TARIHIN MATAYEN GIDAN ANNABI (SAWW) - KASHI NA BIYU ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday, 29 December 2017

TARIHIN MATAYEN GIDAN ANNABI (SAWW) - KASHI NA BIYU

TARIHIN MATAYEN GIDAN ANNABI (SAWW) - KASHI NA BIYU.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Salati da amincin Allah da albarkokinsa da rahamarsa su tabbata bisa Babban Masoyin Ubangijin Talikai. Annabin da Ubangijinsa ya tsarkake Garinsa da Nasabarsa da iyalan gidansa da Matayensa

Salatin ya hada da Sahabbansa da dukkan alayensa da mabiyansa har zuwa ranar da Qasa zata fitar da nauye-nauyen da take dauke dashi.

Idan Daliban ZAUREN FIQHU suna biye damu, awancan darasin mun kawo tarihin Babbar Uwargidan Manzon Allah (saww) wato Nana Khadeejah bintu Khuwailid (rta).

Yau kuma in sha Allah zamu dora da tarihin wacce take biye da ita wajen Shigowa wannan gidan Mai Albarka. wato Sayyidah Saudah (yardar Allah ta tabbata gareta).

NANA SAUDATU (RTA)

SUNANTA DA NASABARTA
*****************************
Nana Saudah (rta) ita ce mace ta farko wacce Ma'iki (saww) ya aura bayan rasuwar Nana Khadeejah (ra). Kuma nasabarta ita ce kamar haka :

Mahaifinta : Sunansa Zam'atu bn Qays, 'dan Abdu Shamsi, 'dan Abdu Wadd,  'dan Aamiru, 'dan Lu'ayyu 'dan Ghalibu.

Wato nasabarta ta hadu da ta Manzon Allah (saww) akan Kakansa Lu'ayyu bn Ghaalib.

MAHAIFIYARTA : Sunanta Ash-Shamoos bintu Qays bn Zayd. 'Yar Qabilar Banun Najjar ce daga garin Madina.

Wato Mahaifiyarta tana da kusancin nasaba da dangin Mahaifiyar Abdul Muttalib (Kakan Manzon Allah saww).

Nana Saudah tana daga cikin mata masu alfarma da girman Nasaba acikin Quraishawa. Kamar yadda Imam Zahabiy ya fada acikin littafinsa na tarihi.

Babban Malamin Tarihin Musuluncin nan wato Ibnu Sa'ad yace : Saudatu bintu Zam'ah da ita da Mijinta As-Sukraan bn 'Amru (ra) - 'dan Uwan babban Sahabin nan Suhaylu bn Amru (ra) suna daga cikin mutanen da suka fara karbar Musulunci. Kuma daga baya sukayi hijira tare zuwa Qasar Habasha.

(Aduba Tabaqat Alkubra na Ibnu Sa'ad, Juzu'i na takwas, Shafi na 57).

HIJIRARTA ZUWA HABASHA
*******************************
Kasancewar Nana Saudah tana daga cikin farko farkon shiga Musulunci, da ita da sauran Sahabban Manzon Allah (saww) sun fuskanci Tsanantawa da wulakantawa da chutarwa mai tsanani daga Kafiran Makkah.

Yayin da chutarwar ta tsananta, Sai Manzon Allah (saww) ya basu Umurnin cewa suyi hijira zuwa Qasar Habasha har sai abubuwa sun daidaita. Domin kuwa Sarkin Qasar yana da adalci kuma ba ya yarda da duk wani zalunci.

Don haka wasu daga cikin Sahabban sukayi Hijira zuwa chan Qasar Habasha din. Wasu sun tafi tare da iyalansu, wasu kuma su kadai suka tafi.

To ita Nana Saudah tayi hijirar tare da Mijinta As-Sukraan bn Amru tare da wasu mutum takwas daga Banu 'Amru.

Saboda Qarfin imani irin nata tun alokacin, ta kyale dukiyarta da iyayenta da dukkan abinda ta mallaka, ta tafi domin tseratar da Imaninta. Hakanan Allah yake jarrabar bayinsa Muminai domin ya Qarfafa imaninsu.

Suna chan suna zaune cikin aminci a Qasar Habasha, sai wani labari marar tushe ya iskesu cewar wai yanzu komai yayi kyau agarin Makkah, kafiran sun dena chutar da Muminai.

Jin haka yasa wasu da dama daga cikin masu hijirar suka dauko hanya suka dawo gida.

Suna shigowa garin Makkah sai suka tarar ashe labarin nan da aka basu ba haka abin yake ba.

Nan take suka fara fuskantar matsaloli fiye da da. Kuma kafiran suka Qara Qaimi wajen tsananta musu.

Shi kuwa Mijin Nana Saudatu tun akan hanyar dawowa gida ya kamu da rashin lafiya. Don haka basu jima sosai da komowa ba, sai Allah ya karbi ransa (Allah shi Qara masa yarda).

Shi kuma Manzon Allah (saww) babu dadewa Matarsa wacce yake ji da ita, wato Nana Khadeejah bintu Khuwaylid (ra) ta rasu. Acikin shekara guda tare da baffansa Abu Talib.

Wannan rasuwar tasu ta zamo babbar abin bakin ciki sosai agareshi. Domin kuwa Abu Talib shine yake kareshi daga maganganun da kafiran suka gaya masa. Kuma sun kasa tasowa gadan-gadan domin dukansa ko Kasheshi saboda albarkacin suna ganin girman Abu Talib din.

Ita kuma Nana Khadeejah ita ke kwantar masa da hankali duk lokacin da ya shiga cikin damuwa. Kuma tana Qarfafarsa akan duk abinda zai gudanar.

Saboda hakane su kansu Sahabbansa maza da Mata suka rika tayashi bakin cikin wadannan rasuwar.

Watarana Manzon Allah (saww) yana zaune sai ga wata daga cikin Mataye Sahabbai tazo wajensa. Sunanta Khaulatu bintu Hakeem (Matar Uthman bn Maz'un rta).

Tace masa "Ya Rasulallahi lallai kana cikin damuwa game da mutuwar Khadeejah".

Yace mata "Kwarai kuwa. Ita ce Mahaifiyar 'Ya'yana, kuma Uwargidan wannan gidan".

Sai tace "Ya Rasulallahi ko zaka yi aure?

Sai yace "Wa zan aura?".

Sai tace "Akwai Budurwa, akwai kuma Bazawara, Sai wacce kake so".

Sai yace "Shin wacece Budurwar?". Sai tace "A'ishatu bintu Abubakrin, 'Yar mafi soyuwar Mutane agareka".

Sai yace "To wacece Bazawarar?". Sai tace "Saudatu bintu Zam'ah.  Wacce tayi imani da Manzancinka, kuma tana bin Umurninka".

Daga nan sai Ma'aiki (saww) yayi farinciki  kuma yayi mata izinin taje ta nema masa duk guda biyun.

Da farko ta shiga ta gidan Sayyiduna Abubakrin, sannan ta fito ta nufi gidan su Saudah (ra).

Ta shiga wajen Saudah tayi mata albishir tana cewa : "Hakika Ubangiji ya sanya albarkarsa da falalarsa agareki Ya ke Saudatu!".

Sai Nana Saudah tace "Menene ya faru?" sai tace "Ai Manzon Allah ne (saww) ya turoni domin in gaya miki yana so zai aureki".

Daga jin wannan sai murna ta lullubeta, tace ma Khaulah "Kije wajen Mahaifina ki shaida masa".

Anan zamu tsaya, sai a darasi na uku zamu ci gaba in sha Allahu. Da fatan ALLAH shi albarkaci dukkan daliban Zauren Fiqhu, Allah ya saka ma kowa da alkhairi. Allah shi bamu ikon koyi da magabatanmu na kwarai.

An gudanar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3) Ranar Juma'a 12 ga November 2015.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support