Duniya makaranta !! (fitowa ta 16) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday 15 July 2017

Duniya makaranta !! (fitowa ta 16)

DUNIYA MAKARANTA

Fitowa ta 16

76. Rinjayar mai karfi ba shi ne gwaninta ba. Gwani shi ne wanda ya iya bakinsa, ya rinjayi zuciyarsa, sannan ya ji tausayin na karkashinsa.

77. Idan ka ga tururuwa ka dage kafarka don kar ka take, ta za ka ga gamu da rahamar Allah don ka ji tausayin wata halitta daga cikin halittunsa. To ya ya ka ke ji idan ka tausaya ma dan Adammai daraja a wurin Allah? Ina kuma ace wanda ka tausaya ma musulmi ne mai fuskantar gabas ya yi sallah?

78. Zunubi da sabon Allah suna cike da shu'umci.mn sukan sa ka da-na-sani, ko su ja maka hasara, ko su hana ka riba, ko su mantar da kai wani alheri, ko su zubar da girmanka, ko su bayyana aibinka, ko su tozarta dukiyarka. Ga shi kuma suna ja maka fushin Allah da tozarta a cikin jama'a. Nisanci zunubi don ka zauna lafiya.

79. Matsalolinmu a yau da guda biyu ne: Mu yi aiki kafin mu yi nazari, ko mu yi ta nazari ba aiki.

80. Idan ka taimaki wani saboda Allah kada ka jira ya yi maka godiya. Yardar Allah ta fi yardar mutane.

Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

21/10/1438
15/7/2017

» Gabatarwa Zauren Minbarin Malamai +2347037477743
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support