Fitowa ta 30
151. Wanda fuskar mata take ba shi sha'awa mata daya ba ta isar sa. Amma wanda kyakkyawan hali yake so daya ma sai ishe shi.
152. Idan kana cikin damuwa ka jira samun sauki daga wurin Allah, wannan jiran da kake yi ibada ne. Domin kyautata zato ne ga Allah. Wanda ya kyautata ma Allah zato kuwa lallai ne Allah zai ishe shi.
153. Duk lokacin da fitila ta yi sama haskenta ya fi yaduwa. Idan Allah ya daukaka ka, yi kokari ka zamo fitila mai kawar da duhu da damuwa daga mutane.
154. Urwatu bn Zubair, ya gamu da jarrabawar ciwon Cancer a kafarsa. Da magani ya gagara sai aka yanke shawara akan cire masa kafar ga baki daya. Amma a wannan dare bai fasa karanta abin da ya saba yi na Alkur'ani da Zikiran Ubangiji ba. Duhu gani, sau nawa ne karamar matsala ta durkushe ka daga ibada?
155. Kyawon hankali ya rika tunani. Kyawon harshe ya rika faadin gaskiya. Kyawon budurwa kunya. Kyawon Yaro biyayya.
Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto
5/11/1438
29/7/2017
» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
0 comments:
Post a Comment