa in har yana tunanin cewa wani laifi kikayi masa. Ki bashi hakuri domin samun hadin kansa.
Idan kuma Ya qi yarda ya fuskanci lamarin, to sai kije wajen 'Yan uwansa da danginsa Ko Mahaifinsa (Wato Kakanki idan har yana raye kenan). Ki sanar dasu halin da ake ciki.
Addini ya basu damar aurar dake. Zasu iya wakiltar Mahaifinki tunda shi ya qi amincewa. Idan kuma duk an bi wadannan hanyoyin amma ba'a cimma nasara ba, zaki iya kaiwa Maganar wajen Sarkin Gari ko Alqali. Su zasu iya aurar dake koda shi bai amince ba. Mutukar dai sun bincika sun gano yadda maganar take.
Daga karshe ku yawaita Tsaiwar dare da nafilfilin dare da rana. Domin ana samun taimakon Allah acikin rayuwa, idan akayi riko da Sallah.
Ku yawaita Sadaqah domin itama maganin Musibah ce. Sannan kuyi riko da LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYIL AZEEM. Ku rika yinta da yawa bisa niyyar neman Kubutar da Mahaifinku daga halin da yake ciki.
Domin bisa dukkan alamu akwai tasirin Sihiri ko wani abun atare dashi.
Allah ya sawwake, Allah ya bashi lafiya. Ku kuma Allah ya kawo muku mafita mafi kyawu, Aaameen.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support