Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Al-Kiyama ta kusanto, ga wasu daga cikin Alamomin ta, wasu sun faru, wasu suna faruwa, wasu za su faru nan gaba. Ga su nan kamar haka:
1. Aiko Annabi (sallallahu-alaihi-wasallam) {ranar litinin, 21/Ramadan/0013bh daidai da 10/August/610m} yana shekara arba’in 40 da wata shida 6 da kwana goma sha biyu 12 lissafin wata/ shekara talatin da tara 39 wata uku 3 da kwana ishirin 20.
2. Wafatin Manzon Allah (sallallahu-alaihi-wasallam) ranar litinin 12/rabi’ul-Auwal/11ah yana da shekara sittin da uku da kwana hudu.
3. Tsagewar wata
4. ‘Karewar Sahabbai
5. Bude Baitil-Makdis
4. ‘Karewar Sahabbai
5. Bude Baitil-Makdis
7. Bayyanar fitintunu masu yawa
8. Bayyanar tashoshin tauraron ‘Dan Adam
9. Yakin Siffaini
10. Bayyanar khawarij
11. Masu da’awar Annabta ta karya
12. Yalwatar Arzi’ki;- Arzi’ki zai yalwata
13. Bayyanar wuta a Hijaz, dutse mai aman wuta
14. Yaki da Turkawa
15. Bayyanar Azzalumai masu dukan babu dalili
16. Yawan zubar da jini;- kashe-kashe
17. ‘Dauke Amana;- masu Amana za su yi ‘karanci
18. Koyi da Yahudu da Nasara
19. Baiwa za ta haifi uwargijiyar ta
20. Bayyanar masu masu tsirara-tsirara (ba sa shiga ta addini)
21. Matsiya ta, Matasa takalma masu kiwon awaki, za su rika yin dogayen gine-gine
22. Yin Sallama ga wanda aka sani kawai;- mutane za su daina yi wa mutum Sallama sai sun san shi
23. Ya’duwar kasuwanci;- ko ina zai zama kasuwa
24. Mata za su yi tarayya da mazan su a kasuwanci
25. Wasu tsirarun ‘yan kasuwa za su mamaye kasuwanci;- ya zama ba a yi da kai sai da yardar su
26. Shaidar Zur
27. ‘Boye shaidar gaskiya
28. Yawan Rowa;- mutane za su zama marowata
29. Yanke zumunta
30. Munana makwaftaka
31. Ya’duwar laifuffuka
32. Bayyanar jahilci
33. Amincewa maha’inci, da tuhumar mai Amana
34. Mutuwar Mutanen ‘kwarai da Ya’duwar lalatattu
35. Yaki Halal Yaki Haram
36. Rubda ciki akan Baitil-Mali (Asusun-gwamnati)
37. Mayar da dukiyar Amana ganimah
38. Rashin fitar da Zakkah da da’din rai;- mutum ya ga zakka kamar Asara Ce yayi
39. Yin Karatu dan Neman Abun duniya
40. Yi wa mata biyayya da sa’bawa Uwa
41. Fifita Abokai/’Kawaye akan iyaye
42. Hayaniya a masallatai
43. Mafi yawan shuwagabannin Al’ummah za su zama fasiqai
44. ‘Kas’kantattu za su zama manyan gari
45. Girmama mutum don tsoron sharrin sa
46. Za a halatta Zina
47. Halatta Alhariri ga Maza (sa Alhariri ga maza haramun ne, amma za ayi zamanin da za a halatta shi
48. Ya’duwar Kayan maye
49. Ka’de ka’de da raye-raye za su mamaye Al’ummah
50. Masifa da Bala’i za su yi wa Har mutum ya dinga fatan mutuwa
0 comments:
Post a Comment