Shekaru 500 yana bautar Allah ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday, 7 July 2017

Shekaru 500 yana bautar Allah

SHEKARU 500 YANA BAUTAR ALLAH
***************************************
Mala'ika Jibreelu (as) ya bama Manzon Allah (saww) labarin wani mutum daga cikin al'ummomin da suka gabata, wanda ya bauta ma Allah tsawon shekaru dari biyar (500).
Mutumin ya gida bukkarsa wacce yake ibada acikinta bisa kan Kololuwar wani dutse atsakiyar teku mai ruwan gishiri, Amma saboda ibadarsa sai Allah ya sanya wani kogin farin ruwa mai dadi yana bulbulowa daga kan dutsen domin wannan bawan Allahn yasha yayi alwala.
Sannan Allah ya sanya wata bishiyar Teen (wani abu ne mai kamar baure) ta tsiro akan dutsen. kullum wannan bawan Allahn yakan tsinki 'Dan itacen guda 'daya yaci.
Wannan Bawan Allahn yayi wata addu'a yana cewa "YA ALLAH KAR KA DAUKI RAINA, FACHE INA CIKIN SUJJADA".
Allah ya amshi Addu'arsa, ya rasu acikin sujjadah saboda haka duk lokacin da Mala'ika Jibreelu zai sauko Qasa sai ya tarar dashi kamar yana cikin Sallah.
Mala'ika Jibreelu (as) yace aranar ALKIYAMA Allah zai ce ma MALA'IKU "KU DAUKI BAWAN NAN NAWA KU KAISHI ALJANNAH SABODA RAHAMA TA".
Shi kuma wannan mutumin zai ce Shi dai yafi son ashigar dashi Aljannah saboda ladan ibadarsa.
Allah zai cewa Mala'ikunsa su auna ladan ibadar wannan mutumin da kuma ni'imar da Allah yayi masa ta tsawon wannan lokacin. da aka auna sai aka ga cewa ladan ibadar shekaru 500 din nan bai kai nauyin Ni'imar idanun da aka bashi ba ma.
Don haka za'a ce ma Mala'iku su wuce su kaishi wuta. sai mutumin nan ya firgita yace "To Ya Allah ka shigar dani Aljannah saboda rahamarka!!"
To anan ne zasuyi zance da Allah kamar haka :
Allah zai tambayeshi : "YA KAI BAWANA, WAYE YA HALICCEKA?"
Shi kuma zai ce "Ya Ubangiji kai ne ka halicceni".
Sai Allah yace masa "SHIN NA HALICCEKA NE SABODA WATA IBADAR DA KA TABA YIMIN, KO KUMA SABODA RAHAMATA NA YIKA?".
Sai yace ''Ya Ubangiji saboda rahamarka kayi ni".
Sai Allah yace masa "TO WAYE YA RAYAKA TSAWON SHEKARU 500 KANA IBADA ADUNIYA?"
Zai ce "Ya Allah kai ne ka rayani ka bani wannan damar".
Allah zai sake tambayarsa : "SHIN WAYE YA SANYAKA BISA KAN DUTSE ATSAKIYAR TEKU, KUMA YA SANYA RUWA MAI DADI YA BULBULO DAGA CIKIN RUWAN GISHIRI, SANNAN YA SANYA BISHIYA TA TSIRO DOMINKA? KUMA WAYE YA BAKA DAMAR RASUWA ALOKACIN DA KAKE CIKIN SUJJADA?"
Sai mutumin yace : "Ya Ubangijin Talikai! Kai ne duk kayi mun wannan".
Sai Ubangiji yace masa "DUK WANNAN YA FARU NE CIKIN RAHAMATA. KUMA KAI MA ZAKA SHIGA ALJANNAH NE DA RAHAMATA".
– ZAUREN FIQHU - Ya Allah ka sanyamu cikin ALJANNATUL FIRDAUSI don falalarka da rahamarka. ba don ibadarmu ko wani abu daga garemu ba.
Daga littafin Tanbeehul Ghafileen na Abul Layth As-Sarmaqandiy (rah).
DAGA ZAUREN FIQHU
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support