Dalilin ziyara ta gidan Buhari da ke Landan - Reno Omokri ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Sunday 30 July 2017

Dalilin ziyara ta gidan Buhari da ke Landan - Reno Omokri

- Reno Omokri ya bayyana dalilinsa na kai ziyara gidan Buhari da ke Landan

- Ya bayyana rashin jin dadinsa na munafurcin mulkin Gwamnatin Buhari

- 'Satar Kudin Gwamnati ba shine kadai Cin Hanci da Rashawa ba' - Omokri

Tsohon hadimin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya bayyana dalilin sa na ziyartar 'Abuja House' da ke Landan inda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake jinya yace 'ziyararsa zuwa gidan don ya bayyana rashin jin dadinsa na munafurcin mulkin Gwamnatin Buhari ne.'

Naij.com a satin nan ta kawo muku labarin Omokri da ya ziyarci gidan da hotunan da ya dauka.


A bidiyon da Reno ya saki yace 'Mulkin Gwamnatin Buhari yafi kowane mulki a tarihin Najeriya munafurci ya kuma fadi dalilan da ya sa ya fadi hakan.'
Dalilin ziyara ta gidan Buhari da ke

Landan - Reno Omokri
'Ya kamata ku san cewa 'Abuja House' ba gidan Shugaba Muhammadu Buhari bane. Ni dan Najeriya ne kuma ina biyan kudin haraji, Gwamnatin zata iya dubawa ta tabbatar da kudinmu ne yake tafiyar da 'Abuja House' din, don haka ina da damar zuwa god an.'

'' ya sake fadi.

'Gwamnatin Buhari tana takamar yaki da cin hanci da rashawa. Buhari ya dauka satar kudin Gwamnati ne kadai cin hanci da rashawa, rashin cika alkawarin da Shugabanni suka dauka lokacin zabe ma cin hanci da rashawa ne.'


'Gwamnatinsa ta jibge Jirgin Gwamnati a filin jirgin Landan yana jan kudinnmu a kullum. Saboda mutum daya Jirgin ya kwashe sama da kwana 80 a ajiye. Akwai ma’aikata da yawa da ba a biya su albashi ba, kudin zaman da jirgin yake ci zai iya biyan ma’aikata 2,000 albashi.'

'Najeriya tana daya daga cikin Kasashen da kananan yara basa zuwa makaranta a duk duniya sama da yara miliyan 12 musamman daga Arewacin Kasar. Yawan yaran da basa zuwa makaranta ya ninka yawan mutanen da ke Togo sau biyu.'

'Gwamnatin Buhari bata gina makaranta ko daya ba, amma Gwamnatin Jonathan ta gina makarantun almajirai a Arewa duk da Jonathan ba daga Arewa yake ba. Kudin da jirgin yake ci zai isa a gina makaranta, ko Gwamnatin zata iya sa a dawo da jirgin Najeriya.'
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support