DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 12
56. Babbar alamar girman kai ita ce ka raina mutane ko ka ki karbar gaskiya. "Mutakabbari ba ya shiga aljanna.
57. Ba kowace faduwa ce matsala ba. Da yawa wanda zai fadi amma idan ya tashi ya sheka ba ka iya cim ma sa.
58. Idan ka saka kudi a account ko ka cire kana samun alert na abin da ya rage ko ya karu a cikin jarinka. Ina ma ace duk lokacin da ka yi karya ko sata ko ka ci naman dan uwanka za ka samu alert na yawan zunubinka? Ko kuma idan ka yi sallah ko azumi ko sadaka za ka samu alert na yawan ladar da ake ba ka? A kullum ka aikata sabo ko da'a haka tana faruwa, amma Mala'iku ne suke lissafa ma ka suna rubutawa, kuma, za su hada rasitinka gaba daya a ba ka gobe kiyama, a buga total, a fitar da sakamako, sannan a yanke hukunc. Allah ka sa mu shiga aljanna.
59. Kada ka cuci wanda ya cuce ka. Sharri kare ne, ko ya yi nisa sai ya dawo ma mai-shi.
60. Abu mafi sauki wajen tunkude cuta shi ne ka manta da an cuce ka.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
17/10/1438
11/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment