Menene yaza wajibi akanmu dangane da sahabban manzon Allah ?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday 10 July 2017

Menene yaza wajibi akanmu dangane da sahabban manzon Allah ??

MENENE YAZAMA WAJIBI  AKAN MU DANGANE DA SAHABBAN MANZON ALLAH?


Abin da ya zama dole akan mu ga sahabban Manzon ALLAH [s.a.w]shine son su da Neman ALLAH ya yarda da su , da kuma kubutar da zuciyar mu da bakunan mu daga cutar da su, da kuma yada falalar su , tare da kamewa daga mummunan abin da ya faru a tsakanin su : domin su ba ma'asumai ba Ne {marasa laifi}.sai dai su masu kokari Ne {mujtahidai masu binciken gaskiya da nemanta}.Duk wanda yada CE daga cikin su yana da lada biyu ,amma idan yayi kuskure yana da lada daya akan kokarin sa {ijtihadin sa}.kuskure sa kuma an gafarta masa .kuma suna da kyawawan ayyuka wadanda zasu tafiyar musu da munanan da suka auku daga gare su ,inya auku .


Manzon ALLAH {s.a.w} yace "karku zagi sahabbaina, Na rantse da wanda raina ke hannun sa , da ace dayanku zai ciyar da kwatan kwacin dutsen uhudu Na zinari, ba zai kai ciyarwar dayansu ba Na mudun ko Rabin sa"

Bukhari da Muslim

Kuma manzon ALLAH [s.aw]yace "Duk wanda ya zagi sahabbaina to la'antar ALLAH da mala'iku da mutane bakidaya su tabbata akansa

"Dabaraniy"


ALLAH kakarawa sahabban annabi daraja baki dayan su

ALLAH kakaremu daga sharrin masu zagin su

ALLAH kayema sahabbai kurakuran su

ALLAH ka shiryar da masu zagin sahabbai in masu shiryuwa Ne

Naku Muhammad Saifullahi Abdulkarim lawan {ABU ZAYYAD}


08143470044
Zauran AHLUSSUNNAH

ALLAH kashiryar da masu zagin sahabbai amin
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support