DUNIYA MAKARANTA
Fitowa ta 18
86. Mace ta gari tana neman yardar Allah da biyan bukatar mijinta. A gidanta ba kazanta, a jikinta ba cuta, a waje ba a jin muryarta. Daga nesa idan ka hango ta ba ka gane ta saboda kamalar suturarta da kwarjinin hijabinta. Muguwar mace ita ce mai yawan kiran ciwo, mai gajiyar hakuri, mai kaushin magana, mai dogon harshe, mai kukan karya, mai tona asirin gida.
87. Mutum yakan kosa da kuruciya, amma idan ya girma zai dawo yana begen ta. Yana karar da lafiyarsa wajen neman kudi sannan ya sa kudi yana neman ta.
88. Wahaltattun mutane a duniya su biyu ne: Wanda Allah ya kawo lokacin abu ya ce ba za ayi shi ba, da wanda Allah bai kawo lokacin abu ba ya ce sai an yi shi. Ka yarda da hukuncin Allah, shi ne zaman lafiya a gare ka.
89. Babbar hasara a lahira ita ce ka samu ladarka a cikin littafin wani, ko ka samu zunubin wani a cikin littafinka. Kada ka zalunci mutane. Kada ka shiga cikin hakkinsu. Idan ka yi haka za su washe ladarka ko su lafta ma ka zunubinsu.
90. Masoyinka she ne wanda yake kare ka idan aka aibata ka. Makiyinka a kullum fatar ya ke yi ka tozarta.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
23/10/1438
17/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743

0 comments:
Post a Comment