DUNIYAR ALJANU DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (DARASI NA DAYA)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Dawwamammun Salatai da Wanzanzun Tasleemi su tabbata bisa Manzon da aka turo zuwa ga Aljanu da mutane da Mala'iku baki daya, Shugabanmu Annabi Muhammadu, tare da iyalan gidansa tsarkaka mahaskaka, da kuma Sahabbansa Yardaddu madaukaka.
DUNIYAR ALJANU
*******************
Wannan shine darasi na farko acikin wannan Maudhu'i na musamman, mai suna Duniyar Aljanu.
Acikin wannan darasin Insha Allahu zamu rika shiga cikin duniyar Aljanu ne domin mu ga yadda suke rayuwa, da abincin da suke ci, da nau'in halittunsa, da mazaunansu, da kuma alakarsu da Bil-Adama.
Kuma zamu tsamo gaba dayan karatun ne daga cikin abubuwan da ALQUR'ANI mai girma ya bamu labari game dasu, da kuma hadisai ingantattu, da labarai tabbatattu daga Magabata na kwarai.
Allah nake roko ya sanya min Ikhlasi da kuma dacewa da samun yardarsa acikin dukkan abinda zamu karanta.
SHIN DA GASKE NE AKWAI ALJANU??
Eh da gaske akwai su. Wanda yayi Jayayya akan samuwarsu ma ya kafirta. Tunda Allah da kansa ya fadesu acikin Alqur'ani agurare da dama.
Allah (SWT) yana cewa :
"(YA MUHAMMAD) KACE (MUSU) "ANYI MUN WAHAYI CEWA WASU JAMA'A DAGA CIKIN ALJANU SUN NEMI SAURARON (KARATUN WANNAN ALQUR'ANI) SAI SUKA CE HAKIKA MU MUNJI WANI ABIN KARANTAWA MAI BAN-MAMAKI.
"YANA SHIRYARWA ZUWA GA HANYAR SHIRIYA SAI MUKAYI IMANI DASHI"
(suratul Jinni ayah ta 1 zuwa ta 2).
YAUSHE NE AKA HALICCESU??
Abu Huzaifa - Is'haq bn Bishr Alqurashiy ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Amru bn Al-aas (ra) yana cewa:
Allah ya halicci Banul-Jaanni (aljanu) ne gabannin halittar Annabi Adam (as) da shekaru dubu biyu.
Imam Dhahhak (rah) ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) yana cewa:
"Aljannu sun kasance mazaunan doron Qasa, Mala'iku kuma mazaunan sararin samaniya. Su suke zaune cikinta.
Akowacce sama daga cikin sammai din nan akwai Mala'iku kuma kowanne suna da irin Salloli da Tasbeehin da suke yima Allah.
Mala'ikun dake cikin kowacce sama sunfi wadanda ke Qasa dasu tsananin yawaita sallah da Tasbeehi. Su kuma Aljanu suna zaune adoron Qasa".
Bisa dukkan hujjoji dai an halicci Aljanu ne tun kafin halittar 'Dan Adam. Kamar yadda Allah da kansa ya fada acikin Alqur'ani.
Bayan ya fadi halittar 'Yan Adam, sai yace : "SU KUMA ALJANU MUN HALICCESU NE TUN FARKO DAGA HARSHEN WUTA MAI HURUWA".
Kakan Aljanu sunansa SUMIYAA. Amma acikin littafinsa mai suna LAQDUL MARJAN Imam Suyutiy yace sunansa SAMOOM. Burhanul Halbiy kuma yace sunansa SHUMIYAA'.
Ikramatu ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) cewa:
"Yayin da Allah ya halicci Sumiyaa kakan Aljanu, ya halicceshi ne daga Harshen wuta. sai yace masa: "MAI KAKE BURI? ".
Sai yace "Ina burin mu rika ganin sauran halittu amma su kar su ganmu, sannan abamu ikon nutsewa acikin Qasa, sannan Tsofaffin cikinmu arika dawo da halittarsu Kamar Yara matasa".
Sai Allah ya basu wannan baiwar. Sun kasance suna ganin mutane amma su ba'a ganinsu. Kuma idan suka mutu suna 'bacewa ne acikin Qasa. Kuma Tsofaffin cikinsu akan dawo musu da halittar jikinsu kamar jarirai, suci gaba da rayuwa har zuwa lokacin da ajalinsu zai yi".
Is'haq Ibnu Raahawayhi yace: "Yayin da Allah ya halicci Aljanu, ya umurcesu da su Zauna adoron Qasa. Sun kasance suna zaune suna bauta ma Allah tsawon lokaci. Har suka sa'ba ma Allah, suka fara zub da Jini.
Acikinsu akwai wani Sarki ana ce dashi Yusufa sai suka kasheshi. Saboda haka Allah ya tura musu rundunar Mala'ikun sama ta-daya. Su dubu hudu. Suka koresu daga doron Qasa.
Wadanda suka ragu daga cikinsu, aka korasu zuwa ga Tsibirai da dazuzzukan da suke kewaye da duniya.
Iblees yana tare da wadannan Mala'ikun da suka kori Banul-Jaanni don haka yaci gaba da zama adoron Qasa yana ta ibada.
Imam Mujahid yace "Iblees Allah ya mallaka masa mulkin Saman duniya da kuma doron Qasa.
Kuma tuntuni ya karanta acikin wani rubutaccen littafi awajen Ubangiji cewa Allah zai sanya wani Khalifa adoron Qasa, kuma wannan Khalifan zuriyarsa zaau zubar da jini, kuma zasuyi zunubi abayan Qasa.
Don haka iblees sai ya bama Mala'iku labarin abinda ya karanta. Kuma ya gaya musu cewa hakika wannan Khalifan da Allah zai halitta, zai sanya Mala'ikunsa suyi masa Sujjada. Amma shi ya riga ya kudurce cikin ransa cewa har abada ba zai yarda yayi wannan sujjadar ba.
Shi yasa lokacin da Ubangiji (azza wa jalla) yace ma Mala'ikunsa "HAKIKA NI ZAN SANYA KHALIFA ADORON QASA".
Sai suka tuno da waccan maganar da Iblees ya basu labari. Don haka ne sai suka ce
"SHIN YANZU ACIKINTA ZAKA SANYA WADANDA ZASUYI 'BARNA ACIKINTA KUMA SU ZUBAR DA JINI?".
Awata ruwayar kuma daga Muqaatil, daga Abdullahi bn Abbas (ra) yace su Mala'iku yayin da Allah ya gaya musu cewar zai sanya Khalifa adoron Qasa, sun tuno da irin Fasadin da Banul Janni sukayi adoron Qasar ne. Shi yasa sukayi wannan tambayar ga Ubangiji (SWT).
Insha Allahu akaratu na gaba zamuyi bayanin yadda yanayin halittar jikinsu da kamanninsu yake.
Salati da tasleemi bisa Annabin Mutane da Aljanu, tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa madaukaka.
DAGA ZAUREN FIQHU

0 comments:
Post a Comment