Masu hikima sunce ?? ( fitowa ta 20) dr.mansur ibrahim sokoto ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 19 July 2017

Masu hikima sunce ?? ( fitowa ta 20) dr.mansur ibrahim sokoto

MASU HIKIMA SUN CE

Fitowa ta 20

91. Idan kai mai yawan fadace-fadace ne, in ba ka cuci masu daraja ba, ashararai za su cuce ka.

92. Al'amarin da ba ka iya shi ba, ka rabu da shi, ka wuce shi zuwa wanda ka iya.

93. Mai ba da amana ga maciyin amana kamar mai daukar kayansa na alfarma ne ya ajiye su wuri mai yawan Zago.

94. Ilimi yakan daukaka kaskantance kamar yadda jahili kan kaskanta madaukaki.

95. Gabas da yamma, kudu da arewa, duk wanda ya yi abota da kai abinka yake so.

Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi

Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

25/10/1438
19/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support