*_HUKUNCIN YIN SALLAR JAM'I A GIDA !!!_*
*_Tambaya_*
Assalamu alaikum. Malam mene hukuncin sallar namiji da ba ya son zuwa masallaci jam'i saidai ya tara iyalinsa a gida ayi sallah tare?
*_Amsa_*
Wa alaikum assalam
To 'yar'uwa Malamai sun yi sabani game da sallar jam'i a masallaci.
1. A wajan malaman Malikiyya zuwa sallar jam'i sunna ne saboda fadin Annabi S. A.W. "Sallar jama'a tafi sallar mutum daya da lada ashirin da bakwai" hadisin yana nuna ingancin sallar wanda ya yi sallah shi kadai, tun da an tabbatar masa da lada daya.
2. Ya wajaba yin sallah a masallatai a cikin jama'a saboda fadin Annabi (SAW) "Na yi niyyar na yi umarni a tsayar da sallar jam'i, ni kuma na je na kona gidajan wadanda ba Sa halarta sallah a masallaci" wannan ita ce maganar Malamai da yawa.
Ibnu-Mas'ud yana cewa: "Babu wanda yake kin zuwa sallar jam'i sai munafiki, wanda aka san shi da munafunci, akan kawo mutum ranga-ranga ba shi da lafiya a tsayar da shi a tsakanin Sahu".
Wani Makaho ya zo wajan Annabi (SAW) ya nemi ya yi masa izni ya yi sallah a gida saboda ba shi da Jagora, ya ba shi izni, bayan ya tafi sai ya Kira shi ya ce masa kana jin kiran sallah? sai ya ce E, sai ya ce to ka amsa".
Allah yana cewa a Suratul Bakara aya ta (43): "Kuma ku yi sallah tare da masu yin sallah"
A bisa dalilan da suka gabata za mu fahimci cewa: Yin sallar jam'i a masallaci shi ne abin da Shari'a ta zo da shi, kuma wajibi ne ga wanda yake da iko, tun da ga shi har Annabi (SAW) ya yi niyyar zai kona gidan wadanda ba sa halarta.
Idan akwai nisa tsakaninsa da masallaci ko kuma yana da lalura ba za'a ce ya aikata haramun ba in ya yi sallah a gida tare da iyalansa saboda fatawar Malikiyya da ta gabata da kuma aya ta karshe a suratul Hajj wacce take nuna sauki da rashin kunci a addinin musulunci.
Allah ne mafi sani.
*_Dr. Jamilu Zarewa_*
27/06/2018
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

0 comments:
Post a Comment