Naji wani malami yace duk macen da tayi sallah kafarta a waje shirme tayi shin yaya abin yake ?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 10 July 2017

Naji wani malami yace duk macen da tayi sallah kafarta a waje shirme tayi shin yaya abin yake ??

*Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 2,399*
..
Naji wani malami yace duk macen da tayi sallah kafarta a waje shirme tayi shin yaya abin yake??

……

Amsa


_To wannan wata fahimtace ta malamai, wacce kuma takeda qarfi sosai, dominkuwa yana daga cikin al'amura na wajibi shine mace ta rufe qafarta walau a cikin sallah ko a wajen sallah, wannan wajabcin yasa wasu daga cikin malamai sukeda fahimtar cewa duk matarda tayi sallah qafarta a bude batada sallah****_
        _Ammadai wasu daga cikin malamai suna ganin cewa sallarta tayi sedai cikakken ladar sallarne batadashi, da wannan yasa muke cewa lallaifa mata suyi taka tsantsan gameda sallarda sukeyi basa lullu6e qafarsu dankuwa suna cikin hatsarin yin aikin banza, kodai aqi kar6an sallar tasu baki dayanta kokuma suyita amma babu lada, domin kuwa qafar mace al'aurace alokacinda take sallah****_


Allah yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس التعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-152200029806Y7561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support