A kowace safiya dan adam yana haduwa da bala'i guda 3 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 10 July 2017

A kowace safiya dan adam yana haduwa da bala'i guda 3

A KOWACE SAFIYA DAN ADAM YANA HADUWA DA BALA'I GUDA UKKU

         Na farko 1

Shekarunsa suna raguwa amma baya tuhumar kansa akan haka.
Idan kudinsa ya ragu zai tuhuma bayan kudi yana dawowa amma shekaru basa dawowa.

        Na biyu 2

kullum yana cin arzikin Allah in Halal yaci za'a tambaye shi in Haram ne za'a yi masa azaba akai bai san karshen hisabin mai zai kasanceba.

      Na uku 3

kullun yana kusantar Lahira yana nisantar Duniya amma duk da haka baya damuwa da Lahira kamar yadda yadamu da Duniya,
Bai san makomarsa ba shin lAjannace ko Wutace.

  Gaskiya

 (Babu abunda zai amfaneka sai sallarka).

wanda yabar karatun Alqur,ani tsawon kwana uku ba tare da uzuri ba sunansa maqauraci (wanda ya qauracewa Alqur,ani kenan).

  Duniya kwana 3 ce
   
 Jiya: munganta ba zata dawo ba,

Yau: muna cikinta ba zata dauwama ba zata wuce,

Gobe: bamusan ina zamu kasanceba.

Ka gaisa da mutane, kayimusu afuwa kayi Sadaka domin Ni da kai da Su duk matafiya ne. Bissalam.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support