Amfanin zakka da sadaka a rayuwar bawa musulmi. ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 25 July 2017

Amfanin zakka da sadaka a rayuwar bawa musulmi.

*AMFANIN ZAKKA DA SADAKA A RAYUWAR BAWA MUSULMI*

✍🏼Rubutawa: *_Dr Aliyu Muhammad Sani, Hafizahullah_*

Daga cikin amfani da fa'idojin Zakka, tana tsarkake mai bayar da ita, kuma tana kara masa imani, kuma tana tsarkake dukiyar tasa, kuma tana karata ta bunkasata, kuma tana amfanar da wanda aka ba shi ita.

1. Amma tsarkakewa da take yi wa shi mai bayar da ita, lallai tana tsarkake halayensa, tana tsarkake shi daga kwadayi da rowa, da munanan halaye da da biyu. Kuma tana bunkasa halayensa, sai ya siffantu da siffofin masu karamci da kyauta da yin alheri wa mutane, kuma masu godiya ma Allah a kan abin da ya yi musu na arziki da ni'imomi, saboda ba da Zakka yana daga cikin manyan aiyukan godiya ma Allah, ita kuwa godiya ma Allah a kullum tana tare da samun kari daga wajensa.

Kuma Zakkar tana bunkasa ladansa da sakamakonsa a wajen Allah, saboda Zakka da ciyar da dukiya ana ninka ladansu ninki masu yawa, gorgodon imanin wanda ya bayar da ita da Ikhlasinsa, da kuma amfaninta da ajiyeta a muhallinta (nau'in mutane takwas (8) wadanda ake ba su Zakka).

Kuma Zakka tana fadada zuciya, ta faranta rai, kuma tana kare wa bawa bala'o'i da cutuka masu yawa.

Kuma Zakka da Sadaka suna kulla soyayya a tsakanin Musulmi, suna gusar da gaba da kiyayya a tsakaninsu, su mai da su, su zama 'yan uwa abokan juna, saboda dabi'a ce ta zukata son wanda ya kyautata mata, wannan zai sa a samu hadin kai a tsakanin musulmai su zama al'umma guda daya a kan Addinin Allah, masoya juna.

Kuma Zakka da kyauta suna sa wadanda aka ba su su yi addu'o'in da Allah yake amsawa ma wadanda suka bayar da ita.

2. Sannan kuma Zakka tana bunkasa dukiyar da aka fitar da ita daga gare ta, tana kare ta daga masifa da bala'i, kuma tana janyo mata albarka, kamar yadda Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, Ya ce:

*_"Sadaka ba ta tauye dukiya, a'a, tana karata ne"._*

Allah Ya ce:

{وَمَا أَنْفَقْتُمْ مِنْ شَيْءٍ فَهُوَ يُخْلِفُهُ وَهُوَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ} [سبأ: 39]

*_"Duk wani abu da kuka ciyar, to Allah Zai maye muku gurbinsa, kuma shi ne fiyayyen masu arzurtawa"._*

 3. Amma amfanin Zakka ga wanda aka ba shi ita, lallai Allah Ya yi umurnin a bayar da ita ne ga mabukata, daga fakirai, da miskinai da wadanda ake bi bashi, da kuma bayar da ita don 'yanta bayi, da kuma bayar da ita don gudanar da maslahohin da musulmai suke bukatansu, don haka duk lokacin da aka ajiye Zakkar a muhallinta, aka bayar da ita ga wanda ya dace, to za a biya masu bukatunsu da yaye musu laruran da suke ciki, fakirai za su wadata ko talaucinsu zai ragu, kuma za a samu daman gudanar da aiyuka na maslahar al'umma gaba daya.

Inda a ce, mawadata da masu arziki za su fitar da Zakkan dukiyoyinsu ta fiskar da aka shar'anta, a bayar da ita ga wanda Allah Ya yi umurni, da an cimma maslahohin Addini da na duniya masu yawan gaske, da an kawar da talauci ko an rage shi, da an magance sharri masu yawa, na zaman banza da rashin aikin yi, da sace – sace da fashi da makami, da ha'inci da satar dukiyar al'umma, da an samu ci gaban tattalin arziki a cikin al'ummar musulmi.

Wannan ne fa ya sa Zakka ta zama daga cikin manyan abubuwan da suke nuna kyawun Shari'ar Muslunci, saboda abin da ta kunsa na janyo maslahohi da amfani wa mutane da kawar da barna da abin da zai cutar da su.

Daga littafin Sheikh Ibnu Sa'adiy, Rahimahullah: Al- Riyadhun Nadhirah.

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support