Fitowa ta 17
2. WASICI
Ga wasicin Sarkin Musulmi Umaru dan Khaddabi da ya yi ma Sa'idu dan Wahabi, lokacin da ya nada shi Gwamna. Yace,
"Ya kai Sa'adu! Na shugabantar da kai a kasar Iraki. To, ka kiyaye wasiyyata. Kar ka rudu da cewa kai kawun Annabi ne, ko kai sahabinsa ne. Ka sani mummunan aiki ba ya wanke wani mummuna irin sa. Aiki na gari shi ne yake wanke mummuna. Ka sani Allah ba shi da zumunta tsakanin sa da bayinsa in ba ta bin sa ba. Ka ga mutane, mai darajarsu, da kaskantaccensu, wurin Allah duk daya ne. Shi Ubangijinsa ne, su kuwa bayinsa ne. Ka dubi al'amarin da ka ga Annabi yana a kan sa, tun ranar da aka aiko shi har ya zuwa rabon sa da mu, ka lazimce shi. Ka saba ma kanka da wanda ke tare da kai alheri, da shi za ka fara. Ka sani tsoron Allah yana cikin abu biyu ne; bin umurninsa da barin sabon sa. To, Allah ya kiyaye ka".
Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi
Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
22/10/1438
16/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
0 comments:
Post a Comment