Tarihin muazu bn jabal (R A) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday 10 July 2017

Tarihin muazu bn jabal (R A)

*SAYYIDINA MU'AZU BN JABAL (R) SARKIN MALAMAI NA FARKO A MUSULUNCI KUMA SARKIN MALAMAI A LAHIRA:*

Rubutun Dr. Mansur Sokoto
15 ga Shawwal, 1438H
9 ga Yuli 2017

*Mu'azu bn Jabal Radhiyallahu Anhu (Sarkin Malamai duniya da Lahira):*

*SUNANSA*: Mu'azu bn Jabal bn Amr bn Aus Al-Khazraji Al-Ansari.

*SIFFARSA*:
Mutum ne dogo, fari, mai manyan idanu, da wushirya, mai kyakkyawan gashi.  Yana da kwarjini matuka da cika fuska. Sahabbai sun kasance suna sifaita shi da Annabi Ibrahim (AS).

*HALAYENSA*:
Mutum ne mai tsentseni da adalci da bin gaskiya. Mai yawan kyauta ne, dalilin da ya sa ya ci bashi mai yawa don kyautata ma mutane har sai da bashi ya taru a kan sa, sai ya sayar da babbar gonarsa ya biya kowa da kowa. A lokacin Jihadi kuma sadda ake samun kudi sosai yakan yi sadaka da duk abinda ya samu har ya dawo babu ko taro a gidansa.
Yana wa'azi mai matukar ratsa jiki da sanya mutane kuka.
Daga cikin adalcinsa: Yana da mata biyu, amma a ranar daya ba ya shan ruwa ko ya yi alwala a gidan dayar. Allah ya yi matansa cikawa a rana daya a cikin annobar da aka taba yi mai suna "Amwás" a kasar Sham. Aka haka masu rami daya, amma sai da ya yi masu kuri'a akan wace za a fara sanyawa a gaba.

*MUSULUNTARSA*:
Ya musulunta yana dan shekaru 18 - kafin Gemu ya fara fito masa - a cikin mutanen nan 70 da suka zo Aikin Hajji daga Madina, suka karbi da'awar Manzon Allah (S) kuma ya yi mitin da su a wurin Jamratul Aqaba a tsakiyar dare cikin matsanantan matakan tsaro. Manzon Allah (S) ya shata masu yadda za su kai Musulunci a Madina, da yadda zai bar Makka ya koma can.

*JIHADINSA:*
Ya halarci duk yakokin da Manzon Allah (S) ya yi - a matsayin soja - tun daga Badar har na karshe in ban da yakin Hunain, saboda a  lokacin Manzon Allah ya zaunar da shi ne a Makka don ya karantar da mutane bayan bude ta da aka yi.
Bayan ya Musulunta shi ne ya kakkarya gumakan Kabilar Banu Salamata.
Ya halarci yakokin da aka yi aka buda biranen Sham, da kuma fitaccen yakin nan na Yarmuk a zamanin Halifa Umar dan Haddabi (R).
A lokacin da mutuwa ta cimma Abu Ubaida (R) ya nada Mu'azu bn Jabal kwamanda a madadinsa. A wannan matsayin ne ajalinsa ya cim masa.

*WASU DAGA DARAJOJINSA:*
Yana da darajoji masu yawa, abinda ya sa Imam Al-Bukhari ya ware masa Babi a kan falalarsa a cikin Kitabu Manaqib Al-Ansar a Sahihin littafinsa. Ga wasu daga darajojinsa:
1. Manzon Allah (S) ya goya shi a kan dabba sun yi tafiya a tare.
2. Manzon Allah (S) ya rika hannunsa ya ce masa, Ya Mu'azu! Wallahi ina kaunar ka. Sai ya ce, ya Manzon Allah! Wallahi ni ma ina kaunar ka. Sannan ya ce, ya Mu'azu! Akwai wata wasiyya da nake son in yi maka: Ka rika fadin - a bayan kowace sallah - "Ya Allah! Ka taimake ni a kan ambatonka da gode maka, da kyautata bautar ka.
3. Manzon Allah (S) ya raka shi a kasa, shi kuma yana kan doki a lokacin da ya nada shi Gwamna ya tura shi zuwa Yaman. Sai Annabi (S) ya yi masa tattaki zuwa bayan birni, in da suka yi bankwana, Annabi ya yi masa addu'a yana cewa: "Allah ya kare ka ta gabanka da ta bayanka, ya tsare ka daga sharrin mutum da aljani". Sannan ya ce, masa "Da wuya ka same ni da rayuwata idan ka dawo". Mu'azu ya kama hanya yana kuka, tafiyar da bai dawo ba sai a zamanin Halifa Abubakar.
4. Yana cikin Alarammomi hudu da Manzon Allah (S) ya ba su shaida, kuma ya ce a koyi Alkur'ani daga wurin su. Su ne: Abdullahi bn Mas'ud da Salim maulan Abu Huzaifa da Ubayyu bn Ka'ab da Mu'azu bn Jabal.
5.Yana cikin masu Fuqaha'u masu ba da Fatawa su shida wadanda Manzon Allah ya ba su izni suna fatawa a zamaninsa; uku Muhajirai ne: Umar da Usman da Ali, uku kuma Ansarai: Ubayyu da Zaidu da Mu'azu kamar yadda Sahabi Sahlu bn Abi Hathmata ya bayyana.
5. Yana cikin mutane biyar da Manzon Allah (S) ya ce mutanen kirki ne. Sun hada da Sayyidina Abubakar da Umar da Mu'azu bn Amr bn Al-Jamuh da Mu'azu bn Jabal da Abu Ubaida.
6. Manzon Allah (S) ya ba shi shaidar sanin ilimin Fiqihu fiye da duk Sahabbai. Kamar yadda Anas (R) ya rawaito cewa, Annabi (S) ya ce:
"أرحم أمتي بأمتي أبو بكر، وأشدهم في الله عمر، وأصدقهم حياء عثمان، وأقرؤهم لكتاب الله أبيّ بن كعب، وأفرضهم زيد بن ثابت، وأعلمهم بالحلال والحرام معاذ بن جبل، ألا وإن لكل أمة أمينًا، وأمين هذة الأمة أبو عبيدة بن الجراح".
"A cikin al'ummata wanda ya fi kowa tausayin al'ummar shi ne Abubakar, wanda ya fi tsanani wajen kariyar hakken Allah shi ne Umar, wanda ya fi kunya da gaske shi ne Usman, wanda ya fi su kwarewa a karatun Alkur'ani shi ne Ubayyu bn Ka'ab, wanda ya fi su iya rabon gado shi ne Zaid bn Thabit, wanda ya fi su sanin Halal da Haram shi ne Mu'azu bn Jabal. Ku saurara! Kowace al'umma tana da amintacce. Amintaccen wannan al'umma shi ne Abu Ubaida bn Jarrah".
Wannan ya nuna cewa, Mu'azu bn Jabal shi ne Sarkin Malamai a zamanin Manzon  Allah (S).
7. Manzon Allah (S) ya fadi cewa: Za a tayar da Mu'azu bn Jabal yana a gaban Malamai da tazara. (Ma'ana shi ne, Sarkin Malaman kuma a lahira kenan).

*MUKAMAI DA YA RIKE:*
Annabi (S) ya nada Mu'azu a mukamai daban daban. Kuma ya ba shi shaida a kan abubuwa da dama.
Daga cikin mukaman da ya rike a zamanin Manzon Allah (S) har da Limanci, da Jakadanci, da karbar Zakka, da jagorancin Jihadi da kuma mukamin Gwamna a garuruwa biyu daban daban a kuma lokuta daban daban. Sannan ya ba shi izinin yin fatawa. Ya kuma yi masa ijazar karantar da Alkur'ani shi da wasu Sahabbai guda uku kamar yadda ya gabata.
Da aka buda birnin Makka sai Annabi ya nada Attab bn Usaid a matsayin Gwamna, ya zaunar da Mu'azu bn Jabal shi kuma ya karantar da mutane Alkur'ani da ilimin Fiqhu kamar yadda Ibnu Sa'ad ya riwaito ta hanyar Mujahid bn Jabr.
Ko da Manzon Allah (S) ya cika Mu'azu yana Gwamna.
A bayan zamanin Manzon Allah (S) Halifofi biyu da ya yi zamani da su: Abubakar da Umar (R) sun ci gaba da gabatar da shi a cikin sha'anoni da dama. Amma a zamanin Halifa Umar, bayan shigar sa a cikin sha'anin jihadi ya fi karfi a bangaren Fatawa. Domin yana cikin wadanda Sayyidina Umar (R) ba ya yanke hukunci sai ya tuntube su. Haka kuma ya rika mukamin Alkali a wannan zamanin.
Sayyidina Umar (R) yana jinjina masa matuka a sanin ilimin Fiqihu. Don ya taba yin huduba a cikin ta ya ce:
"من أراد الفقه فليأت معاذا"
"Duk wanda ke son karatun Fiqihu ya je wajen Mu'azu bn Jabal.
Kafin haka, lokacin da Sayyidina Abubakar ya tura shi Jihadi a yankin Sham Sayyidina Umar ya ba da shawarar a janye shi saboda amfanin sa wajen ilmantar da mutane. Amma da ya nuna yana sha'awa sai Sayyidina Abubakar ya ce, a bar shi ya je watakila Allah zai ba shi shahada. Sayyidina Umar (R) ya ce, to ai ko a gida ana iya samun shahada. Ya dai tafi din, kuma ya samu shahada daga bisani amma ba a wurin yaki ba kamar yadda za mu gani.
Don haka, duk wanda ya ce Sayyidina Mu'azu bai san Fikihu ba ya yi kuskure babba, kuma ya wautar da Manzon Allah (S) da halifofinsa.

*CIKAWARSA:*
Mu'azu bn Jabal (R) ya cika a yankin Jordan na kasar Sham yana matashi bai wuce shekaru 32 ba. Ya rasu a cikin Annobar nan ta Amwas wadda ta ci dubun dubatar bayin Allah; Sahabbai da Tabi'ai, bayan ta kashe matansa da yayansa maza da mata yana mai hakuri da mayar da lamari ga Allah a shekara ta 18H. Ya cika yana fadin cewa: "Ya Allah ka yi mani yadda kake so. Na rantse da girman ka, ka san ina son ka".
Allah ya kara yarda da shi, ya saka masa da alheri bisa jihadinsa da karantarwarsa, ya sa mu zama cikin masu bin sawunsa tare da sauran Malaman Sunnah zuwa gidan aljanna.

Mai neman karin bayani game da Rayuwa, Matsayi da Darajojin wannan bawan Allah sai ya duba:
- Sahihul Bukhari
- Sahihu Muslim
- Al-Isaba fi Tamyiz As-Sahaba
- At-Tabaqat Al-Kubra na Ibn Sa'ad
- Siyar A'lám An-Nubala
- Usd Al-Gába
Da sauran littattafan Tarihi.

*_Alhamdu lillah._*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support